Lost But Found

8.8K 668 2
                                    

Ibrahim's POV

Last thing da ya gani kafin motar sa ta fadi shine fuskar Moon, and she looked so scared. Sanda motar sa ta fadi babban tsoron sa na shine mutuwa ba, tsoronsa shine kar wani abu ya samu Moon because of him. A lokacin daya dawo hankalinsa abinda ya fara tunawa shine Moon, fatan sa Allah dai yasa babu abinda ya same ta, dan haka kalmar daya fara furtawa itace "Maimunatu" muryar mamansa yaji a kusa dashi tana yi masa magana, sannan kuma yaji shigowar wani namiji yana tattaba shi, mutumin ya bude idonsa ya haska masa wata karamar fitila, daga nan kuma ya koma bacci.

Sai daya farka for the second time sannan ya fahimci kwanansa uku a asibiti unconscious, ga maman sa da little Moon sun zo daga Ibadan, amma ita maman sa abinda aka gaya mata shine accident yayi, ba ta san dalilin accident din ba, dan haka ya san bata da labarin ko Moon taji ciwo ko bata ji ba.

Doctor ya saka ya kira Amina, wacce tun da ta kai shi asibiti kullum sai ta je ta duba shi, haka ma Daddy, Doctor ya gaya wa Amina cewa ya farfado kuma yana nemanta, ba'afi awa daya da wayar ba sai gata tazo. Sosai ta nuna murnar ta daganin ya dawo hayyacinsa, ta ringa yiwa doctor din tambayoyi akan lafiyar Ibrahim din har sai da ta fahimci babu wani muhimmin concern dangane da lafiyar tasa, shi kam Ibrahim kallonta kawai yake yi yana murmushi, sai da doctor ya fita sannan yace "har haka aka damu dani dama ni ban sani ba?"

Tace "no, ba damuwa nayi da kai ba. Naso ace ka balla spinal cord yadda ba zaka sake bin mata da miji ba" yace "yes you are right. Nasan banyi dai dai ba, komai yayi min ni na jawo wa kaina, I was just scared he would hurt Moon"

Tace "matarsa ce fa? In ma menene zaiyi mata ina ruwanka? Kuma ma Sultan will never hurt Moon. Yanzu gashi sanadiyyar abinda ya faru sunyi rigima, har ya kwanta a asibiti ma. She is pregnant fa. You ought to get over her by now"

Yace "I am over her. Abinda ya faru nima ban san ya akayi ya faru ba and I feel sorry na jawo problem a tsakanin su. Is she OK?" Tayi ajjiyar zuciya ta zauna a kujera tace "yes she is fine" yace "please can you go to her ki bata hakuri on my behalf? Ki basu hakuri ita da mijinta" ta bata fuska alamar bata son zuwa, ya marairaice murya, "please kinga bani da lafiya fa. Take little Moom with you in suka ganta sai sufi hakura".

Har ran Amina bata so zuwa ba, ita a ganinta menene kuma na zuwa wani bada hakuri? Ai kamar kokarin tayar da magana ne kuma, aikin gama ya riga ya gama, daga Ibrahim har Sultan kowa jikinsa ya gaya masa shikenan magana ta wuce sai dai fatan a kiyayi gaba kuma. Amma sai ta yarda zata je din to put his mind at ease. Ta dauki little Moon suka tafi tare.

Moon ta tare su sosai kuma taji dadin ganin takwararta amma kamar yadda Amina tayi tsammani sam ba ta ga alamar soyayyar Ibrahim a tare da Moon ba, sai care da mutunta juna, tace mata zata zo ta duba Ibrahim amma ita kan ta Aminan ta san fada kawai Moon tayi ba zuwan za tayi ba. Da zasu taho Moon ta hada kaya da yawa ta bawa takwararta suka dawo asibiti gurin Ibrahim.

Suna shiga dakin suka tarar Ibrahim ya tashi zaune suna magana da Mama, Amina ta durkusa ta gaishe da Mama wacce ta amsa mata da fara'arta, daga nan Mama ta fita ta basu guri suyi magana. Ba tare daya kalli Amina ba yace da little Moon "sweetheart menene wannan a leda kika samo haka?" Ta karaso gurinsa tana washe baki tace "namesake dina ce ta bani" ya karba yana dubawa "wow duk wannan naki ne ke kadai, bata baki komai ki kawo min ba?" Tace "ba abinda ta bani in kawo maka" yace "kuma bata ce tana gaishe ni ba?" Tace "eh bata fada ba" ya dauki yarinyar ya dora a cinyarsa, yana shafa kanta "sweetheart yau kinga namesake dinki ko? How do you find her?" Tace "she is beautiful and nice" yace "yes sweetheart she is the nicest person I have ever known".

Amina ta ajiye ledar hannunta ta juya zata fita, sai a lokacin ya tuna tana gurin, yace "wait" bata juyo ba yace "Maimunatu Please wait"

Chak ta tsaya kafin ta karasa kofar, ta juyo a hankali tana kallonsa, a nutse ta fara magana "I am not Maimunatu, I am Amina" ya tsaya kawai yana kallonta dan shi bai ma san ya kirata da Maimunatu ba sai data fada. Ta kalli little moon akan cinyarsa tace "Moon je ki nuna wa Mama kayan da kika samo"

MaimoonTahanan ng mga kuwento. Tumuklas ngayon