Drunk

7.8K 622 4
                                    

Nabi motar da kallo har ta fice, jin kaina nake a cushe cos babu wani tunanin da yake tafiyar min dai dai. Kamar daga sama naji kara mai kama da accident din mota a waje, ko ba'a gaya min ba na san Sultan ne, bansan lokacin da naje bakin gate ba kawai nima gani na nayi a gurin, motar Sultan na gani ta daki bishiyar da take opposite din gidan mu, ji nayi tamkar zuciya ta ta fado kasa, ina ganin masu gadi suna tafiya gurin amma ni kamar an daskarar dani, ga mamaki na sai naji ya yi wa motar key yayi reverse da ita tare da tarwatsa mutanen da suka tafi kayo masa dauki, gaba daya gaban motar yayi damage amma a haka ya sake fisgarta ya yau titi.

Yana tafiya masu gadi suka fara surutu:

"wai yaron nan me yake kawoshi unguwar nan ne kwanannan? Kar fa yazo ya tattaka mana yara a banza kuma babu mai daukan mataki a kansa"

Ni dai jiki a sanyaye na koma gida. Sai da na kama hannun kofar shiga palour sannan na tuno da ya Habeeb da kuma alkawarinsa na gaya wa Mommy. Ga mamaki na sai naji babu wani tsoro a zuciya ta, gwara a yi ta ta kare kowa ma ya huta, dan ni yanzu ban damu da kome za'ayi min ba, nafi damuwa da halin da Sultan yake ciki, I feared he might hurt himself, ni kuwa nasan ba za'a taba yimin wani physical damage ba. Na murda kofar na shiga da sallama, babu kowa a palourn sai ya Habeeb, fuskarsa sam babu rahama a cikin ta, kallo daya nayi masa nayi hanyar kitchen, haushinsa nake ji sosai duk da cewa deep down nasan ba laifin sa bane ba laifi na ne, he was only trying to protect me.

A kitchen na samu Asma'u, cook din gidan nace "Ma'u ina Mommy?" Tace "Mommy taje unguwa, lokacin kina gurin baƙon ki, tace in gaya miki sai dare zata dawo" banji dadi ba cos I didn't want to delay this any longer. Na sake fito wa na wuce ta gaban yaya Habeeb na hau stairs din part dina. Direct balcony na wuce na saka kujera na zauna ina kallon bishiyar da motar Sultan ta daka.

Kamar ranar ne na tsaya a gurin nan ina kallon Ibrahim ya fita daga gidan nan ruwan sama yana dukansa. Can't believe it has already been six years and history is repeating it self. Amma yanzu a shirye nake, I am no longer sixteen years old, I am twenty two. Yanzu ba yarinyar nan bace da ta gama secondary school, wannan double degree ne da ita a second best university in the world. Ba wai zama zan yi in jira abubuwa suke faruwa ba kamar yadda na zauna nayi ta jiran Ibrahim, this time I am going to make things happen. Tashi nayi na koma daki na dauko laptop dina na kunna, email na shiga na rubuta wa Daddy saƙo kamar haka "please Daddy check this out" sai nayi masa attaching da duk rubuce2n da nayi akan sultan, na tura masa.

Nayi missing Hafsat, da at least in na gaya mata zan dan samu sassaucin radadin da zuciya ta take yi. Na dauko wayata nayi dialing number din Sultan, matar mtn ce ta yi min bayanin the number was switched off. Wani murmushin takaici nayi, exactly haka nayi ta kiran Ibrahim switched off, it is funny sometimes yadda rayuwa take zuwa wa mutum. Wani tunani ne ya fado min, this is my chance na ganin Sultan in tabbatar masa da cewa abinda ya dauka ba haka bane, and most importantly to find out if he is Ok. Dan nasan Mommy tana shigowa gidan nan suka hadu da yaya Habeeb to ni da in kara fita sai wani ikon Allahn kuma. Kuma nasan duk bayanin da zan mata ba zata fahimta ba da taji cewa Abbakar din da nake gaya mata Sultan ne shikenan zata toshe kunnuwanta daga dukkan bayani na.

Amma still it will be better in ni na fara gaya mata. Na dauko waya ta nayi dialing number ta, ta dauka suna ta hayaniya a gurin tace "Moon ya akayi ina gurin taro ne, akwai wani abu ne?" Nace "Mommy akwai maganar da nake so muyi ne" tace "am very busy yanzu, can't it wait sai na dawo?" Nace "Ok Mommy, sai kin dawo din" na ajiye wayar a raina nace "why is everyone not available when I needed them the most?"

Ina daki har aka kira magrib ina ta kiran Sultan har yanzu switched off, in ma nace zan fita neman sa bansan inda zan same shi ba, to ko gidan su zanje? Tunda gidan babba ne maybe har in fito babu wanda zai san na shiga? Amma fa ni ban taba shiga palace ba, in naje ma bansan inda zan dosa ba. Na tashi nayi alwala nayi sallah na zauna ina adduoi na naji karar wayata, ban dauka ba sai da na kammala, na dauka naga bakuwar number, ina kokarin dialing wani kiran ya sake shigowa, na daga da sallama. "Maimoon Amir ne, kina ina?' Ji nayi gaba daya yawun bakina ya kafe nace "Amir ina Sultan?" Ya sake cewa "kina ina?" Nace "ina gida, me yake faruwa?" Ya danyi shiru sannan yace "ina gida dazu wani friend din mu ya kirani yake gayamin yaga Sultan a bar and he seems to be injured, to shine naje gurin na same shi, he is injured kuma yaki tashi in kaishi asibiti" da sauri nace "how bad is it?" Yace "not that bad, kawai dai kafarsa ce, kuma tana bleeding har yanzu. Sultan taurin kai ne dashi, ban sani ba ko ke in kika yi mishi magana zai tashi, he has been drinking also" na runtse ido na na bude, a raina nace "nasan za'a rina, an saci zanin mahaukaciya" ya katse min tunani na da cewa "can you come, please?" Na ce "of cause I will come. Kuna ina?" Yayi min kwatance, nace "amma kuma fa ban iya driving ba, bana so kuma in dau driver, ko kuma zuwa zakayi ka dauke ni?" Yace "alright gani nan zuwa" tashi nayi da sauri na chanja kaya zuwa wani material simple doguwar riga, nayi rolling veil sai kuma na saka dogon jihab, na sauka kasa, yaya Habeeb ya tashi daga inda yake dazu ina jin masallaci ya tafi, na samu Asma'u tana shirya dining nace mata "Ma'u kinga kaina ne yake ciwo, na sha magani yanzu zan kwanta, please in Mommy ta dawo ki gaya mata ina kwance banjin dadi" da sauri tazo ta dafa goshina, "oh oh, sannu mai sunan Daada, gashi nan kuwa jikin ki ya fara zafi, Allah ya sawake" nace "Ameen" na koma kamar na hau sama sai nabi ta kofar baya na fita, ina fita Amir ya kirawo ni yace gashi ya zo, na zagaya ina duba securities, dama in Daddy baya nan basu da yawa, guda biyu kawai na hango tare da baba Habu a can gefe a zaune, sai da na zagaya ta side din da ba zasu ganni ba sannan na shige seat din baya na durkusa a kasa yadda wanda yake waje in dai ba lekowa yayi ba ba zai ganni ba. Ina jin baba Habu yana tambayar Amir "har ka karbi sakon?" Shi kuma yace masa eh sannan muka fita.

MaimoonWhere stories live. Discover now