The Blood Donor

9.7K 721 7
                                    

Pre-eclampsia ciwo ne na masu tsohon ciki. Shine ciwon da yake saka mata convulsions (jijjiga) during labor. Alamominsa sune matsanancin hawan jini, kumburi, jiri, matsanancin ciwon kai, sensitivity to light, blurred visions etc. Matan da suke at risk of samun ciwon sune wadanda already suke da hawan jini kafin su samu ciki, wadanda mahaifiyar su ko sister din su ta taba yi, yara kanana da suka samu ciki da wuri ko kuma manya wadanda shekarun su suka ja sosai. In kina da ciki kuma kika ga kina da wadan nan alamomin dana lissafa a sama to kada ki yarda ki fara labor, it is very deadly, za'a iya rasaki ko babyn ko duk ku biyun, ko kuma ki samu wani mugun ciwon, wani lokacin har hauka ake haduwa dashi. In baiyi tsanani ba kuma cikin ki bai tsufa sosai ba, ana iya control dinsa, in yayi tsanani best solution shine ki tafi asibiti ayi miki aiki a cire babyn. Shikenan.

Na rintse idona ina lissafa condition dina, a take na yanke shawara. Na bude idon na sauke su akan Sultan, a hankali nayi magana "Sultan stop the car" ya dan kalle ni yaga am serious sai yasa signal yayi packing a gefen titi. Ya juyo gaba daya yana kallona "Moon menene? What do you need? Jikin ne?" Na danyi masa murmushi kadan nace "asibiti zaka kaini ba gida ba" ya dan tsorata kadan "is the baby coming?" Na girgiza masa kai, "asibiti zamuje, za suyi min aiki su fitar da babyn" a take naga tashin hankali a rubuce a fuskarsa, na rike hannunsa sosai nace "don't do this Sultan please, I need your support and strength. Please don't freak out" ya dan nutsu kadan yace "me yasa kika ce zasu yi miki aiki? Kince kuma ba labor kike ba" nan nayi masa bayanin duk situation dina da risks din da nake facing.

Sosai naga hankalinsa ya tashi, ya daki stirring wheel da hannunsa yace "damn it, I hate that Ibrahim" na bata rai nace "Ibrahim bai dora min ciwo ba Allah ne ya dora min. Ba akaina aka fara ba ba kuma akaina za'a gama ba. Tunda na samu ciki lafiya lau nake, ko mugun laulayi banyi ba, wadansu matan daga ranar da suka samu ciki ba zasu samu lafiya ba har sai sun haihu. Wadansu matan talauci ya saka ko abinci mai kyau basa samu a lokacin da suke da ciki, wadansu matan basa samun medical care, wadansu matan zasu hadu da ciwo irin nawa amma basu san menene ba kuma su zo su fara labor a haka, a karshe su samu matsala koma su mutu gaba daya. Amma ni na samu komai, komai da nake bukata na samu, abinda nake bukata a yanzu shine support dinka, together we will get through this" ya dan nutsu ya dakata yana kallona, na mayar da idona na rufe inajin kaina tamkar zai rabe gida biyu, ga wani jiri da nake ji duk da cewa a zaune nake. Naji hannun Sultan yana shafa fuskata, na dan bude idona ina kallonsa, na rike hannunsa da yake kan fuskata nace cikin sanyin murya "I need you to be strong" ya hadiye wani abu a makogwaronsa yace "yanzu me zamuyi" nace "asibiti za muje. Amma please bana son ka kira kowa, Mommy da Ummee in suka zo zasu kara min pressure ne. We can do this alone. Everything is going to be alright" da hannu daya ya dauko wayarsa yayi dialing, na fahimci Doctor na yake kira, yana dauka ya fara masa bayanin abinda nace masa da kuma symptoms dina, banji mai Doctor din yace masa ba yace "alright, we are on our way" ya kashe, hannun na yana cikin nasa ya kunna motar yayi reverse muka dau hanyar hospital, na koma na kwanta na rufe idona.

Sama sama naji shigowar mu asibitin, naji Sultan yana gayawa doctor a waya cewa gamu mun iso, hannunsa daya a rike da nawa dayan kuma ya saka yana shafa fuskata, na dan bude ido da niyyar in kalleshi amma hasken fitulun cikin asibitin ya saka na mayar da idona na rufe ba tare dana kalle shi din ba, naji zuwan doctor gurin mu, ya kunna fitilar wayarsa ya haska ni, na kara runtse idona saboda bana son hasken, yace da Sultan "gwara da Allah yasa kuka taho yanzu baku zauna kunce sai safe ba, she is in critical condition and we have to take the baby out now" Sultan yace "yes, haka tace".

Doctor din ya tafi sai ga wasu nurses sun kawo gadon daukan marasa lafiya, Sultan ya chika hannuna ya zagayo ya dora ni akan gadon sannan ya kuma mayar da hannun sa cikin nawa aka tura ni zuwa cikin asibitin. Ko sau daya sultan bai cika hannuna ba har aka kaini dakin da za'a shiryani.

Doctor ya kawo wa Sultan takardu yayi signing, har zai fita Sultan ya tsayar dashi ya fara magana muryarsa kamar wanda zaiyi kuka yace "doctor please, nasan kasan aikin ka ba wai koya maka zanyi ba, but please if anything should arise, in kana ganin Moon zata iya samun wata matsala, please doctor just forget about the baby and save my wife. Gwara in rasa shi akan ace wani abu ya same ta" doctor ya dawo ya tsaya a gaban Sultan ya dora hannunsa akan kafadar sa, fuskarsa da murmushi yace "Our Prince, insha Allah nayi maka alkawarin zan kawo maka matarka da ɗan ka lafiya lau, babu abinda zai same su duk su biyun" Sultan ya ɗanyi murmushin yaƙe yace "thank you doctor" Doctor yace "amma nima ina bukatar wani taimako daga gareka, akwai maganar da zamuyi ka biyo ni office yanzu" Sultan ya ɗan juyo ya kalleni yace da doctor din "bazamu iya maganar anan ba? Cos I don't want to leave her alone" doctor yace "OK, sai muyi anan din" suka zauna akan kujera doctor ya fara magana yace "kaga dai halin da take ciki yanzu, dan haka dole ba zamuyi mata anaesthesia ba, muna bukatar control over her bp, in muka yi mata allurar bacci ba zamu samu wannan control din ba, we need to keep her awake through the entire operation. Da akwai aikin da ake yi na ido biyu, zamu kashe lower part of her body yadda ba zata ji zafin komai ba har mu gama. Taimakon da nake nema a gurinka shine ina so ka shiga operation room din a tare damu ka zauna a kusa da ita kana yi mata magana mai dadi wacce zata kwantar mata da hankali".

MaimoonWhere stories live. Discover now