page 2

703 63 3
                                    

👣SARTSE👣

©by $ophieG❤&😘Um Nass

Page 2⃣

"Ya shafe fiye da mintuna goma awajan amma bai iya tantance yanayin da yakeba.
Addu'a yake ya farka daga wanan mummunan mafarkin da yakeyi, amma ko kadan bai hango hakanba.

Fizgoshi yaji anyi da ƙarfi Wanda hakan ya tabbatar masa gaskiyar al'amarin dake faruwa.
Idanuwan sa ya dago Wanda tuni sun sauya kala daga farare zuuwa jajaye kamar garwashin wuta.

Mahaifin sa ne ke jansa da ƙarfin sa wanda azuwa yanzu komi na kan Ma'aruf ya tsaya cak, sai binsa kawai yakeyi kamar rak'umi da akala.

Sosai ya bama mutanen wajan tausayi kowa fiskar sa ɗauke da alhini, saɓanin dazu da suke cike da farin ciki.
Liman ne ya kalli inna kulu cikin takaici da wulak'ancin da ta musu "kinji haushin kanki kulu, akwai lokacin d zaizo kiyi kaico da abin da kika aikata. Wallahi Kinyi asara bata raiba kin kuma wulak'anta kanki mafi k'ask'anci arayuwa, kin wargaza auran ɗiyarki ke da kanki kika Burma ma cikin ki wuk'a."
Maganar sa na fita da k'unan rai ga kuma sanyi na busashi dai-dai yanda ruwan da ta zuba musu ya jiƙashi.

"Allah ya kiyaye nayi dana sani akan wannan soloɓiyon yaron. Mungun bakinka kuma ya fada kanka, na daɗe da sanin cewar kai dan baƙin ciki ne burin ka kaga kowa cikin tozarci, to na Rigaka cewa Allah, duk da rawani da carbin da kake fama dashi kamar zakiru, nan kuwa k'arshen tsiya Na tare da kai, ai mun san komi balle a yaudare mu ade yima wasu."

Kamar dolo haka liman yake kallon ta shida jama'arsa takaici da bak'in cikin abin da kulu ta masa Na k'age ya hanashi magana. Kai ya jijjiga ya wuce idanuwansa cike da k'walla.
Yana kuma kaicon karambanin da yasa shi mata magana duk da sanin wacece Itan da yayi.

Ahankali kowa ya tafi ya barta da yawa suna kaico da halayya irin tata.
Idan aka dauke malam yakubu wanda yake tsugune kamar gunkin da aka sassak'a, tun lokacin da malam lawan yayi rantsuwa akan haramtama ma'aruf auren khairat.
Bai k'ara sanin abin da yake faruwa awajan ba.
Sai dai yaji wajan shuru kamar guguwar data taso ta lafa.

*****

A can gidan su ma'aruf komi ya ƙara dagulewa Wanda mahaifiyar sa najin labari ta yanke jiki ta fadi.
Da ƙyar aka yayyafa mata ruwa ta tashi, hawaye ne yake zarya a idanuwanta.
Anya akwai tozarcin daya wuce wannan? "BABU SHI" ta fada afili Wanda hakan ya janyo hankulan mutane suna ƙara bata haƙuri ahankali kowa ya fara kama gabansa, kafin wani lokaci gidan ya zama tayau babu kowa, sai yayar ta data rage.
Dafa kafadarta tayi kana taja numfashi "kiyi haƙuri Abu ko wani mutum da irin jarrabawar sa dama can Allah bai k'addarama ma'aruf khairat amatsayin matarsa ba."
Murmushin takaici Abu tayi kana ta fara magan "ko kaɗan banji haushi ba Yaya Indo sai dai lamarin ne yazo min Abazata, tabbas ban taɓaga wulak'anci irin wanan ba. Amma ba komi nagode Allah da lamarin y tsaya haka. Sai dai zamusha habaici awajan mutanen garin nan, kin dai san komi ba sai n faɗa miki ba."

Jijjina kai Indo tayi tabbas wannan zai zama k'unci agare su, bama iya su Abu da suke Iyayen ma'aruf ba harda su da suke dangin su sai ya zama abin gori agaresu.
To amma ya suka iya da abin da yafi k'arfinsu? Ajiyar zuciya ta sauk'e sannan ta fara magana "ba komi Abu mutane ai sun saba da magana, namu da sauk'i ma idan kikaga na wasu, ni dama nasan rashin sana'ar Ma'aruf zai kawo masa damuwa wata rana.
Amma ina fatan hakan ya zama izina gareshi da sauran masu hali irin NASA."

"AMEEN yaya Indo"abin data Iya fada kenan tayi shuru tana tuno rayuwar baya irin famar data sha da ma'aruf akan Neman Na Kansa.

"To nikam zan tafi Abu sai wani lakacin, Allah ya jisshemu alkhairi."

Tashi tayi ta rakata har ƙofar Gida tana mata godiya, ita kuma na ƙara jaddada mata akan tayi haƙuri ta maida komi ba komiba.

*****

A ɓangaran khairat Amarya cike suke da k'awayanta suna ta shagali, ana yima khairat kitso saboda aranar da aka ɗaura aure ake kai amarya da daddare.

Kulu ta kalli yakubu dake tsugunne da kara ahannun sa yana zane a kasa kamar ma besan abinda yake yiba tace.

"Sai ka tashi ka koma cikin gida, banga abin bata rai da tunani anan ba, kaida aka taimaka Ai abin kayi murna ne, yaushe zaka yadda ka siyar da akuya tadawo ta naci maka danga?"

Cigaba yayi da zanensa dan bai san abin daze CE mataba, idan yace zai biye ta zuciyar sa dukanta zai yi, irin dukan da baya tunanin koda tayi jinya zata tashi dadukkan jikin ta lafiya lau.

"Sai kayi ta yi, kayi ta tsuguno har sarkin tsuguno ya iske ka nidai bazan yadda ajefamin ya hannun me matacciyar zuciya ba."
Gidan tashiga tasamu su Khairat sai raha suke an kammala mata kitso yazubo gefen kunnenta tayi kyau sosai.

Kallon su tayi tsaff sanan ta fara musu magana cikin hargowa da faɗa "To gayyar tsiya wato Ku murna kuke za'a aurawa ƴata ragon maza ko? To ku tashi ku fi cemin na watse taron ba naku kadai ba harna mazan waje, mugaye masu shirin ɗaurawa ƴata aure da wanda ya rako maza."

Wa ƴanda zasu shigo gidan suka ganta awaje tana tafka tsiyar ta su suka soma tashi suna ficewa, ahankali dukkan su suka watse.

Cike da rashin fahimta Khairat take kallon ta cikin mamaki.
"Kalleni da kyau, ki kuma buɗe faka-fakan kunnuwan ki kiji ni da kyau. Ni nan Hauwa kulu na haramta miki auren ma'aruf wallahi ko bayan raina."

"Inna lillahi wa inna ilaihirraji'un" abin da Khairat take nanatawa kenan abakin ta.
Bayan ta rasa duniya take ko kuwa dai mafarki take?
Me take shirin ji? Mi kuma kunnuwan ta suke jiyar da ita?
Ma'aruf din ta
za'a hana ta auren sa.
Yanzu ashe inna rashin mutunci taje tayi awaje?
Tarin tambayoyin da takema kanta kenan, kafin kuma hawaye ya fara tsere akan fuskarta.

🥀🥀🥀🥀🥀

#Sartse
#NWA
#CMNTS, VOTE SHARE
#GIRMAMAWA

SARTSEМесто, где живут истории. Откройте их для себя