page 4

452 52 3
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG❤ &😘Um Nass🏇

®NWA

Page 4⃣

"Binta da kallo M'aruf yayi  amma bazai iya tantance mi yake jiba, shi kansa yasan ya zama saƙaƙon da cagi nasa ya ƙare masa.
Tabbas rayuwa ta sauya masa alokacin da ya sakankance da zata bashi farin ciki na har abada.
Ido ya lumshe ya buɗe wanda ya sauƙo da zazzafan hawaye, musamman tuna furucin mahaifinsa akan maganar Khairat.
"Ya Allah ka bani ikon jure wanan kaddarar."
Da ƙyar ya faɗi hakan a ƙasan maƙoshinsa.

Ji yayi an dafashi afirgece ya jiyo domin wani sanyi da yaji ajikinsa.
  Mahaifiyar sa ce ta fara goge masa hawayen da yake zuba tsakanin kwarmin idanuwansa.
Wata karaya da rauni ne suka ƙara dirarma zuciyar sa, wani sabon kukan ya kufce masa yana mai rungumarta.
Kansa ta fara shafa ahankali ba tare data ce masa komi ba. Har yayi kukansa mai isarsa Wanda hakan yake ƙwarzabar zuciyar ta, ji take da tana da iko da tabbas zata cire masa ciwon da yakeji aransa.
Haka kuma tana jin tsanar kulu data zama silar wargazama autan ɗan nata farin cikin sa.
"Innah fada min ya zanyi?  Ina jin zuciyata Na zafi kamar zata fashe? Ko wani bugawarta da ƙunci sosai take bugawa? Innah dama rashin sana'a yana zama matsala ga rayuwar mutum har ya shafi farin cikinsa.?Innah kingafa su Audi ba'a haramta musu auran mata ba duk da tare muke da su? Mi yasa ? Mi yasa saini hakan ta faru akaina?"
Wani kukan ne ya ƙara kufce masa Wanda a ɓangaran Innah Abu ya zama rauni da tausayama yaron nata.
Numfashi taja ta furzar da iska mai zafi cikin sanyin murya ta fara mgn "Saboda ka ban-banta dasu ma'@ruf, haka kuma ƙddararka da tasu akwai ban-banci mai yawa. Ko wani mutum aduniya an ƙaddara masa rayuwar sa, sai dai wata tana zuwa da sauƙi idan mutum ya yawaita Addu'a da aiyukan alkhairi. Ka ƙaddara aran ka babu alkhairi ne a auran ku da khairat shi yasa auran ku ya wargaje adai-dai lokacin da babu Wanda zai tsammaci faruwar hakan."
Numfashi taja tana kallon ma'aruf yanda yake sauraronta da alama yana amsa duk wani saqon da take Isar masa. "Ina son ka zama namiji ma'aruf. Lokaci yayi da zaka nunama mutanen ƙauyan nan harda kulu kai ba lusari bane kamar yanda suke fada, ayanzu kake da ikon tsayuwa da ƙafafuwan ka, kana ka dogara da kanka, ka kuma miƙa lammuran ka ga Allah zai Isar maka akan ko wani al'amari. Ka rufe babin Khairat arayuwar ka zaka samu fiye da ita anan gaba. Ka ƙwarara zuciyarka Ma'aruf kada ka taɓa yarda ka fadi, tabbas kulu tayi gaskiya ta wani ɓangaran, akwai rai da rayuwa ga mutuwa mai bibiya babu tabbacin zamu ci gaba da kula da kai, ya zakayi abayan babu mu? Tun yanzu ya kamata ka fara sabawa da riƙe kanka harda wanima tun muna Raye."

Numfashi yaja mai ƙarfi yana ƙara ƙan-ƙame Innah Abu ji yake kamar tana masa wasiyyar ban kwana ne.

"Na miki alƙawali Inna zan zama namijin duniya, zan dogara da kaina. Zan kuma rufe shafin Khairat arayuwata. Innah zan zama namiji guda awanan ƙauyen saina kafa tarihi mai yawa da yardar Allah."

Murmushi itama tayi tana rungumeshi "Allah ya yarde mana, Allah ya albarkaci rayuwar ka ya dafa maka adukkanin lammuranka."

"Ameeen innahta"

Murmushi mahaifin ma'aruf yayi Wanda yana ganin abin daya faru, aransa yana ƙara jinjina ƙarfin soyayyar dake tsakanin ɗa da uwa, yana kuma fatan ci gaban ɗan NASA."

***********
Azuwa yanzu khairat ta karaya, ta kuma sawa zuciyarta haƙuri saboda babu mai lallashin ta sai babanta, wanda tun faruwar lamarin ya kasa koda shiga gidan.

Akwai ƙuna da nauyi azuciyar sa sosai, ga tarin kunyar mutanen ƙauyen daya gama ji musamman malam Auwalu mahaifin ma'aruf.
Ya yankema Kansa shawarar daina fita saboda bazai juri ganinsu ba.

Amma mi gobe zata haifar??

🥀🥀🥀🥀🥀

#SARTSE
#NWA
#CMNT, VOTE SHARE
#GIRMAMAWA

SARTSETempat cerita menjadi hidup. Temukan sekarang