👣SARTSE👣
SophieG❤&😘Um Nass
NWA
Page 8⃣
Soron gidan ya shiga ya tsaya daga gefe yayin da zuciyar sa ke bugawa da sauri.
'Anya kuwa banyi wautar kiranta ba? To ni mema zance mata?' taron tambayar da yake acikin zuciyar sa kenan, ya kasa lalibo amsar su, yana tsaye idon sa na kallon ƙasa har yaji shigowar ta soron.
A ɗan diririce ya ɗago sai dai ga mamakin sa tabi ta gefen sa taleqa wajen bataga kowaba
"Mtsww" ta juyo tanajan tsaki "wallahi wannan imranan sai naci gidan su, dan naga take-taken fitsarar sa ya soma zuwa kaina."
Da gan-gan tayi haka saboda ta fahimci ma'aruf ne ya tura kiran ta, wanda ya gagara mata magana, so take taga ƙarshen gudun ruwan sa, shi yasa tayi kamar bata san shi ya kirata ba.
Shi kuma anasa gefen mamaki ya gama cika ma'aruf, ko dai bata ganshi ba ne? Amma ai ta gabansa ta wuce. Zuciyar sa ke bashi amsar kokonton da yake.
Mamakin sa ƙaruwa ya sake yi ganin tan shirin komawa ciki, ganin tabbas bata lura da shiba yasa yayi saurin kiran sunanta cikin sarƙewar muryarsa ahankali, sosai zuciyar sa ke bugawa kamar zata faso ƙirjin sa dan tsoro.
Tsayawa khairt tayi cikin rashin nuna muhimmancin sa awajan ta amsa a daqile bayan ta juyo.Daburcewa yayi ya fara kame-kamen abin faɗa ga kuma tarin tsoron da ya fito afuskarsa.
"Baka da Abin fada ne malam? Ka kirani kuma kayi shuru." Sautin muryarta ya sake amsa kuwa akunnen sa.
Ƙarfin hali yayi ya fara ƙoƙarin magana sai kuma yasoma in-ina alamar ruɗewa da rashin sanin takamai-man abin cewa, da ƙyar yace:
"Dan Allah ruwa zaki bani nasha ƙishi na keji."Kallon sa tayi taga yanda ya gama ruɗewa gashi ko ina ajikinsa rawa yake. Dariya ce taso kufce mata tayi saurin kawar da kanta "Saboda shan ruwan kayi tattaki tun daga gidan ku har nan?" tambayar data masa tana ƙara ganin yanda ya sake diriricewa, dariya take sonyi amma sam bata son ya gane.
Kallon ta yayi kana ya sunkuyar da kansa.
"Um eh! Dama hanya ce ta kawo ni, kuma nasN kafin naje gida zanji qishi sosai. Shinefa na tsaya anan."Murmushi tayi mai sauti maganar sa tana mata daɗin ji, harda yanayin sa, amma bata gaskata iya gaskiyarsa ya faɗa mata ba.
"Oh to zan bawa Rumasa'u takawo ma, danni aiki ma nake aka samu dan rainin hankalin daya taso ni."
Tana maganar ne tareda shigewa gidan, shi kuma sokon ya bita da kallon kauna irin na dolaye.
Bai tsaya jiran akawo masa ruwan ba ya kaɗa kansa ya tafi, dama ita yake son gani tunda ya ganta magana ta ƙare.
**
Tun daga wannan lokacin yake ta kai kawon binta duk inda zataje yana bayan ta, sai dai baya barin ta ganshi.
Duk hanyar da take wucewa ya santa, yana zaman jiran wucewar ta da kuma dawowar ta, sai dai bai san ta ina zai fara faɗa mata abin da ke damun zuciyar sa ba? Sau da yawa yake zuwa gidan su sai dai yagaji da tsayiwa ya juya, hakan na hanashi sukunin bacci bayayi ba tare da mafarkan ta ba. wata rana sai dai ya tsaya a ƙofar gidan idan yaji motsin wani sai ya gudu. Ya shafe sati biyu yana wannan dabi'ar.Innah Abu tasha tambayar sa ganin yanda shurunsa ya ƙara ninka na da, haka kuma yawan fitarsa tayi yawa saɓanin abaya da baya wuce awa guda awaje ya dawo gida.
Amma ce mata yake babu komi. Ƙyaleshi tayi taci gaba da sabgoginta.
Duk abin da yake Khairat tana lura dashi harta fahimci lokutan zuwansa, dan haka take ɓoyewa abayan ƙyauren gidan tana kallonsa, bakuma karamar soyayyar sa ya haifar mata ba, wata rana tausayinsa ma takeji, akwai wata rana data fito ta riskeshi sai ya juya cikin sauri ya dake sai da yayi Nisa ya waiwayota tana nan tsaye tana kallon sa, batasan lokacin da hawaye yazuba mata ba, tana sonsa tana kuma jin zata iya sauya shi ya koma namiji wanda bashi da tsoro a zuciyar sa, murmushi tayi ganin yanda yake ta waiwayen ta harda tuntu6ensa. Sai da ya ɓacema ganinta sanan ta koma gida.
****
Kamar ko wani lokaci Yauma hakance ta faru, bayan sallar isha'i shine lokacin da yake zuwa daga masallaci sanin mahaifin ta baya dawowa sai ya tsaya karatu da dalibansaa acan tareda liman kana ya dawo.
Fitowa tayi ta tsaya daga gefe tana kallon sa yana jingine da bishiyar dake gefen gidan ya lumshe idon sa yana tunanin khairat, ganinta kawai yayi a gaban sa da azama ya ɗaga ƙafa zai gudu ta riko rigar sa tace."Minene matsalarka ne ma'aruf?" tambayar da take masa tana ƙara kafeshi da manyan idanuwan ta.
Kallonta yake cikin rashin fahimtar abin da take faɗa "Ni! Ni ƙalau nake"ya faɗa yana kallon jikin sa.
Dafe kanta tayi cike da takaicin sa "Ma'aruf mana! kayi kokarin zama namiji, ka furta abin da ke ranka, wannan lunge-lunge ba zai samar da mafita a garemu ba, kullum kana ƙofar gidan nan amma daga kaji motsi kake guduwa, sannan ko ina naje kana biye dani, mine ne damuwar ka akaina? Shin wai baka gaji bane?"
Tun da ta fara magana yake kallon ta, yana kuma cike da mamakin sanin da tayi yana bibbiyar ta, ɗa ƙyar ya buɗe baki cikin sanyin nan nasa yace "ina sone dama in faɗa miki...." Sai ya kauda fuskar sa gefe daga kallon da take masa, kafin da ya ɗora da "Zan faɗa miki ne wallahi, um um kawai dai ina jin zuciya taa nata bugawa ne da Sauri da sauri, idan ban gankiba ina jin tana zafi, shinefa su Audi sukace wai Ina sonki ne."fuska ya sauya kamar zaiyi kuka.
Dariya ce taso kufce mata ganin ya da yake magana kamar mai koyon ta, da ƙyar ta iya riƙe ta tace "Tun yaushe ka fara jin hakan a zuciyar ka?"
Kansa ya ɗaga sama alamar tunani "Yauwa tunfa ranar dana fara ganin ki agidan Audi, kuma ni bansan ta Ina zanfara ba Ina tsoron ki ƙi kulani irin wanda kika min ranar nan." ya ƙarasa maganar yana langaɓe kansa ƙasa.
Komi nasa burgeta yake sosai, haka duk maganar da yake tana kara rura mata wutar ƙaunar sa "Ma'aruf na maka kama da wacce batasan darajar ƴan Adam bane? Ka daina tunanin zan maka wulaƙanci, kuma dan Allah ka daina shakkar yimin magana, kar ƙawaye na suce min matar matsoraci"
Murmushi Shima yayi duk da maganarta ta ƙarshe tabashi mamaki amma haka ya daure yace "To shikenan nagode khairat zan tafi gidan nagaji."
"Kagaji dakayi aikin me?"
"Wallahi yau kasa hakuri nayi tun magrib nake tsaye anan, masallaci ka ɗai naje nayi Isha'i na dawo ina jiran ko zaki leqo in ganki."
Yadda yakai ƙarshen maganar yanuna mata lallai ya gaji, dan haruffan ma da ƙyar suke fita daga bakinsa, gashi muryar ta kuma yin kasa sosai, gefe guda kuma tana jin tausayin sa da ƙaunar sa aƙasan ranta.
"To Ma'aruf Allah ya hutadda gajiya, zaka iya tafiya sai Allah yasake hadamu da alkhairi, ka gaishe da gida."
Murmushi yayi ya soma tafiya kamar bayason taka ƙasa ita kuma ta nufi hanyar gidan.
******
Tun daga wannan ranar soyayya tashiga tsakanin su, irin wacce bata faɗuwa da fatar baki, kasan cewar bashi da aikinyi yasa idan abokanan sa suka tafi kasuwa ko gona sai ya zo gidansu khairat suyi hira, duk da bashi da Sana'ar yi hakan baya hanashi yimata kyauta irin ta takalmi, dankunne, da kuma kayan kwalliya.
******
Lokacin da inna kulu taji labarin soyayyar ba ƙaramar hauka tayiba, saboda tun asali taƙi jinin Ma'aruf ganin yanda ya sangarce baya aikin komi sai cima zaune.
Bakinta da kumfa ta fara magana."Wallahi kunyi kaɗan, yaushe zan ɗauki ƴata inbawa matsiyacin yaron nan, wanda bai san yaa ake neman kwabo ba. Tsinannen talaka ma ya fishi danshi yana ƙoƙarin nema ajiyewa ne dai ba yayi? To badaniba bazan yadda ƴa na gidan miji yana morarta ba amma lalurarta na kan iyayen ta ba. Keee khairat idan ma mafarki kike to ki farka, dan ban haifeki saboda soloɓiyon saurayin da iyayen sa suka gama sangarta rayuwarsa da rashin zuciya ba."
Ɗagowa khairat tayi tuni idanuwanta sun kawo ruwa, domin jin soyayyar Ma'aruf take ajinin jikinta, rabata da shi kamar rabata da rayuwarta neeee....
🤝🏼ZUCIYA DA SO
🥀🥀🥀#SARTSE
#NWA
#CMNT, VOTE SHARE
#GIRMAMAWA
YOU ARE READING
SARTSE
ActionSARTSE ba a iya tafiya kawai ake yinsa ba, wani Sartsen yakan zo acikin daƙushewa da kuma kankare mana burika da hasashen mu. Idan muka kalli rayuwa afai-fan hannun mu zamu ga wasu abubuwan dalili kawai suke buƙata dan wargaza ka da kuma tanadin d...