page 1

1.9K 117 11
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG❤ &😘Um Nass🏇

®NAGARTA WRI. ASSOCIATION

Page 1⃣

GURI L.G
Jahar jigawa...

Ko ina Na a ƙauyen mutane ne maza dattijai da samari, suke kai kawo a wajan tafiya, wanda mafiya yawan su suna sauri kamar sa kifa.

Abin zai baka mamaki idan kaga yanda suke nufar wata ƙatuwar bishiyar dake ƙofar wani gida.
Wanda tabirmi ne shimfiɗe awajan, ga kuma manyan mutane da suke zazzaune kowa fiskar sa dauke d fara'a.
Ɗaya gefen kuma matasa ne atsaye suna ta hira da dariya, kowa yasha wanka da gayu dai-dai na ƙauyen wanda da alama iya ƙure adaka sukayi.

Hakan ya ƙara tabbatar mana da cewar daurin aure ake shirin yi, da kuma alamun mahalatta ɗurin auren suna da alfarma agarin, musamman yanda wajan ya cika sosai da mutane.

"Ango! Ango"shine sunan d wani ya ƙira yana gyara zama hular sa akan sa.
Da Sauri Wanda aka ƙira da sunan Angon ya juyo. Tabbas ya amsa sunan sa na Angon, duba da yanda yasha sabon dinkin jamfa ga kuma hula zanna akan sa, sai faman washe haƙora yake.
"Audi ai ka kusan makara, dan ƙiris ya rage a ɗaura auren."
Dariya yayi yace "kai ma'aruf da doki kake, ai da sauran lokaci, dan naga liman bai ƙaraso ba."

Dariya ma'aruf yayi yana gyaɗa kansa, wanda hakan ya tabbatar ma da Audi bazai sake magana ba.
Girgiza kai yayi, sosai halayyar ma'aruf ke birgeshi."

*******
Zuciyar ta ke ingiza ta, tana ƙara azal-zalar ta, akan ta aikata koma meye wanda zai zama sila na wargajewar Auren da ba'a kai da ƙullashi ba, ko kadan bata k'aunar tabbatuwar wannan auren, hakan ya ƙara mata ƙwari gwuiwa akan tayi duk abin da zuciyar ta ke raya mata, wanda zai janyo ya wargaje auren, ya ragar-gazashi har abada.

Bokitin da yake cike da ruwa wanda iska da sanyin suka bi ta kansa, bashi da wata maraba d ruwan ƙan-ƙara.
Afusace ta dauko shi cikin ƙunan zuciya, ta fara nufar qofar gida, bata damu da yadda ruwan ke zuba daga bokitin yana jiƙataba, ita dai burinta kawai ta ƙarasa wajan ɗaurin auren.

Ido ta fara bazawa tana warasu cikin dan-dazon ƴan daurin auren.
Ƙam idanuwan ta suka tsaya akan mutanen da suke zaune ƙar-ƙashin bishiya, waɗanda sune jigon ɗaurin auren, adai-dai lokacin da liman ke zama suna gaisawa.

Murmushin mugunta tayi, cikin Sauri ta ƙarasa wajan, bata tsaya tunani komi ba ta daga bokitin ruwan ta sheƙa musu ajikin su.
Cikin tsorata da firgici suka miƙe tsamo-tsamo acikin ruwan, wanda tuni sanyin sa ya kadasu.
Kafin su gama al'ajabi muryar ta ta fara amsa Amo awajan.
"Tabdi jam! Ku atunanin ku, da ƙaramar ƙwaƙwalwar ku ta Baku, kunzo daurin aure ne?
Ku saurara, babu dan iskan ds ya isa ya ɗaurama ɗiya ta aure da sakaran yaron nan ma'aruf.
Wanda tuni kurarsa tayi kuka wajan sakarcin sa, da rashin zuciya, yaron da ko kadan baya iya juya sule ya koma kabbo, shi kuke tunanin ƙaƙaba ma diyata, saboda zalinci ya samu muhallin zama azukatanku."
Afusace take maganar bakin ta cike da kumfa ko tsayawa batayi.
"Innalillahi wa inna ilaihirraji'un" itace kalmar da malam Yakubu yake ta mai-maitawa, Wanda tuni idanuwan sa suka rikiɗa zuwa jajaye, hakan zai hasko maka iya ƙuncin da zuciyar sa take ciki.

"Haba kulu wani irin tozarci ne wanan? Gaban dinbun mutane kizo ki wulaƙanta ni."
Saurin dakatar da shi tayi "Dakata malam! Ai kaine kaso ka tozarta kanka, tun yaushe nake ce maka bana son wanan auran, amma kayi kunnen uwar shegu dani.
Dan haka yanzu babu ɗan ƙaniyar da zai aurar min da diya ga sakaran yaron nan."

Nufarta yayi cikin zafin rai da zumar kai mata bugu, cikin sauri mutanen suka tareshi.

Cikin hargitsattsiyar murya da kana jinta kasan ta damuwace malam Zakar ya fara magana "Kinyi gaskiya Hauwa'u, ba irin ɗana ya kamata ɗiyar ki ta aura ba, sai dai naso ace tun wuri nasamu wanan labarin wallahi da bazamu 6ata lokacin mu haka ba wajan zuwa da gayyato mutane."
Numfashi yaja ya furzar da iska mai zafi, kana yakai kallons ga Ma'aruf "Kai wuce muje gida. Na rantse da Allah koda ace khairat itace ɗaya ce mace data rage till awannan duniyar na haramta maka auren ta har abadan abadina."

Bai tabbatar da ya kaɗe ba sai yanzu, sai yanzu ne yake ganin tarin tulin wautar sa, baya tunanin yanada sauran farin ciki idan baya tareda Khairat.
   Wannan shi ake kira da Sartse mai katse tafiya. Furucin da mahaifin sa yayi shine yafi komai daga masa hankali.
Ɗagowa yayi yana kallon mahaifin sa, kafin ya sauƙe idanun sa a kan mahaifin Khairat, cike da rashin sanin abinyi dakuma abin cewa, da ƙyar ya iya buɗe bakin sa da yake jin yamasa nauyi yace "Baba kada kuyi min haka, ku taimaki rayuwa ta, kada kuyi kokarin raba zuciya da abin da take so, ka janye furucin ka akan auren, nayi alƙawarin zama mutun me zuciya da Neman nakansa Dan Allah kuji ƙaina."

Kallon sa mahaifin sa yayi yakuma maimaitawa
"Wallahi summa tallahi, ko bayan raina ban yadda da auren ka da Khairat ba.
   Babu wani mahaluki daya isa ya wulakanta ni tunda mahalicci na bai wulakanta niba."
Yana gama fadar haka yawuce kamar me shirin zuwa sama ta bakwai, babbar rigarsa sai cika take da iska.

Ma'aruf bashida maraba da mutum mutumi, ya sandare awurin, yarasa ta ina zai kamo zancen, ya ƙwallafa ransa da auren Khairat, ya gama tsara rayuwar su a gidan auren su. Ashe duka tanadin da yayi zai wargaje ya rushe acikin mintuna biyun da suka rage ta zama mallakin sa.

🥀🥀🥀
Wasa farin aiki...

Wanan daga alƙaluman mutum biyu yake zuwar muku UmNass da kuma SophieG.

SARTSEWhere stories live. Discover now