👣SARTSE👣
© by SophieG ❤& 😘Um Nass🏇
®NWA
Page 🔟
Khairat gidan goggo ta fara zuwa tadan zauna bayan sun gaisa ta tambaye ta ya Innar ta.
"Lafiya lau goggo, dama tace wai ki bani Sako zan tafi mata dashi."
"Eh wallahi dama Ina Neman Dan aike ne, sai gaki ma Allah yahutar dani."
Murmushi khairat tayi kafin tabata saqon tatafi.
Gidan yayarta ta nufa dan babu qarya tana neman abokin shawara, bataji akwai wani abu daze rabata da ma'aruf d'inta.
Murnan ganinta yayar tayi suka zauna se hira suke kafin khairat tace murya a sanyaye.
"Yaya shawara nazo nema gunki"
Gyara zama tayi tace "me kuma yafaru? ince dai ba matsalar inna bace har yanzu bata wuce ba?"
Qasa tayi da kanta tace"Yaaya itace, yanzu da zagin ma'aruf da tsinuwa muka karya kumallo, Babanmu bashida halin zama gida sai ta ringa masifar yana d'auremin gindi zan auri matsiyaci me matacciyar zuciya."
"Hmmm" tasauke ajiyar zuciya tace "Ni nasan inna bazata bari azauna lafiya ba, amma bana baki shawarar wulakanta soyayyar ma'aruf domin masoyinki ne na gaskiya, kuma na tabbatar iyayensa bazasu zuba mai Ido haka ba, dole zasu d'orashi kan ingantacciyar rayuwa, dan idan sune yau basune gobe ba, duk yadda suka kai ga kaunar sa bazasu ci gaba da kula dashi da iyalansa ba, kuma kema Ina baki shawara akan ki qarfafa mai gwiwa akan yatashi tsaye daneman nakansa. Inna kuma kibita ahankali ku rabu lafiya, domin uwa uwace koba komai kina Neman albarkar agareta. Tunda baba yana baki qwarin gwuiwa akan ma'aruf kada ki damu da ita kuma kici gaba da addu'a in sha Allah ma'aruf ne mijinki. Dan babu wani auren da yake qulluwa ba tare da an samu qalubale acikin sa ba. Allah ya kaimu ranar auren ki."
Gyad'a kanta tayi cike da gamsuwa da abinda Yaya Saddiqa ta fada mata, kuma taji duk rabin damuwar ta ta kau Dan haka tayi mata sallama tace zata tafi.
"Ke kin isa ma kitafi? Ki jira na sauqe girkin koda ba za kici ba Kya tafi dashi. Kuma d'an gidan ki nakeyi, harda man shanu kika qi tsayawa kinyiwa kanki."
Murmushi tayi tace "Zan ma Jira. Dan yau inna masifa takeji ko kud'in cefane da baba yabata bata dauka ba."
Dariya saddiqa tayi tace "Ki qyale ta zata gaji ta sauqo dan kanta ne, kinsan inna bata dogon fushi."
Kai ta jinjina "Haka ne kuma Yaya Saddiqa." Sun dad'e suna tattaunawa akan matsalar mahaifiyar tasu har zuwa lokacin da ta kammala girkin ta zubo musu suka ci cikin jin dad'i da annashuwa.
Haka ta koma gida cikeda qwarin gwiwa akan shawarwarin da Yaya saddiqa ta bata. Gefe guda tana kuma son ganin fuskar Ma'aruf d'inta amma babu yadda zatayi da qatuwar katangar da aka gindaya musu.
*****
'Ban garen ma'aruf kuwa yana can yasaka mahaifinsa agaba akan yaje nema Masa auren khairat.
Kansa a qasa muryarsa a sanyaye labbansa kamar baya motsasu yace "Baba dama kan zancen khairat ne Dan Allah kuje Ku nema min auren ta." Da qyar ya had'a kalmomin da yayi amfani dasu, ga mutuqar kunyar da tai masa dabai-bayi.
Sai zane yake aqasa yana sharewa kamar mai shirin maida wajan filin Zane.Dariya mlm Auwal yayi yana kallon Ma'@ruf aransa yana cewa "Hamdala ga Allah ko ba komi yana sa ran ma'aruf xai gyaru ya xama kamar ko wani mutum."
Afili kuma yayi hyaran murya yayi kulawa yake magana "shi mahaifin khairat d'in ne yace ka turo da iyayenka?"
Girgixa kai yayi cikin sarqewar murya yace "A'a ni kawai na gaji da tsayuwar hira, kullum fa sai naje gidansu yafi sau d'aya, kuma " "Yan unguwar har sun riqe sunana. Ni ban son yawan damuna da suke, kuma dai ina sonta sosai da sosai."
Ya qarasa maganar yana rufe fuskarsa da rigar mahaifinsa.
Dariya sosai yaba iyayen nasa musamman inna Abu "Ikon Allah! yau namiji ne da kunya haka?"
Shafa Kansa malam Auwalu yayi cikin yanayin da yake nuna tsantsar farin cikin sa yace "In sha Allah zanje nema maka Auren khairat. Na tabbata mahaifinta ba zai hanaka ba, dan haka daga yanxu ka fara shirin zama angon khairat."
Dad'i ne ya cika Ma'aruf ya qara rungume mahaifin sa, bakin sa Na motsi amma muryarsa ta gagara fitowa saboda farin ciko.
Bibbiga bayansa yake ahankali ya miqar da shi "Bari naje na samu aminina sai muje maka tambayar auren."
Ido inna ta fiddo waje "Daga fad'a sai tafiya kuma malam?"
Dariya yayi yace "Yo mi za'a jira kuma. Kin San da zafi-zafi akan bugi qarfe, kuma kinsan bana wasa akan duk abin da Ma'aruf yake so."
Yana gama fad'ar haka ya fice. Kai ta jinjina tana yalwata murmushi akan fuskarta, da kuma binsa da Addu'a. Yayin da ma'aruf yake dariya yana kallon inna....

YOU ARE READING
SARTSE
ActionSARTSE ba a iya tafiya kawai ake yinsa ba, wani Sartsen yakan zo acikin daƙushewa da kuma kankare mana burika da hasashen mu. Idan muka kalli rayuwa afai-fan hannun mu zamu ga wasu abubuwan dalili kawai suke buƙata dan wargaza ka da kuma tanadin d...