👣SARTSE👣
©UM NASS &SOPHIE G
®NAGARTA WRI. ASSOCIATION
PAGE 13
CI GABAN LABARI
Tun da suka shigo gidan ya samu waje a ƙarƙashin bishiyar darbejiyar da ke cike a gidan ya zauna, hawaye ke bin ƙuncinsa da kuma tarin tunanin rashin Khairat da yayi a lokacin da bai wuce minti guda ta zama mallakinsa ba.
'Wata irin ƙaddara ce wanan da bata zo minba sai a lokacin da na ke gab da cika burina? Yanzu shikenan na rasa khairat rasawa na har abada?' Tarin tunanin zucin da MA'ARUF YA KE YI, hawaye na ƙara ambaliya a kuncinsa.Sai da ya shafe fiye da awanni a wajan ba abin da ya ke banda hawaye, ya gaza gaskata abun da Inna Kulu ta masa a yau, gani ya ke kamar mafarki ne da ko yaushe zai iya farkawa, mi yasa Baba ya yanke hukuncin rabuwarsa da khairat?
Ji yayi an dafa kafaɗunsa wanda ya sashi ɗagowa, Mahaifiyarsa ce ta ke dafe da kafaɗarsa idanuwanta cike da tausayin Autan nata.
Ganinta da yayi ya sashi sakin wani sabon kukan yana ƙanƙameta "Mi yasa rayuwa ta zo min a haka Inna? Minene laifina da ya sa aka fasa aura min Khairat a lokacin da na ke gaf da mallakarta? shin laifina ne dan na zama mutum daban a garin nan Inna? mi muka rasa a garin nan ki duba mana Inna?"
Hawayen Fuskarsa ta goge masa tana murmushi "Baka da laifi ko ɗaya Ma'aruf, duk abin da aka maka ba laifinka ba ne namu ne da muka gaza baka damar zama namiji kamar ko wani namijin da kanyi fafutuka da rayuwa.
Madadin haka mu ke wanan fafutukar da sunan gatan maka da sauƙaƙa maka ababen da zasu zama wahala a gareka. Mun manta cewar gata baya hana kare kai, mun manta sangarci muke ma da zai sa ka samu tawaya a rayuwarka."Lumshe idanuwansa yayi yana jin sauƙar ko wata maaganarta a ƙasan zuciyarsa, amma har yanzu bai hango hakan a matsayin laifin iyayensa ba face ƙaddarar rayuwarsa da ta zo a bai-bai da ta sauran mutane.
"Inna ku ai soyayya kuka nuna min, ba ku gaza ba ta ko wani gefe, ni ne ma na gaza wajan kasa tsayuwa da tallafa muku a matsayinku na iyayena."Kai ta ke girgiza masa tana faɗaɗa murmushinta "Kaima baka gaza ba Ma'aruf, har yanzu kana da damar da zaka nunawa duniya kai namiji ne, zaka iya samun Khairat ko kuma wadda ta fita a cikin garin nan idan har ka sauya?"
Da mamaki ya ke kallon Mahaifiyarta sa "Ta ya hakan zai faru Inna? Bayan tsanar da mutane suka min da kuma mahaifiyar Khairat."
"Ka sauya! Ka fara cimma nasara! Ba zaka cimma muradanka ba, mutuƙar kana zama a duniyar lusarai, mafi munin tunanin da muke tilawarsa a ƙwaƙwalwarmu shine "Muna da wata dama".Ma'aruf! wanan rayuwa tamu da kake gani tana gadar da kasada mai yawa, sai dai mafi munin kasada shine "Zaman kashe wando". Nasara, ba'a jiranta, binta ake yi. Dole sai ka yunƙura dan ka zama mai nasara. Ko dai ka tashi dan ka zama mai Nasara, ko kuma ka kwanta dan ka zama mai asara.
Sai ka yi gwagwarmaya, kafin ka zama sananne. Ko kuma ka yi lalaci, ka zama mantacce. Ka yunƙura koda yunƙuri irin na zomo ne, nasara zata zo ma zuwa irin na zomo.
Kai ke da damar dabunta duniya da rayuwarka, ka wara hannunka da dukkanin ƙarfinka, ka kuma ƙawata zuciyarka da ƙarfin da furgici ko tsoro bai tatsata, daga nan ne zaka fahimci ko kai waye."Shuru ya yi yana nazartar kalaman Mahaifiyarsa, a idanuwanta ya ke ga, tsagwaran ƙarfafa gwuiwa da kuma jarumtar da ta ke fatan ganin a tare da shi.
"Ka shafe babin rayuwar da kayi da Khairat a baya, ka fuskanci yau ɗin da ta zama dalilin haramta maka aurenta, ka tsammaci samun khairat da wadda ta fita a lokacin da ka tashi a daga matsayin lusarin da duniya ta baka, idan ka zama mai nasara da gudu za'a fara binka."Murmushi yayi yana share hawayen da ke faman zuba a kan fuskarsa "in sha Allah daga yanzu zan sauya Inna, zan tashi daga Ma'aruf ɗin da aka sanni, daga yanzu kina kallona a matsayin sabon Ma'aruf ɗin da kika haifa ne.
Nagode sosai Innata Allah ya ƙara miki lafiya da nisan kwana."
Shafa kansa tayi, tana murmushin jin daɗin ganin sauyin da ta gani a kan fuskar ɗan nata "Ameen ɗana, Allah ya albarkaci sabuwar rayuwar da zaka fara."
"Ameen ya amsa."Daga nan ta tashi ta ɗauko masa abincinsa, karɓa yayi ya fara ci, duk da yana jin babu daɗi a ƙasan zuciyarsa, amma yana so ya nunama Inna ta sauya ɗin, ya kuma jinginar da wahalallan tunanin Khairta da ke mintsinin zuciyarsa.
*****
Dare.
Lokacin da Babansa kan zauna suna hira akan abun da ya shafi yau da kullum, shi da mahaifiyarsa, a wanan zaman sukan bawa junansu nishaɗi da labaran da kan ɗebe ma kansu kewa.
Sai dai a yau kowa yayi shuru ba abin tattaunawa, dan kuwa cike suke da alhinin tozarcin da Inna kulu ta musu a yau.
"Baba ina son na ɗebi kayan lambunka na fara shiga kasuwannin ƙauyukan da ke kusa da mu da ma na nesa da mu ina siyarwa."Bazata ya malam zakar ya ji maganar Ma'aruf ta sauƙa a kan kunnuwansa "Ka ce mi ne MA'ARUF?"
"Ina so ka bai sarin kayan lambunka kamar yanda kake bawa masara su siyar su kawo ma da kuɗin su ɗauki ribarsu, nima kamar haka na ke so ka bani, na maka alƙawalin kawoma kuɗinka ba tare da ƙwange ba."
Kai Malm Zakar ya jinjina "Ban ƙi ta maganarka ba Ma'aruf. Amma ta yaya ne zaka fara kasuwanci bayan ba sanin yanda ake yinsa ka yi ba, asalima ko kasuwa baka taɓa zuwa da zummar siyo abu ba balle ka saida. Mutane kuma da kake ganinsu ba amana gare su ba, kowa son zuciya da son kai ya masa yawa, da sunga kai baƙo ne a harkar ba wuya sun cuceka."
Murmushi ya yi yana tauna hannunsa a kan bakinsa "Baba ai kowa da haka ya koya, idan ka ce ba zan iya ba tun yanzu ka sa min tsoron hakan a raina, a cikin mutane ɗari na mutane akan samu mai kyau ko da ɗaya ne, ka min fatan haɗuwa da shi, ka kuma sanya min albarka da ƙwarin gwuiwa akan hakan."
Murmushi Malam Zakar ya yi yana shafa kan Ma'aruf "Allah ya sanya alkhairi a cikin kasuwancin da zaka fara, ya baka nasara a kan abin da za kayi.
Gobe sai mu je gidan gonar ka ga zaɓi abun da kake son farawa da shi.""Yauwa Babana nagode sosai, Allah ya ƙara girma."
"Ameen ya faɗa yana shafa kansa."
******
Washegari da sassafe Ma'aruf yayi sammako ya isa lambun mahaifin nasa, kayan miya ne barjuk mafiya gawansu nunannu ne, tun daga kan tumatir da tattasai har da kuɓewa ɗanya, sai attaruhu, sune ababen kayan miyan da ya fiya shukawa a lambun nasa, sauran kuma duk bishiyoyin kayan itaciya ne dangin su mangwaro da ayaba da lemon zaɓi, su kam da sauran lokaci dan basu nuna ba, amma sosai suka ƙawata lambun nasa wajan bashi kyakkyawar iska mai daɗi.
Kwando kusan biyar aka cika ma Ma'aruf da shi da dangin kayan miyan, kana aka lissafa kuɗi akan farashin sari dubu biyar kai, ya jinjina yana fatan dawowa da kuɗin kamar yanda ya karɓa, zuciyarsa cike da fargaba da shakkar abin da ka iya zuwa ya dawo.
🌷🌷🌷🌷🌷
INA fatan dai baku manta da labarin SARTSE BA, dan yanzu ya dawo da ƙarfinsa, mi kuka tsammata a cikin sauyin da aka samu na MA'ARUF? wata rayuwa kuka hasko masa a yanzu da kuma nan gaba, ina son ganin ruwan vote da cmnts dan samun ƙarafafa gwuiwa wajan baku labarin daki-daki.
daga alƙalamin
oum-nass $sophieG
YOU ARE READING
SARTSE
ActionSARTSE ba a iya tafiya kawai ake yinsa ba, wani Sartsen yakan zo acikin daƙushewa da kuma kankare mana burika da hasashen mu. Idan muka kalli rayuwa afai-fan hannun mu zamu ga wasu abubuwan dalili kawai suke buƙata dan wargaza ka da kuma tanadin d...