page 3

581 48 0
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG❤&😘Um Nass🏇

® NWA

Page 3⃣

Miƙewa tayi azabure kamar an mintsine ta "Ina wannan ba gaskiya bane,! Ina ko kadan ba'a fasa aurena da ma'aruf ba! Kima daina min irin wannan wasan inna na roƙoke ki, nasan bazaki tarwatsa min rayuwa ba." arikice take magana cikin ruɗewa.

Doketa tayi da ƙarfi "ke dallah ki barni da wanan soki burutsun, ko ina wasa dake ai ban taɓa miki akan wannan marar zuciyar yaron ba, dan haka kiyi gaggawar farkawa daga mafarkin da kike, dan tuni naci alwashi akan haramta miki auran sa har abada."

Hannu aka khairat ta ɗora ta zunduma wani uban ihu "wayyo Allah na shiga sittin na lalace, kin kashe ni da raina Inna"
Nan ta tsugunna tana shure-shure kafin wani lokaci tuni tayi bususu da jikinta da ƙasa.
Salati inna kulu ta fara rafka tana tafa hannu.,kafin ta wawuro sanda ta nufi khairat tana ta "kai jama'a kuzo ku tayani ganin yanda duniya ta lalace, bari na ɓanje miki kai idan yaso ki shiga dubu ma ba sittin ba, ai da naga auran ki da ma'aruf gara ace gawarki aka shimfiɗe min na gani." da zafi take maganar wanda gaba daya maƙotanta suna jinta, haka kuma suna tirr da lamarin na inna kulu, idan aka ɗauke ƴan tsirarun mutanen dake bin bayan ta.
Da gudu khairat ta tashi ta shige ɗaki ta bugo ƙofar dan ba ƙaramin aikin Innah kulu bane ta lakada mata Na jaki ba.

"Ja'irar Yarinya da kin tsaya ai da kinyi kuka mai dalili."ta faɗa tana jefar da sandar da ke hannun ta.
Kana ta zauna atsakar Gida tana karkaɗa ƙafa, wasai take jin zuciyar ta haka kuma ashirye take  da duk Wanda yace mata Cass tace kule.

"A huwo Aminiya ta! Ahayyeeee yirirrrrrriiii! Kaii barkan mu da arziƙi,  mun yada kwallon mangoro mun huta da k'udaje.,"

Wata komaɗaɗɗiyar mata ta faɗa, dana shigowa gidan inna kulu, da ganinta idanuwan ta atsaye fess imani zaiyi ƙaranci a tare da ita.

Baki inna kulu ta washe cikin ƙara jinjina ma kanta, da bajintar da tayi ayau ta fara magana "Ai tuni ƙasa ta ƙara buɗe kwallon da muka yada da ƙasa Marka. Yanzu fess nake jin zuciya ta, har yaushe zan tsaya na ƙare arziƙin dana tara awajan kasasshen namiji, Aradun Allah ɗiyata tafi ƙarfin auren jeka nayi ka."

Dariya Marka ta ƙara yi cikin yanayi Na zuga tace "shi yasafa naƙi zuwa bikin nan, saboda jinin yaron dana ƙi tun farko, da har inaga wautarki Na barin Khairat ta auri yaron da kaf garin nan yafi kowa rashin zuciyar neman na kansa, ashe ke kwanton ɓauna kikayi tashi ɗaya kika afka musu taron ya watse."

Jijjiga kai inna kulu tayi tana dariya ita kanta tasan yau ta kafa tarihi mai kyau a kauyen nan "Haba Marka! Wane mutum inji mutuwa, yanda na tsani yaron nan ma'aruf haka Na tsani mutuwata, yaro kamar an daddaƙa masa zuciyar kare yaci yaushe zan hada jini da shi."

"Kin min dai-dai, amma kuma ya kikayi da Khairat? Dan nasan tana bala'in sonsa. Har mamaki nake a kyau irin na Khairat amma ta mace akan wannan yaron, kamar da ya asirceta."

Zaɓulo da harshe inna kulu tayi alamar yanayin na bata takaici, da kuma ko in-kula akan hakan "Babu asiri ko kadan Marka, kin san irin su sunfi shiga rai, tuni na fatattaketa da sanda ta shige ɗaki, dan yanzuma ina jiyo gunjin kukan ta."

Dariya ta ƙarayi gami da miƙa mata hannu suka kashe "daɗina dake bakya ɗaukan lammura da sauqi, shi yasa ina samun labarin lalacewar auren nazo muyi murna tare."

Azuciyar ta kuma tana mata dariyar mugun ta da ganin wautar ta na ɓata auren diyarta da yaron da yafi kowa nutsuwa da kyau a ƙauyan, sanan kuma idan aka koma nasaba to iyayensa dattijai ne, ga kuma arzik'in noma, dan ko mai gari bazai fada musu arzik'iba.

'Ai tunda ɗiyata bata samu miji ba har yanzu, bazan bari khairat ta samu yin auren wuce sa'a ba muje ahaka ayita mutuwar kasko.'   duka wannan maganar da Marka keyi azuciyar ta ne, afili kuma ta daure da zuga inna kulu Wanda kaf garin bata da Aminiyar data wuce Marka itama.

Haka nan khairat tana jiyo hirar su wanda take jinta kamar feshin garwashi suke mata. Yanzu shikenan an rabata da ma'aruf.?
Wannan tambayace da ta riga data fidda ran sauyawar amsar ta daga eh zuwa a'a.
Kife kanta tayi taci gaba d kukanta Wanda yake tsuma zuciyar duk mai imani

******Ma'aruf fa?,

Mahaifin sa jansa yake tamkar raƙumi da akala, shikam ma'aruf binsa kawai yake yana tunano yadda rayuwar sa zata kasance idan bai auri Khairat ba.

Tsakar gidansu baban ya tsaya yace "Ka dawo hayyacinka ma'aruf, idan ba haka ba zaka tabbata mahaukaci."

Hawaye nabin fuskar sa yace "Baba na haukace! Wallahi na haukace, Khairat ce hankalina kuma kun rabani da ita."

"Ai kuwa ka tabbatar min kai jiƙyaƙƙe ne marar zuciya, a wulakanta iyayen ka agaban ka amma kazo da zancen banza, idan kakuma kiramin sunan wannan yarinyar saina tsine maka"

Afurgice ya ɗago da kallon sa ga Baban nasa "Baba ashe kuwa tsinuwarka zata tabbata akaina, dan bazan iya daina ambaton sunan khairat ba."

Kallon sa mahaifin nasa yayi kafin yajuya gun mahaifiyar sa data zama tamkar kurma.

Bakin cikin dake zuciyarta ya isheta, labulen dakinta kawai ta ɗage ta shige.

🥀🥀🥀🥀🥀🥀🥀

#SARTSE
#NWA
#CMNTS, VOTE AN SHARE
#GIRMAMAWA

©UmNass &SophieG

SARTSEWhere stories live. Discover now