page 6

420 35 1
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG❤&😘Um Nass🏇

®NWA

Page 6⃣

Shekaru sun ja ta yanda kwanaki ke gudu, kamar su cimma lokaci ɗaya amma babu abin da ya sauya daga halayyar Ma'aruf dan da yawan lokuta zamu ce gara mace da shi, ko ta fuskar kuzari ko kaɗan baya da shi.
Komi zaiyi yana yinsa ne a sanyaye da kuma lalaci.

Ahaka Auren abokin sa Audi ya zo kasancewar sa babban Abokinsa yasa yake iya jure hada-hadar mutane, sai dai sosai magan da mutane ke sashi ciwon kai.

Har mamaki yake yanda Audi ya samo mata, dan shi matan ma tsoronsu yake, ko ido suka hada da mace Indai ba cikin yayyansaba ko innarsa gabansa ya rinƙa faduwa kenan.

Kamar yarda al'ada take na biyan kudin yini da anko haka CE ta faru ga su Ma'aruf kasancewarsa babban abokin Audi na kusa, yasa sukaje da sauran abokanansu dan biyan kudin.

Komawa baya ma'aruf yayi dan baxai iya magana da tawagar amarya ba, wanda da alama kauɗinsu yayi yawa.

Bayan gaisuwar da sukayi kai tsaye suka yanke kuɗin da za'a basu 50k anko da yini, ido abokanan Audi suka fiddo waje cike da mamaki yayin da dariya ta ƙwacema ma'aruf dan shi kallon marasa hankali ya musu.
  "Anya kanku ƙalau yake?"  yayi maganar yana murmushi kafin ya dubi Mutari yace "Ka basu dubu ishirin, ban son hayaniyar nan kaina ciwo zai yi." cikin muryarsa mai sanyi da gajarta magana yayi wannan wanda da ganinta da ƙyar ya haɗata.

"Tabdijam! Mi dubu ashirin zata mana? Amma kai kam anyi ɗan wulaƙanci ba tambaya kaji mun yarda ko bamu yarda ba, zaka wani ce abamu haka. To wolla ta mana ƙaramta."

Juyowa yayi yana kallon ta tuni gaban sa ya faɗi dan  idan ba ƙarya yayi ba, zai iya cewa bai taɓa ganin yarinya mai kyau irin taba, amma kuma sai yaji yana tsoron mata magana ko musanta maganar ta.

"Mutari basu talatin daga haka kada ku ƙara musu." yana gama maganar ya juya ya tafi, dan jin zuciyar sa yake tana bugawa cike da tsoro da kuma wani irin yanayi, wanda bazai iya tan-tance ko na miye ba.

Binsa da kallo Khairat tayi tana jinjina yanda yake magana, cikin ta akwai sanyi da gajarta harrufa ko kadan baiyi kama da ɗan garin ba bashi da hayaniya.

Idan bata manta ba wannan shine ganin ta da shi na huɗu ko yaushe yana gefe yana wasa da hannun sa bai damu da kallon mutane ba balle hayaniyar da suke.
Mamakinta ya ƙaru lokacin da suka haɗa ido yayi saurin kawar da nasa kamar yaga dodo, hakan yasa taji nauyi da kunyar maganar data masa.
"Gashi ku karɓa" maganar da Mutari yayi ta dawo da khairat daga duniyar tunaninta.
Hannu tasa ta karɓa tana ƙirgawa, jinjina kai tayi tana juya kudin kafin tace "Yanzu da gaske 30k kaɗai zaku bamu, bayan kun san hidimar da zamuyi tana da yawa." muryarta ta koma mai sanyi ayanzu dan sam ba zata iya maganar da ta fara abayaba, yayin da sauran ƙawayen suka fara hayaniya akan lallai aƙara musu yawan kudin.
"Kuyi haƙuri da wanan ɗin, shine abin da Ma'aruf yace abaku, gashi ya riga daya tafi balle ace ya ƙara muku."

"Wane ne shi?"
Tambayar da ta jefo garesu cike da takaicin sa na tafiya ba tare da komi ya dai-daita ba.

"Shine yake riƙe da ragamar komi, saboda shine babban Abokin Audi."
Tsuka khairat tayi kana tabar wajan ba tare da ta ƙara magana ba amma azuciyar ta tana ƙiran 'Ɗan rainin hankali kawai, ita bama ta sanshi ba acikin jerin abokanan Audin ba, kodan ko yaushe yana gefe kamar basarake.'
Ita kadai take mgn tana bawa kanta amsa.

Haka akaci gaba da hidimar biki ba tare da sun sake haduwaba, sai dai sosai Khairat ke son ganin sa, yanayin sa na burgeta.
Amma abin da bata saniba ko yaushe Ma'aruf yana biye da ita, har sai ya ganta yake wucewa nasa wajan, ba tare da ya bari sun hada ido ba ko ta ganshi.

Lokacin da akazo ɗaukan amarya alokacinne Ma'aruf suka sake haduwa da khairat domin shima wani sabon cinikin ne akan ba zasu bada amarya ba sai an basu kudin ɗaukarta.

Murmushi yayi baice komi ba, yana jin suna ta fafatawa dasu Muutari akan abin da bai wuce dubu guda ba.
Can yaga lokaci na tafiya ya ƙaraso inda suke ba tare da yayi magana ba ya zaro kudi a aljihunsa fararen dubu biyu ne ya miƙa musu.

"Dare yayi nikam kada Innah taji shuru, ku ɗauki amaryar Ku kaita, ni Na tafi Na kwanta."

Yana gama fadar haka ya juya ya tafi, da kallo khairat ta bishi suma dai kallon ne nasu dan basu zata zai iya tafiya da wuri ba, gashi wanan karon ya ninka kudin da ake badawa.

Murmushi Mutari yayi yana ƙara jinjina halin Ma'aruf ɗin, wani lokacin kamar mutum wani lokacin kuma sai a hankali.

Ba'a ƙara ɓata lokaci ba suka kawo amaryar Audi aka kaita gidanta.

Ɓangaren ma'aruf bayan ya koma gida sallama kadai yayi wacce itama dan tazama dole ne, daga ɗaki inna ta amsa beyi kokarin shiga ya gaisheta ba sema itace tafito lokacin har yadaga labulen dakin sa zai shiga.

"Auta ya hidimar biki?" ta tambaya tana karasawa kusa dashi.

"Lafiya lau inna, nagaji ne shine zan kwanta.'

"Sannu amma bari Kaci abinci tukunna."
Ji yake duk yagaji da magana.

"Inna karki damu nakoshi, bacci kawai nake so nayi."

"To Allah ya tashemu lafiya." akan laɓɓan sa ya amsa ya shige ɗakin sa, ya kwanta kan katifara bayan yayi addu'ar kwanciya bacci.

Ya kusa awa ɗaya akwance ban da tunanin Khairat babu abin da yake, ba zai yi ƙarya ba, ta birgeshi sai dai wannan surutun nata da tsiwa.
Murmushi yayi daya tuna lokacin data harareshi tana murmushi tace
'Me dubu ashirin zata mana? amma Kai Kam anyi ɗan wulakanci.'
   Da irin wannan tunanin yaci rabin daren kafin ya samu damar yin bacci.

Washe gari karfe sha biyu muntari yazo ya janye Ma'aruf, zasuje cin tuwon amarya.

A ƙofar gidan suka zauna kan tabarma kasan bishiya sai hira suke, yayin da ma'aruf yazubawa kofar gidan Ido ko Allah zai sa Khairat ta kuma leƙowa, kamar yadda tayi basu Jima dazama ba tana neman dan aike.

Shafa fuskarsa yayi dole yayiwa tufkar hanci.

🥀🥀🥀🥀🥀
Kuyi hakuri darashin  posting jiya kamar yadda mukaso umnass ce tazama lazy😂 .

SARTSEحيث تعيش القصص. اكتشف الآن