page 7

400 35 4
                                    

👣SARTSE👣

©by $ophieG ❤&😘Um Nass🏇

®NWA

Page 7⃣

Juyar da kansa yayi daga kallon ƙofar gidan, yana bama zuciyarsa gargaɗi a kan halin da zata jefashi wanda bai san ina zai jefa shiba.

Sallama Khairat tayi gami da ajiye musu kwanukan abinci da tire.
Kallonta Ma'aruf yayi bai bari yayi nisa ba ya sunkuyar da kansa.

Gaidasu tayi duka suka amsa suna mata dariya da tsokanar ta, amma shi Ma'aruf baiyi magana ba, saima kawar da kansa yayi.

Kallonsa khairat tayi ta harareshi ganin yanda yayi kamar bai san anyi ruwan ta awajanba.
'Ɗan girman kai.' ta faɗa a ranta sai dai kalmar ta fito karaf akunnen Ma'aruf, dagowa yayi ya kalleta yana murmushi dan ya san da shi take.

Baki ta murguɗa masa ta tashi tabar wajan dan su samu damar cin abincin sosai.

Da kallo yabita yana murmushi wanda duk maganar da su Audi suke bai san mi suke faɗa ba, zuciyar sa ta ɗauke shi ta jefa shi awata duniyar daban.

Jijjigashi Mutari yayi da ƙarfi, furgigi yayi ya juya yana kallonsu.

"Yadai! Baka fara cin abinci ba ka tsaya kallo, ai har ta ɓacema. Idan sonta kake ka faɗa mata bayan mun gama cin abincin kawai."

Dariya sukayi gaba ɗayan su ganin yanda ya fidda ido waje, ba tare da yace komiba ya fara cakalar abinci.
Dariya suka sake masa wanda shima murmushi yake musu "Kuna da surutu fa, bakin ku baya gajiya ne ne?"
Ya tambaye su yana murmushi, da wuya kaga dariyar Ma'aruf amma ko yaushe fiskarsa ɗauke take da murmushi, haka maganar sa kamar ta ƴan koyo, sam baya iya jera harrufa hakan nada nasaba da doloncin sa da kuma gatan da ya samu.

Kafin yayi magana iyayen sa sun san mi yake so, hakan yasa bai fiya magana ba sai dai gani da ido, sosai yake ga ƙarfin halin mutane su zauna suna ta abu guda.

"Kai kuma baka gajiya da ƙunshe baki? Baka jin kana so kaima ka koyi magana iri tamu."

Girgiza kai yayi yana fidda ido kamar yaga abin tsoro "magana irin taku ai wuya gareta, ko amafarki ban sonta"

Dariya sukayi duka sanan sukaci gaba da cin abincin su da ɗauko wata hirar.

Miƙewa Ma'aruf yayi wanda dama cin nasa bai taka kara ya karyeba.

"Nikam na qoshi, Mutari ya kamata ka tashi haka kaima, ka buɗe ciki sai zuba loma da santi kake, agidan mutane"

"Barni naci na Allah kaimu nasan wani lokacin agidana za'aci. Kai Allah ya hutar da kai Audi da jiran tsakure akwano."  bakinsa cike da loma yake maganar.

Wanda ba kaɗan sautin ta yake fita ashaƙe dariya sukayi harda Ma'aruf duk da cewa sautin dariyar sa kaɗan ce.

Fita yayi ƙofar gida yana cewa "Ka sameni agida idan ka gama, ka haɗa tukuicin amarya harda nawa, amma fa ka tabbatar baka manta hannun ka ba."
Daga haka ya wuce, barinsu yayi suna dariya shima murmushi yake tayi sosai yanayin yake birgeshi.

Kasa tafiya yayi ya tsaya aƙofar gidan kamar mai jiran wani abu.
Tsayuwarsa ba daɗewa Khairat ta fito ita da ƙawayen ta guda biyu, da alama suna cikin jerin ƙawayen amarya amma baxai iya tan-tancesu ba kasancewar ba ganin ƙurulla ya musuba.

Gaida shi sauran ƙawayen nata sukayi ya amsa da murmushi afiskarsa, yayin da Khairat ta bishi da Harar  'wato ita ya rainama hankali yaqi amsa gaisuwarta ɗazu, amma su harda murmushi ya musu.'
Ƙwafa tayi ta jijjiga kai, wanda bata san tayi hakan ba saida taji ƙawayen nata na tambayar ta ko lafiya?
Dariyar yaƙe tayi tana son shiririntar da maganar "Wani abu naa tuna."

Bin bayansu Ma'aruf yayi yana murmushi ba tare da sanin abin da zai ce musu ba.

Laure da waiwayenta uku tana ganin sa abayansu yasa tacewa khairat.
  "Khairat wannan fa mu yake bi, kuma sai murmushi yake dokawa."

Dariya Khairat tayi tace "Ke dai ƙyale sarkin girman kai, magana gareshi yakasa fada. Muje dai yanzu na cire wannan kayan, muje kasuwar can ta hayi mu siyo rake."

"Khairat to kiyi Masa magana mana."

"Chab! Allah ya kiyaye, ko zanyi ai sai na gama wana shi, ki barshi kawai da murmushin da yake fama dashi kamar rogo."

Dariya ƴan matan sukayi su kace "Amma khairat bakida kirki."

Bata tanka musu ba dan  sun iso gida, basu jimaba suka fito ta sauya kaya dan wancen manja ya zuba ajiki.

Yana tsaye ƙofar gidan yana Saka wasiƙar jaki ya jiyo shewarsu da sauri ya ɓuya bayan bishiyar kuka Dake ƙofar gidan.

Da ƙyar ya jure ya koma gida daniyyar gobe idan ya ganta in sha Allah duk yadda za ayi sai ya mata magana.

Koda ya koma gida ɗakin sa ya shige ya faɗa tafkin tunanin khairat, kayan data saka ɗazu sun karɓeta sosai in sha Allah irin su zai mata acikin lefen ta.

Washe gari bayan azahar Audi ya biyo masa wai yazo za suje yiwa iyayen amarya godiya.

Irin wannan murmushin daya saba yi kawai yayi yaje ya chanjo kaya, suka tafi daga can gidan amaryar suka wuce har suna mamakin yadda ma'aruf bece ya gajiba.

Shi kuma so kawai yake yayi tozali da khairat, a inda suka saba zama nan suka zauna hira banda ma'aruf daya rakube gefe yana tunanin khairat haɗi da zubawa kofar gidan ido ganin kamar bazata fito ba yasa shi miqewa ya je kofar gidan ya tura yaro akira masa khairat.

Ko yauma umNass ce ta ɓata lokaci nidai babu ruwana😂.

🥀🥀🥀🥀

#SARTSE
#NWA
#CMNTS, VOTE SHARE
#GIRMAMAWA

SARTSEDove le storie prendono vita. Scoprilo ora