page 9

418 52 2
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG❤ & 😘Um Nass🏇

®NWA

Page 9⃣

"Kiyi haƙuri Inna, ina jin son Ma'aruf acikin ruhi na! koya kika so rabani da shi zan sha Wahala, ni ban damu da wani abun hannun saba ko rashin zuciyar sa. Kawai dai shi nake so innah." tana maganar tana hawaye kamar tseren su akeyi.

Salati inna kulu tasa tana tafa hannu. "Na shiga uku ni Hauwa'u! Yanzu har mun zo cikin zamanin da Yarinya budurwa zata cema uwar data halallaƙota duniya ga mijin da take so, ahakama suna musayar yawu tsakanin su."

Sunkuyar da kai Khairat tayi ƙasa hawaye naci gaba da xuba a idonta. 'akan Ma'aruf zata iya jure ko wani ƙalubale ne amma banda rabuwa da shi.'

"Kiyi haƙuri inna, naga ke mahaifiyata ce, inaga zakifi kowa son Ma'aruf kasancewar sa wanda nake so aduka wanan garin. Ki duba nutsuwar sa da hankalin sa, karki duba raunin da ke tare da shi."

Galala Innah kulu take kalon Khairat kafin ta cire silifas ɗin dake ƙafarta ta wurga mata "Ungo nan ƴar ƙaniyar nan, naƙi na duba nutsuwar tasa. Yo in banda shashanci nutsuwar zakusa agaba kuna caccaka? Kul Na ƙara jin maganar Ma'aruf abakin ki, zan iya tayaki son ko wani Abu aduniyar nan amma banda auren lusarin yaro, wanda zuciyar sa ta gama mutuwa. Yo a ɗauri kashi ko a ɓataa igiya."
 
Kuka sosai ta farayi mai sauti wanda ya ƙara ƙular da Innah kulu ta rarimi muciya ta iyo kan Khairat zata ranbatsa mata, ji tayi an riƙe muciyar a lokacin da khairat take tsandara ihu dan ta san ba makawa rushe mata kai innah kulu zatayi.

"Haba Hauwa'u! Yaushe ne zaki girma kibar duke-duke? Yanzu da Allah bai kawo ni ba sai ki fasa mata kai ko? Haba wanan masifa har Innah?"
Malam Yakubu yake faɗa fiskarsa cike da ɓacin rai.

Harar sa tayi tana hucin masifa kamar wanda tayi tseren gudu.

"Barni na banje ja'irar yarinyar nan, har dan lalacewa tayi yawa ta rasa Wanda zata so sai yaron mlm Auwalu, wanda ya gama sangarcewa da rashin nema, ni har tantama nake akansa anya ba mace akaso yi ba yazo a namiji? Ko kuma rufarmu iyayensa sukeyi, dan ko kad'an bashi da zubin maza ga axababben girman kai acikin sa, magana wanan wuya take masa kamar ɗan gidan shugaban qasa, da ta aureshi gara na shimfiɗeta na huta."

  Ido malam yakubu ya zaro cike da mamaki da alhinin maganar matar tasa "Subhanallahi! Hauwa'u wanan fa saɓo kikeyi, har abin naki yakai kisa shakku da mantuwa ga Allah, wanda ya halicci komi da komi.to maxa kiyi gaggawar tuba da dawowa hayyacinki idan b so kike son zuciya ya kaiki ga shiga wutar jahannama ba."

Rud'ewa Innah kulu tayi dan Idan akwai abin data fi tsoro shine taji an anbata mata wutar jahannama akwai lkc da take xuwa jin wa'axi da Azumi tunda malamin yayi bayanin wutar jahannama ta shiga tsoro dan kwana tayi tana firgita aranar. Duk abin da take akace mata wutar jahannama sosai take nutsuwa ta rud'e tuni yanxu ma ta kai kanta qasa tana turgu6a goshinta qasa tana kiran "istigfari ya Allah"

Kallonta malam yakubu yayi cike da takaici ga kuma dariyar data bashi har bata san mi zatace ba.

"Ai ba haka ake cewa ba."
Ya fada mata yana qunshe dariyarsa

"To ya ake cewa malam? Nifa bana son magana da shiga wuta. Allah Na tuba ka yafe min ba ina nuna gajiyawar ka bane, akan halittar ka."

  "Astagfirullaha wa Atubu ilaihi haka xaki CE".
"To to bari Na iyo Alwala sai naxo Na fara."

Gyaran murya yayi yace "kafin nan ki fita a sha'anin yarinyar nan, ba ruwanki da soyayyarsu idan Allah yayi yaron nan shine mijinta ba yanda kika iya. Naki sa musu albarka da addu'a tunda tana sonsa ai shikenan, Sam baxan jure wanan tsangwamar da kike mataba."

Yana gama fadar haka yaja hannun khairat xuwa daki ba tare da ya qara bi ta kan Innah kulu ba balle yaga halin da take ciki.

Da ido ta bisu da kallo tana qwafa koda xa'a Mutu sai ta rushe wanan soyayyar.
Buta ta xara ta fara alwala tana bari ta tuba kafin tayi tunanin abin da xatayi.

********
  Soyayya gamon jini d'aurin gindin da khairat ta samu awajan mahaifinta ya qara mata qwarin qwuiwar sakankancewa akan babu mai rabata da shi, koda mutuwa xatayi addu'a ta jinkirta musu Na wani lkc xuwa cunma burinsu ko kuma ta d'aukesu tare.

Haka kuma a6angaran ma'@ruf shima Wannan ragwantar tabi jini da jikinsa kamar yadda soyayyar khairat ta mamaye 'bargonsa,
Ji yake baxai iya komiba idan aka rabashi da ita, duk kuwa da cewar ba komi yake assalawa ba a cikin tafiyar soyayyar tasu.

Sai dai sosai maganarsa ta qaru agida da waje, xancan kullum daya Khairat khairat Innah Abu mahaifiyarsa da baba Auwalu mahaifinsa kullum cikin hirarta suke. Har sun haddace labarin ta ko kunyarsu bayaji. Haka yayyansa ma'u da binto abin ya xame musu jiki.

Suna farin ciki ganin yanda d'an uwansu yake sakewa dasu yanxu sa6anin da ko gaisuwa sai dai su sumasa.
Sukam gara wasai suna qara shima khairat albarka haka suna sonta ko banxa ta gyarama dan uwansu rayuwarsa.

****
Sai dai a6angaran inna kulu labarin yasha ban-ban.
Saboda ta d'aura niyyan kawowa wannan soyayya cikas yayin da mahaifin khairat yake qarfafa mata gwuiwa akan kada tayiwa masoyinta wulakanci kuma insha Allah batada miji se ma'aruf.

Kamar ko wani lokaci yanxuma ta tasa khairat agaba tana mata hud'uba akan aibun ma'@ruf
    "Wallahi khairat kimaida hankalin ki jikin ki, kibar ganin wai baban ki na tare miki babu abinda bazan iyayi ba aduniyar nan, dan ko bana kaunar wannan shegen yaron da xcyrsa ta gama mutuwa."

" Inna Dan Allah ki daina zaginsa, iyayen sa fa zasu tsaya Masa kuma Dan baya aiki ko Sana'ar komai ba shi ke nufin haka rayuwar sa zata qareba." cikin sanyin murya Khairat take magana dan wanan sukan ra'ayin Na Innah yana qona mata zuciya.

"Khairat yaushe kike da tabbacin hakan? Ina magana kinayi akan wanan yaron ba zaki daina jayayya dani ba? Dan uban ki idan iyayensa sun tsaya Masa sai akace idan kukayi auren zasu ci gaba da tsaya muku ko?" ranta ya fara 'baci dama hirar ba d'orewa takeba.

Kallon inna tayi tace "To ai umma d'ansu ne, suna sonsa da abinda yake so bazasu barmu mu wulakanta ba." tayi murmushi mai sauti "Dan ma bakiga yanda iyayensa suke sona ba kamar fa su goyani, haka yayyansa ma kullum cikin gaidani suke. Gaskiya suna sona sosai."

Baki ta saki tana qara qan-qance idon ta cikin takaici da haushin ta tace "da yake su suke aurenki ba, yo ai dole su so ki tunda kina son dolon d'ansu. Ko ba komi ya samu qawar wasan kara, abin takaicin ma ya tumurmushe ki ad'aki yana kwance iyayensa su ciyar dake. Da yake sune suke morar ki ko? To baki isaba, wallahi kunyi kad'an duk wani shege dayake cewa zaki auri ma'aruf zamu zuba ni da shi, naga in wani d'an iskanne ya haifar min ke. Ina ga annabi kina runtse Ido, meye amfanin ka aurar da "ya kaxo kana hidimarta, ga yayarki can ta kere sa'a amma ke naga alamar zuciyarki ta soma qeqashewa, kuma Ina tabbatar miki da ki kiyaye ni yafi miki arziki da zaman lafiya."

tashi khairat tayi ganin idan taci gaba da Zama agidan zuciyarta fashewa zatayi yasa tace "inna natafi gidan goggo Na kwana biyu banjeba."

Harara ta mata"kyaji da shi dai kice kin gaji da surutuna kin tashi nayi ta yi ni kadai kamar karya."

Murmushi khairat tayi dan fadan inna kulun ya daina bata haushi yanzu "A'a wace ni innah ai maganarki akwai armashi kamar sarkin da bai gadaba."

Dariya inna tayi  jin erta ta hadata da sarki "to Allah ya kiyaye, kice tabaki saqon, dama ko bakije ba ina shirin aikenki."

Tafiya tayi tana dariya 'ho inna daru abin da bata saniba mutuwa kadai CE xata rabani da ma'@ruf inaji araina xai samu 'DAUKAKA asanadin soyayyata."

*****

Kuyi hqr da wanan En uwa yau kam matsalar bamu da lkcn sabunta muku labarin ne, shi yasa kukaji shuru.

Amma muga ruwan girmamawarku ta hanyar yin vote da cmnts d'inku.

Mungode.

SARTSEWhere stories live. Discover now