page 12

627 55 2
                                    

👣SARTSE

©SophieG❤&😘Um Nass🏇

®NWA

Page 1⃣2⃣

"Ka kashe ni da raina Malam?Ƴar tawa ka ɗauka ɗun-gurun-gum ka bawa mai matacciyar zuciya? To wallahi ba zata saɓuɓa sai na nuna maka nima ina da iko da khairat."

Malam dai ɗakin sa ya shige ya barta saj sambatu take, khairat da ɗaki tana jinsu wani irin daɗi taji, nan tashiga yiwa Allah godiya akan cikar burin ta.

"Ai dole ka ƙyaleni ina ta zuba. Tun da kayi abin da ranka ke so, kuma burin ka ya cika na baƙan ta min rai, dama kana cewa ni sha tara ce, wallahi sai na nuna ma na cika sha taran, mu zuba ni da kai ɗan halak ka fasa."

Ita kanta bata san iya awannin data ɗauka tana masifa ba, gajiya tayi dan dole tayi shiru, ganin babu wanda ya tanka mata.

Da la'asar Malam yafito tana zaune waje tasa khairat agaba tana masifa.

"Ke yanzu sai kika yadda ki auri me matacciyar zuciya? To shike nan tunda shi kika zaɓa, duk abin da ya taso karki sake kizo guna, na tsame hannuna acikin lamarin ki."

Malam ya kallesu yace "Ke Khairat ƙyale ta kinji, ai kina da gatan ki a duniya, balle nasan in sha Allah babu wani mummuna al'amari da zai faru a wannan auren kiyi ta addua kinji?"
Tana kallon kasa tace "To Baba, In sha Allah zan ci gaba da addu'ar."

Nan fa yata da sabon balli a wajan inna kulu inda take shiga banan take fita ba, malam dai tuni ya kama gaban sa yabar mata gidan, sanin bakinta baya gajiya da masifa balle kuma an taɓo ta.

Gidan yayan sa ya nufa Malam Iro akan Neman shawarar yadda za suyi.

Murna fal zuciyar sa yace "Masha Allah! ALHAMDULILLAH. Malam ai ba zamu jira awani tsaya ɓata lokaci ba,  sai a kira shi mahaifin Ma'aruu ɗin idan ashirye suke ayi bikin auren zuwa nan da sati uku, ko ya ka gani?"

"A'a yayi wallahi saj dai matsalar daga kulu ne, dan har tace ta cire hannunta a lamarin khairat ɗin."

Murmushi yayi yace "Ai mata haka suke ba'a gane musu alokacin da suka ƙi abu, in sha Allah zata sauƙo tunda ita tahaifi ƴar ta ba zata so tagan ta a wulaƙance ba."

"Hakane kuma Yaya, insha Allah yanzu zan je in aika yaro asanar dasu nagode sosai."

Basu wani samu matsala da iyayen Ma'aruf ba domin ashirye suke. Nan take suka fara gyaran ɓangarain da ma'aruf ɗin zai zauna, yayyen sa suka je hado kayan lefe dai-dai iyawar su.

Inna kulu taji labarin amma tayi kamar bata san mi suke yi ba.

Ma'aruf kuwa shida abokanan sa suka zo aka yanke kuɗin da zasu bayar, amarya sai shiri ake babu kama hannun yaro.

Sunyi ƴan al'adodinsu na biki kowa sai murna yake, inna kulu tayi kamar tafara san auren komai da ita ake yi.

Yau dinnan data wargaza ɗaurin auren babu wanda yayi tunanin rashin mutunci ta yakai har haka, tun cikin dare ta hanasu bacci banda tsinuwa babu abinda ma'aruf ya kesha agurinta amma duk da haka Malam bai kulata ba.

Amma da yake ƴar duniya ce washe gari bata nunawa ƴan biki komai ba, sai binsu take ana haba-haba da mutane, ita dakanta ta haɗawa amarya ruwan lalle tayi wanka dashi.

"Ina khairat take? Maza zo kiyi wanka mutane sun fara zuwa, amma kina zaune duƙun-duƙun kamar ba amaryar Ma'aruu ba." inna kulu ta faɗa tana faɗaɗa fara'arta.

Ba ƙaramin mamaki yakama khairat ba, kuma haka nan taji gabanta ya faɗi da wanan sabon sauyin na INNA sai ta mata wani ban-barakwai.

Haka tayi wankan ta shiga ɗakin Malam da aka ajiye kayan lefen ta acan, inna tabata mai da turare akan ta fesa.

"Karɓi ki shafa sai kije ayi kitson abu yaƙi-ci-yaƙi-cinyewa sai dangin mijin sunzo sun sameki a yamutse."

Kallon tuhuma mai kama da rashin yadda khairat tayi mata hakanan ta yi komai ta saka kayan ta fito za'a ci gaba da kitson.

Daga waje kowa ya hallara  dangin ango dana amarya ana jiran a ɗaura aure.

Daga cikin gida kuwa khairat tana zaune da kawayen ta ana hira suna kitso, tasha kwalliya taga inna kulu ta ɗauki bokiti da ruwa sai dai bata damu ba dan ganin ta nufi toilet da alama amfani zata yi da ruwan.

Wannan itace mummunar rana agurin khairat da ma'aruf, ranar da inna kulu ta watsa taron ɗaurin auren su.

Mi yasa inna ta kunyata kanta? Mi yasa ta wulaƙanta Baba? Mi yasa ta mu zanta ƴan ɗaurin auren? Mi yasa ta zaɓi ta muzgunawa rayuwar ƙarta?

Saboda ma'aruf bashi da Sana'ar yi koda iyayen sa zasu ci gaba da ɗawainiya da shi da iyalansa. Dole wata rana zasu bar duniya ita kuma bata yadda zuri'arta ta wulaƙanta ba, bata yadda tabawa ƴarta ragon namiji ba dan acewarta Ma'aruf rako Maza yayi.

🌾🌾🌾🌾🌾

Alhmdlh anan muka kawo gundarin labarin, zamu dakata kuma sai zuwa bayan sallah in sha ALLAH.
mun gode da bibbiyar labarinmu da kuke, duk da ba kwa samun published nasa akan lkc.
hakan yasa muka ajiye muku kalmar girmamawa mai yawa acikin tafiyar.

SARTSEWhere stories live. Discover now