page 11

372 29 0
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG ❤& 😘Um Nass🏇

®NWA

Page 1⃣1⃣

Murmushi inna tayi tana kallon yanda ma'aruf ke ta washe Baki kamar an masa bushara da kujerar makka.
"To rufe bakin haka mana kada ya yage saboda dariya."

Saurin rufe idanuwan sa yayi da hannayen sa, wata sabuwar kunyar innah ce ta dirar masa alokacin.

Haɓa ta riƙe cike da mamaki "Ikon Allah! Yau kuma ni kake jin kunya?"
Kai ya gyaɗa mata yana ƙara rufe fuskar sa.

Dariya sosai tayi tana ƙara godema Allah akan rahamar daya mata, da kuma tarin ni'imominsa gareta, ciki kuwa harda kyautar tilon ɗan nata wanda ta fidda rai da samun sa.

Haƙiƙa duk wani mai rai ango ne, haka ɗan Adam koya yake wajen ƙas-ƙanci baya fidda rai da rahamar ubangijin sa. Ko kaɗan bata taɓa kawowa Ma'aruf aure akur-kusa ba, bama wai aure ba ayadda take masa kallon mutum da ban, mai halayya mabam-banciya da sauran mazaje masu ji da ƙumajin su gami da jarumta saɓanin nata yaron ko kaɗan baya hasko masa rayuwa da macen da zata so shi da gaskiya
ba.

Amma cikin hikima da iko na ALLAH sai ga khairat ta faɗo cikin rayuwar sa, cike da zallar ƙaunar da babu algus acikinta. Hakan yasa take son khairat har zuciyar ta, take kuma girmamata da burin kyautata mata da dukkanin abin data mallaka.

"Inna kukan mi kike haka? Ko bakya son aurena da khairat ne?"
Muryar Ma'Aruf ta doki dodon kunnuwan inna Abu. Tuni ta dawo daga duniyar tunanin data shilla tana kai kallonta ga Ma'Aruf.

Murmushi tayi tana shafa kumatun ta, hawaye taji wanda bata san da gudanarsa ba "ko kaɗan ba kuka nake ba, asalima ban san hawayen ya zuba a idanuwana ba."
Shafa kansa tayi cike da kulawa "Sai dai ina mai tabbatar maka Cewar ina tsananin farin ciki ayau, ina fatan tsawon rayuwa dan naga auranka da khairat. Domin na kyautata mata akan alkhairin data min na auran tilon ɗana da tayi."

Rungume Inna ABU yayi yana dariya fuskarsa kuma ya rufeta da rigar ta. itama dariyar tayi saboda har yanxu ma'aruf bashi da maraba da lokacin ƙuruciyar sa "Ya kamata kasan ka girma fa yanzu, ka ɗaga ni, kada ka karya ni."

Kafaɗar sa ya maƙale"um-um Innah, nifa har yanxu yaro ne "
  Shafa Kansa tayi ba tare da ta Ƙara cewa komiba. Amma azuciyar ta tana jim ƙaunar sa na ratsata.

*******

Lokacin da mlm Auwal ya fita bai tsaya ako ina ba sai agidan yayansa anan ya sanar dashi labarim nemawa Ma'Aruf aure hakan ba ƙaramin daɗi ya masa ba.

Basu ɓata lokaci ba suka tafi gidan su khairat ɗin, kasancewar almuru yayi sun riski malam yakubu agida.

Cike da girmamawa suka gaisa ganin ba baƙin fuska bane awajansa ya shigar dasu har zaure yana ƙoƙarin shimfiɗa tabirma .

"Maraba! maraban ku da zuwa" Kalmar da yake ta mai-maitawa kenan fiskar sa cike da fara'a

"Bismillah ga waje Ku xauna."
zama sukayi suna godiya a gareshi, daga nan suka sake gaisawa.

Anan Yayan mlm Auwalu ya gabatar da buƙatar su akan nemawa Ma'aruf aure da suka zo tare da fatan ba'ayi ma Khairat miji ba."

Fara'arsa ce ta ƙara yawaita "Ikon Allah! Ai babu komi wallahi, ko kaɗan banm khairat miji ba. Dan na daɗe da yima Ma'Aruu alƙawalin auren Khairat duk lokacin daya shirya, duba da yanda suke son junansu. Amma tunda kunzo zan ƙara tabbatar muku Na bama Ma'Aruu auren Khairat duk lokacin da yaso koda kuwa bana raye ne."

Dariya sukayi ta nuna jin daɗin  dattakun da mlm Yakubu ya musu "to Alhamdulillah mun gode sosai, mun kuma ji daɗin yanda ka karɓi buƙatar mu. Allah ya saka da alkhairi yasa albarka acikin lamarin. Kuma in sha Allah kana raye xa'ayi har ka dauki jikokin ka."

Mahaifin Ma'aruf ya faɗa yana ɗara faɗaɗa fara'arsa.
"Ammafa bama son auren.ya ɗauki lokaci"
Jin-jina kai mahaifin khairat yayi "Babu damuwa Zamu tattauna da ƳAn uwana duk abin da suka yanke zan sanar daku."

Godiya suka masa sosai daga nan suka tafi.

Har qofar Gida ya rakasu fiskarsa ɗauke da fara'a ya naɗe tabarmar kana ya shiga Gida.
Da fara'a Innah kulu ta taresa take tambayar sa " Su waye suka zo ne ina ta jiyo dariyar ku ai? Nace yau mun tashi da farar sa'a kenan?"

Dariya ta bashi ya jin-jina kai shima "Sosai kuwa Hauwa'u, manema auren Khairat ne sukazo tambayar aurenta?"

Cikin zaƙuwa tace "Su waye ne malam?"

Murmushi ya ƙara yi kana ya ja kujera ya zauna "iyayen Ma'aruu ne mlm auwalu da yayansa suka zo nema masa auren khairat "

Ji tayi ranta yayi bala'in ɓaci cikin takaici tayi tsuka "Mtsss
! Na ZAta wani mutumin ƙwarai ne ya futo, kuma kai mi ka faɗa musu?"

"Cewa nayi na bashi duniya da lahira, ko bayan raina bata da mijin daya wuce shi."

Ido ta fuddo waje cikin tashin hankali da rudani "Mi ka bashi malam?"

Cikin farin ciki ya ɗauko goron sa ya tauna fiskarsa ƙunshe da fara'a yake magana "Auren khairat ma bashi duk lokacin daya shirya yaxo adaura musu aure."

Daɓass ta zauna  aƙasa cikin murya mai rauni tayi magana "ka karni da raina kawai zaka ce!"

🌷🌷🌷🌷🌷

SARTSEDonde viven las historias. Descúbrelo ahora