page 5

514 34 2
                                    

👣SARTSE👣

©by SophieG❤&😘Um Nass🏇

®NWA

Page 5⃣

  Fitowa Inna Kulu tayi daga ɗaki taga Malam Yakubu Mahaifin Khairat ya rafka uban tagumi hannu bibbiyu, dariya tayi ta ƙara da shewa "Ahayeeee lallai masu wahala daban suke arayuwa, aini yau zuciya ta karr, kuma ban san mutum na cikin damuwa ba sai ya faɗi yana ƙafewar fitar rai. Dama tass nake ganin ka, da cutar da kake shirin yi min na aurawa ɗiyata namijin da yafi kowa kassara da rashin madafa agarin nan."
Ɗagowa yayi ya kalle ta bai tanka mata ba, dan tsab zuciyar sa zata iya bashi umarnin yi mata dukan kawo wuƙa, abin da bai taɓa yi ba kenan, ba kuma ya fatan yi.
Ƙarasawa kusa da shi tayi, nan taga kwanon abinci agabansa bai ci ba "Aikin ɓirr inji tusa, ciki ai ba'a masa shamaki da abinci, idan yaji wuya tuni zaka wawuri kwano ka nema ka zura."
Tashi yayi ya zura takalmin sa ya kakkarɗai rigar sa "Kiyi duk abin da kike son yi Hauwa'u, saura ƙiriss lokaci yazo da komi zai sauya, bazan tsaya ina ɓata lokaci atare da ke ba, har yanzu baki san kanki ba, amma ki bari nawa labarin agaba zai sha bam-bam da tsammanin ko wani tunanin ki." yana gama faɗar haka ya fice ya barta.

Hakan ba ƙaramin fusata yayi ba, taci gaba da kururuwar masifa dan ba kasaifai Malam yakubu ke maida mata da martanin magana ba "Ni ai nafi ƙarfin mutum wallahi duk inda kaje zaka dawo ka sameni, idanma wani ɗan iskan ke zugaka zanyi maganin sa, dan bana tsoron ta kife wallahi."
Juyawa tayi da niyar tafiya idon ta ya kai ga khairat Wanda ayanzu bata da maraba da mutum-mutumi, Sam bata da wani amfani, iyakarta tabi mutum da ido shima ba fahimtar mi ake takeba.
"Mtssss wahalalliya Allah ya ganar da kee gsky." ta fada gami da ranƙwashin kanta.
Dafe kanta tayi Wanda taji zafi amma bata iya fahimtar komiba akan dalilin dukan nata da tayi.
Hawaye ne ya sauƙo daga kwarmin idonta bata damu ta gogeshi ba, amma tana tantama aranta anya kuwa Innah kulu itace mahaifiyarta? Tabbas zata iya cewa ba ɗiyarta bace, amma kamannin da suka iyo shike share mata ko wata irin tantamar dake zuciyarta.
  Azkar taci gaba dayi azuciyarta domin samun sauƙin abin dake damunta.

****
Bari muyi waiwaye Adon tafiya

Asalin labari:-

GURI ƙaramar hukuma wadda ke ƙarƙashin jahar jigawa, tana ɗaya daga cikin local government guda biyar da jigawa take da su.
Sai dai ta kasance koma baya ta fiskar cigaban akan sauran jahohin, sai dai akwai manoma da ƴan kasuwa sosai agarin wanda ya farfaɗo da garin, sanan mafiya yawansu ƴan uwane ataƙaice zamu kira garin da Ahali guda wanda jininsu ke zagaye.

Malam Auwalu ya kasance ɗaya daga cikin manoman garin, wanda yake da gonaki masu yawan gaske, ana masa noman ababan masurufi sanan yana daya daga cikin manyan dattijan garin wanda suke tsayawa ma kowa wajan taimaka ma masu buƙatar hakan, da Aljihun su da kuma ƙarfinsu.
Yana da sauƙin kai mutuqa, hakan yasa ƴan garin kee girmamashi, wanda ko sarkin garin ya maidashi na hannun damansa, ba'a taɓa yin wata magana mai muhimmanci ba tare da shi ba.

Duk da wanan tsayuwar tasa akan mutane wajan dai-daiton lammuransu hakan yayi ƙaranci agidansa.
Matarsa ɗaya Zainabu Wanda akafi kira da Abu, zamansu cike yake da zaman lafiya da kwanciyar hankali sai dai sun samu wabi sosai kafin su haihu.
Yaransu biyu mata Asma'u da BInto Wanda sun shafe shekaru goma kafin Allah y sake azurta su da haihuwar  Ma'@ruf sosai suka shiga murna, wanda har sun fidda rai da samun haihuwa.
  Ma'aruf ya taso d gata sosai aɓangaran iyayansa da yayyansa, ko kaɗan ba'a barinsa yin aiki ko aike innah Abu bata fiya yi masaba.
Haka mahaifinsa ma duk lokacin da yaga yana wani aiki tuni zai hana shi acewar sa ya jira akwai lokaci yanzu yayi ƙanƙanta.
Yayunsa ma'u da binto suna sonsa kasancewar sa ƙaninsu ko dukansa akayi awasa sai sun rama masa. Wanan shine mafarin labarin sa.

.*******
Ma'aruf kazo ka ɗauko min niƙan garina kaga almuru ta gabato ga aiyuka sun cakude min. Idan nace zanje da kaina aikin zai ƙara dagule min."

Ma'aruf wanda yake tsugunne yana faman zane da kara kusan karatun da ake musu amakarantar boko yake ƙoƙarin zanawa, shuru yayi kamar baya jinta.

"Ma'aruuu da kaifa nake kamin shuru kamar baka jina."

"Innah ban iya ɗaukowa wuyana zai karye."

Zaro ido Innah Abu tayi cike da mamaki "Wuyan ka zai karye fa kace? Har ina garin ma yake da zai karya maka wuya? Zaka tashi ne kokuwa sai na zo na sassaɓa maka?"

Suna cikin haka babansa yashigo yaji suna wannan takaddamar "Kinga ki kyaleshi tunda yakawo uzurin sa, bani niƙan ni na kai miki."

Kallonsa tayi tana girgisa kai tace "Bari kawai zankai da kaina."

"Yauwa yafi akan kibashi yaje ya zubar ahanya."

Irin haka dasuke masa yasa gaba daya ya lalace baya aikin komai banda zuwa makaranta sedai yaci ya kwanta, yayyensa suna bakin cikin wannan lamarin se dai babu yadda zasuyi idan sunyi magana se anuna musu shine auta Dole sukayi hakuri suka zubawa sarautar Allah Ido, duk da suma wani lokacin suna hanashi aikin mai wahala, amma bai kai na iyayen sa ba.

Cikin wannan yanayin ya girma zuciyarsa a raunane, komi cewa yake bazai iyaba ko kuma ƙarfin sa bai iya kaiwa, babu labarin zai kama wata Sana'a tunda karatun nasa ba zurfi yayi ba iyakar sa makarantar gaba da faramare, ko gona baya raka babansa koda ya bisa kuma sai dai yayi zaune cikin inuwa yana kallonsa yana aiki, gashi Allah ya zuba mai rashin son magana, ko acikin abokanan sa sai dai yayi zaune yana kallon su sunata zuba hira da shaƙiyyanci irin na abokanai, shidai aikinsa murmushi sai kallonsu.

🥀🥀🥀🥀

Muna Baku hqr akan rashin jinmu da kukayi tsawon lkc hakan ya faru sakamakon sa6anin dake ta riskarmu.
Mun gode ss masu jira da masu tmby..

Daga alqalamin '''SophieG nd UmNass'''
In sha Allah yanxu xakuna jinmu ko wani lkc...Ku karayin hakuri naga page din bayawa

SARTSEHikayelerin yaşadığı yer. Şimdi keşfedin