1 - 10

5.1K 140 1
                                    

[02/11 8:35 PM] Aishat muh'd: [02/11 7:30 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿  TAWA CE!!!   💞

                💞         🌿🌿🌿

1⃣

Wata yar yarinya nagani karkashin mota ga dukkan alamun gyaran motan takeyi,, sai wani dattijo wanda akalla  zaiyi shekera 59 yana tsaye yana mika mata sufanu.

Dattijon ne yace yar baba " kifa daure notin da kyau", tana karkashin motan tace to baba na. Fitowa tayi daga karkashin motan saida na tsorata danaga kyau yarinyar dukda da bakin mai a fuskan nata tana sanye cikin biri da wando sai wata bakar riga a ciki da alamu kayan aikin tane saboda duk bakin mai ajiki.

Murmushi tayima baban nata tace babana, nadaure notin amma exhaus din sai an sake sabo,saboda yana fitar da hayaki dayawa. yay murmushi yace yar baba kenan, yanzu harkin kware, oya muje ki dauraye jikinki kisa kaya kitafi islamiyya, inkika dawo sai mukoma gida ko??to tace, baban nata yakama hanunta suka shiga cikin wani dan shago na langa langa haka.

Biri da wando wanda muyan ph ke kiranshi da "dongare" dake jikinta nayin kanikancin tacire, ta dauko yar kodaddiyar atampanta riga da zani tasa ta daura hijab abunta tace babana na shirya, Kallonta yayi yace to Allah kiyaye, baruwanki da kawaye, banda magana da  kowa ahanya kinajina ko??tace eh yace to wuce kitafi...

Tsayawa tayi ta turo baki, baban nata yace wuce kitafi mana, kuka tafarayi baba baka bani kudin break bafa, yace yar baba bakijin magana, kinsanfa kudin waec dinki nake tarawa  saikin cinye kudin, kuka takara saki wlh baba saika bani ni bazan yardaba,tadinga bubbuga kafa a kasa, girgiza kai yayi ya dauko wata kodaddiyar naira goma yabata oya wuce kitafi ayi karatu dakyau.

Nagode babana tafada tana share hawayen idonta tazira takalmin ta dan madina tatafi.

Mikewa baban nata yayi yace Allah dai yasa mai motar nan yazo yabada kudin gyaran motanan, koma samu nacin abincin dare yau, ya girgiza kai yakoma wurin motan yaciga da aiki.

Maman shakur 😘

[02/11 7:30 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿  TAWA CE!!!     💞

                   💞         🌿🌿🌿

2⃣

Wuraren karfe shida ta taso daga islamiyyan, direct shagon kanikancinsu tataho, tasamu baban nata yana hahhada kaya, da gudu takarasa ta rungume baban oyoyo babana, dariya yayi yar baba andawo tace eh baba na, me aka koyo?? Tace yau mungama suratu tauba, munyi hadith, da fiqhu.

Baba yace masha Allah, yace to kicigaba da karatu ki dage in sha Allah wataran zaki zama wani Abu a duniyan nan ki taimaki musulmai kinji ko, ki kasance mai yawan taimako, inhar kikaga mutane na bukatan abu inzaki iya taimaka musu ki taimaka musu. mekika siya da naira goman, taciro yar ragowan  aya jikakka a leda tace babana aya nasiya narago maka ma.

Dariya yayi yace kai yar baba da wauta ni tsoho dani yaushe zan iya tauna aya cinye kayanki na gode, yanzu tayani mu kwashe kayanan mu maida cikin shago mu kulle mutafi gidako? Tace to babana.

Wani injin mota taje zata daga baban da sauri yazo ya karba haba yar baba kidena daukan abu mai nauyi ke mace ne kinji ko?? Tace yakuri baba nadena.haka suka shigar da komi ya kulle shagon yakamo hanunta suka tafi gida.

Irin katon gidan hayan nan ne dakuna kusan 15 bayi daya kacal a gidan. Dakinsu shine daki na karshe, bude dakin yayi suka shiga yace yace yar baba kiyi alwala kiyi salla bari naje masallaci, karfa kifita kinsan yan gidanan dukanki suke ko?? Tace to babana bazan fitaba, ta make murya tace babana kadan siyomin alawa kaji, banza yay mata yawuce yafita.

Kaman yanda yace alwala tayi tai salla ta dauko littafan bokonta taduba, bai dawoba sai bayan isha yashigo musu da ruwan bunu da beredi, kadan yasha yabata sauran dukdan ba koshi yayiba, tasha tai nak, tace babana zanyi wanka, yace muje narakaki.

TAWA CEWhere stories live. Discover now