[12/11 12:24 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
6⃣0⃣
kowa afalon jikinshi yay sanyi harda dad, zaifi kowa murna in thariq ya auri shukra, amma a zuciyanshi yanaji cewa inhar shukra Nazir takeso shizai bata ba thariq ba.
Shukra ko jitayi kaman a mafarki wai yayanta na sonta anya kuwa yaya ne yafadi haka?? Kodai aljanu sun shiga jikinshine??daga baya kuma tafashe da kuka sosai ta durkushe a wurin.
Dad yace shukra Nazir kikeso ko?? Ta girgiza kai, yace karki damu shizaki aura, zanje nai bincike kan Nazir inhar yaro nagari ne shizan baki, mum ta taso tace shukra karkisa maganan thariq a ranki farinciki zamu baki kinji, inhar Nazir kikeso shizaki aura oya jeki kwanta.
Tana juyowa taga umma na hararanta, da sauri tai hanyar daki ta kwanta amma takasa baccin da'akace tayi, kawai tunanin maganan yaya thariq take.Washe gari har Suka tafi zamfara bataga thariq ba, duksai taji ba dadi, suna kaiwa zamfara gidan ummanta suka tafi yayinda hj amina tatafi nata gidan.
Alh tafawa yasa aka gyaramata daki komi pink dakin yay kyau sosai, yasaima shukra sabon waya sai murna take tai godiya.
Thariq bangarenshi ko dad yazo yasameshi adaki, yace son kai kuskuren kin fadama shukra son dakake mata, gashi har tafara soyayya dawani, nasan kai danane,amma in shukra ta nuna bata sonka bazan iya batakai ba, thariq yace dad inda ace Nazir mutum nagarine zan hakura nabata farin ciki, amma Nazir baida addini, yanashan taba, yana neman mata fa, baida girmama mace, he is nothing but a womanizer, baidau mace abakin komiba.
dad yace ban address din gidansu zan binciko dakaina thariq yabashi, yatashi ya shirya yatafi zaria.Tunda yakoma zaria tunanin shukra yasashi agaba,.
Dad yaje har gidansu Nazir, akaimishi iso a falon baki, yana shiga yaga tangamemen hoton Nazir sarai dad yatuna dashi wanan wanda yamai rashin kunya, chief din gidan yakawoma dad drink, dad yanuna mai hoto wanene wanan?? Cheif din yace dan mai gidana ne sunanshi Nazir ai dad baima tsaya jiran baban Nazir ba yamike yabar gidan.
Maman shakur 😘
[12/11 7:21 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
6⃣2⃣
Washegari Wuraren 10 nasafe dad da mum suka iso zamfara amma a gidan Hj amina suka sauka.
Umma, shukra da twins suka shirya dan zuwa gidan kaka, suna shiga gidan da gudu shukra taje ta rungume dad tana murna tasakeshi ta rungume mum, sanan ta rungume kaka, saida akaci akasha akai wasa sanan dad yay gyaran murya.
Yace shukra dama kece dalilin zuwan mu zamfara... Shukra ta tari numfashin shi tace dad dama inason kazo nafadama na hakura da Nazir yaya thariq nakeso yanzu shizan aura.
Kowa adakin yaji yay mamaki, sunji dadi harda dad dan dama abunda zai fadamata shine bazai iya aura mata Nazir ba, dan baida tarbiyya.
Kaka tace yaya me muke jira tunda ta amince asa rana yanzu mana ko. atake akasa rana wata daya. Shukra dai murmushin yake kawai takeyi dan batajin son Nazir zai iya barin rantaba, nazir yadawo jinin zuciyarta bazai taba karewaba. umma ce kadai talura da yanayinta saisa tajata sukabar dakin sukaje garden anan tafashe da kuka tafada jikin mamanta.
Umma ta shafa bayanta tace yar baba wot u did was d right thing, thariq shiyafi chanchantan malakan ki, bawani chan wanda baisan wahalan kiba, ta share mata hawaye karki damu bazaki taba nadaman auran thariq ba, ta rungume maman tana kuka sosai, ta cigaba da shafa kanta tace nasan Nazir kikeso amma lokacin shizai nuna miki ko da gaske Nazir kikeso.Atake awajen dad yakira thariq, hello son kanajina gobe kazo zaria inada magana dakai yace to dad.
Saida yamma su dad sukabar zamfara, shukra tai kokarin boye damuwar datake ciki dan umma tace karta bari su dad sukagane ( wayaga su shukra anfara wayau.).Washegari karfe 12 a kano taima thariq side dinshi yafara zuwa yay wanka sanan yasa 3quarter da singlet fara fat sai kamshi yake direct dikin dad yawuce, yasamu mum a dakin.
Dad yay murmushi yace Hj bashi good news din, mum tai dariya tace Thariq jiya shukra tace ta amince zata aureka atake wajen muka sa rana 1 month, thariq zuwa yayi yarike cinyar mum yace mum are u sure??da gaske?? Ita da bakinta?? Mum tace jibimin yaron zamani natabama wasa ne, wani dadi yaji da sanyi ya ratsashi yay sujjada sanan yadago ya rungume mum sosai yadogo kanshi yay mata kiss i luv u mum. dad yace kai denama matana kiss, sosa kai yayi yabar dakin yana dariya. Dad yay mamaki dama haka thariq keson shukra, lallai son yay DAKON SO littafin Kawalli kausar.Washegari da sassafe yadau hanyar zamfara gidan hj amina ya sauka sai bayan sallan la'asar yaci gayu cikin wasu fararen yadi dikin half jumper sai uban kamshi yake driver hj tasa yajashi sai gidansu maman shukra.
Maman shakur 😘
[12/11 8:03 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
6⃣1⃣
Yau kimanin satinsu biyu a zamfara umma batacema shukra komiba saboda tanason tasake da ita sosai.Yau fariday Wuraren goma nasafe umma ta aika yar aiki ta kira shukra. Da sallamanta tashiga dakin tace umma gani, umma tace shukra inason ki natsu magana zamuyi gabanta yafadi tace to.
Maisa bakison thariq?? Maisa bazaki yarda ki aureshiba?? Shukra thariq dan uwanki y shukra?? Shukra ta share hawayen daya zubo mata tace umma wlh nibance banison yaya thariq ba, kawaidai inason Nazir ne. Umma azuciyarta tace shukra Allah nunamin randa zaki chanza kifara magana kaman adult.
Umma tace shukra karki manta thariq shine cinki, shanki, yabaki sutura, yasaki amakaranta, ya baki magani dabaki da lafiya, ya kasance uba agareki lokacin dakika rasa naki, nakasance uwa agareki, ya kasance jagorar rayuwarki shukra is dat hw u will pay him 4 all wot he did to u?? Haba shukra karki zama butulu, inda badan thariq ba daharyau bamu haduba, daharyau bakisanniba, thariq yafita yanemo miki mahaifiyarki. shukra duk abubuwan nan dayamiki baitaba tambayanki abu ba,
Amma rana daya yanemi abu a wurinki saikiki mai?? Tai maganan tana kallon shukra dake kuka sosai.
Tace umma wlh natuba, nayarda zan aureshi plz umma bazan sakeba, banason Nazir.Umma tace abinda nakeso dake gobe su dad zasuzo kice mishi kin yarda zaki auri thariq kinji ko?? Tace to ummana. Saikuma ta kwanta jikin umma tana kuka.
Umma ta shafa kanta tace shukra nasan Nazir kikeso amma ki auri thariq lokaci shizai fadamana ko kinason Nazir. yar baba am sure duk inda babanki yake inhar yaji kin amince zaki auri thariq he will be proud of u. Shukra takara rungume umma tace i luv u soo much my umma, inason babana yay alfahari dani, inhar auren thariq zaisa haka wlh mama na yarda banason Nazir kuma.Maman shakur 😘
[12/11 8:09 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
6⃣3⃣
Shukra tana tsakar gida suna buga ball itada twins, tana sanye cikin wani 3quarter jeans baki, da blue top kanta ba dankwali jiya umma tai mata kalaba harda bid pink taca umma tasa mata, umma tace shukra waike yarinyace, ta shagwabe wlh umma inaso nidai kisamin haka ko aksamata kuma sun mata kyau sosai. sai ball sukeyi su twins sun fita iyawa sun cika gidan dahaya niya.Suna shiga gidan driver yakoma. shikuma thariq ya karaso cikin gidan, inda yaji ana hayaniya yabi yana zuwa wazai gani shukra ce ke buga ball da twins tunda yake da shukra baitaba ganinta da irin shiganba tsayawa yayi yana Kallonta.
Shukra tasamu tabuga ball din yashiga cikin raga ihu tafarayi tana tsalle tsalle yess i won yeee harda yima twins gwalo, juyowan dazatayine idanunta suka sarke dana yaya thariq jikinta ne yafara rawa ko ina....Yana karasowa kusa da ita ta juya aguje tashiga cikin gida kan gadonta tafada tana kuka sosai, Nazir wlh inasonka, maiya sami wayarka? i want to talk to you, banason kace na yaudareka, inaso nafadama aure zanyi.tacigaba da kuka tana dukan gado.
Twins ne sukazo wurinshi da gudu suna oyoyo uncle thariq sukaja hanunshi har falo, da gudu suka kira umma tafito, thariq yace anty ina wuni yana wani dukar dakai, tai dariya tace doc barka da zuwa saida suka gaisa sosai sanan sanan takaishi dakin baki.Dakin shukra ta shiga tace oya tashi kishirya, ta dago jajayen idonta tace ummu wlh banason... Umma tace shiii, mike muje umma ce tashiryata da kanta pink doguwan riga na material mai taushi,tai kyau sosai. Sanan tahada mata abinci a tray takai mishi.
Da sallamanta tashiga dakin kallo daya tai mishi ta dukar da kanta saboda wani irin kwarjini daya mata, a table din gabanshi ta ajiye tray murya alamun ta kuka tace gashi, sanan ta juya dan tatafi karaf taji yarike mata hannu......
Maman shakur 😘