64 - 65

1.2K 50 0
                                    

[13/11 5:56 AM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!!   💞
                💞          🌿🌿🌿
6⃣4⃣
Yajuyo da ita taki hada ido dashi amma hawaye kawai ke fita daga idonta, murya kasa kasa yace shukra mesa kike kuka?? Bakisona ko?? Tai shiru, mum ne tace kicema dad kin yarda da aurena?? Nan mai ta shiru, sai dai kuka ya dago kanta yace look at me shukra kifadanmin gaskiya kinsan banison karya.

Yace Nazir kikeso?? Tadaga mai kai alamun eh, cikin muryan kuka tace yaya dan Allah karka cema umma nace Nazir nakeso, yace umma ne tace kifadama dad kinasona?? Tace a'a, tadaice inhar na yarda na aureka babana zaiyi alfahari dani, ni inaso babana yay alfahari dani. Ta matukar bashi tausayi harga Allah yanajin cewa inda ace Nazir mutum nagari ne zai hakura yabarshi ya aureta.

Zaunar da ita yayi kusa dashi yace to kukan ya isa haka share hawayen, ta share yace duk randa kikaga dad kice mishi baki sona saboda afasa auren kinji, kaita girgiza mai. Yay shiru kanshi ma ya kwance zuciyarshi na zafi, kanshi na wani irin mugun ciwo  haka suka zauna a wurin bai kara cemata kala ba.
Lokacin magrib ne yabar dakin yaje yama umma sallama yatafi.

Ranan kwata kwata thariq yakasa bacci, maisa shukra bazata soshi ba?? Nazir ya cuceshi, yacusama shukra sonshi, yaji kanshi na ciwo yasha maganin dakyar bacci yay awaon gaba dashi.
Washegari da sassafe yabar zamfara direct zaria yawuce.
A ranan umma da kanta tadau shukra takaita chan gidan wata kawarta buzuwa, dan afara gyaran jikin shukra sai ana jibi biki zata dawo. Akano za ayibiki, shukra nata kuka wai bataso da kyar ta hakura ta zauna, masu gyaran jiki aka fara tsuma shukra.

Thariq koda ya isa zaria gidan amininshi isma'il ya sauka yafadanma isma'il komi, isma'il yace friend to me, kaine zaka koyawa shukra sonka, kaizaka koyamata yanda zata manta da Nazir aranta. Just think about it, kafa waye amma ace shukra nabaka headache, thariq yace kasan ni bantaba soyayya ba, wlh basan tayaya zan bullo ma al'amarinba. Isma'il yace cool ir mind yanzu kabari in ankawota gidanka saikafara janta ajiki kana nunamata soyayyar ka.

Maman shakur 😘
[13/11 6:16 AM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!!   💞
                💞           🌿🌿🌿
6⃣5⃣
Kwanaki sun jaa, shukra tayi wani irin kyau takara haske, taji gyaran jiki.
Tuni su umma suka tafi kano dan achan za'ayi biki. Yaune kawar umma zata kawo shukra daga zamfara zuwa kano.
Lokacin da shukra ta iso kowa mamakin kyau datakara yake, amma kana ganin ta kasan tana cikin tashin hankali tai zuru zuru, kwata kwata bata hadu da thariq ba, saidai Amina daya kawo mata tatayata zaman biki dan yasan batada kawa.

Tana ganin Amina taja hanunta suka shiga daki tafashe da kuka tafada jikin Amina. Amina tashafa bayanta shukra kukan nan ya isa, gobe ware haka kin dawo mallakin yaya thariq in sha Allah............................

Ayaune dubbanin mutane, bataliyan likitoci, yan uwa da abokan arziki suka shaida daurin auren THARIQ da SHUKRA akan sadaki dubu 100. Shukra tanajin an daura aure takara haukacewa dauko wayanta tayi takara kiran wayan Nazir amma a kashe saita fara typing text kaman haka
" slm masoyina Nazir, bansan maiya sami wayarkaba bata shiga, dan Allah duk randa kadawo kanemeni ta wanan layin, akwai magana mai matukar amfani dazan fadama.Allah dawomin dakai lpy. Shukra ".
Tana tura text din tafashe da kuka sosai.
Wuraren karfe 4 Amina ta shirya amarya dan zuwa walima tana sanye cikin doguwan riga baki yay mata kyau a garden din gidan akai walimar...

Nazir yana zaune adakinshi akasar Paris kira ya shigo wayanshi yadauka babban abokinshi ne, yace Nazir wai bazaka dawoba ga news yacika ko ina yarinyar dakakeso an daura mata aure da wanan doc din yayanta, mikewa yayi yace wot?? Abokin yace u heard me ya katse wayan.

Nazir glass cup din dake hanunshi yabuga aksa yafashe, idanunshi sukaja, yace now mothan ever i have to continue  with my plan, shukra wlh wlh saikinyi dana sanin sanina a rayuwanki, sainasa yayanki ya tsaneki sama da mutuwarshi dan inhar baki zama TAWA ba to bazaki zama takowa ba...

Zan samiki tabon da duk randa yayan naki ya kalli tabon saiya karajin tsanarki a zuciyanshi...

Maman shakur 😘

TAWA CEWhere stories live. Discover now