16 - 20

1.5K 66 4
                                    

[04/11 9:14 PM] Aishat muh'd: [04/11 9:09 PM] Aishat muh'd: TAWA CE!!!   

1⃣6⃣
Nazir mekewa yayi daga tsugunen dayake ya kalli dad, yace wot are u saying men?? As old as u are men?? Yarinyar dakamayi jika da itane zaka aura?? Dad ya gyara malunmalun din jikinshi yace u heard me, shukra TAWA CE, she mine, babu abunda zaka iyayi ka chanza hakan, kabar kofar gidana kafin ranka yabaci.

Nazir da idonshi yay jaa tsabagen kishi, ya kalli dad yace tsoho bari kaji, Inhar money speaks, inhar money solves problems, inhar money buy happiness wlh write it down, mark my words sai na mallaki shukra, shukra TAWA CE, shukra tafi karfin tsoho, shukra tafi karfin kowa a duniyan nan balle ma kai dazaka kai shekara 70 ko fi ma, dad ya kalleshi yace muzuba nidakai,  ya kwall ma mai gadi kira budemin gate, yakoma motanshi ya kunna saura kadan ya bige Nazir, Allah yasa yay saurin matsawa  ya shiga cikin gida yay parking.

Nazir komawa motanshi yayi ya dafe kanshi dan sarawa yake, ya tabbatar inhar baiga shukra yauba hala sai ciwo yakamashi dan jiya kasa bacci yayima, ciro taba yayi ya kunna yana zuka daga bisani kuma yaja motanshi yabar unguwar.

Dad na shiga gidan dakin hj yawuce yaga basu dawoba, yakirata awaya ta dauka, hj wai haryanzu ba'a gama gyaran bane?? Tace alh yanzunan aka gama, gamunan zuwa, yace to yakashe wayan, zama yayi yay shiru yana tunanin, maisa yakejin son shukra?? Yarinyar da jiya yafara ganinta, nifa ba yaro bane shekara 75 ina zankai yarinyar dako 17 batakaiba, jiyakeyi wani wutan sonta na ruruwa a ranshi, dukya kosa sudawo rabonshi da ganinta tun jiya da daddare.

Thariq ne ya shigo dakin da sallamanshi dad ya Amsa, yazo ya zauna kusa da dad ya daura kanshi a cinyan dad, dad yay murmushi yasa hannu yana shafa kanshi yace thariq baka girma ko, gaka da kani amma haryau saika dinga shagwaba, yace dad ai ni har yanzu nima autane, dad yace imran dinfa shida yake 4 years kaiko kakusa kai 31, yace son tashi muyi magana.

Maman shakur 😘
[04/11 9:10 PM] Aishat muh'd: TAWA CE!!!  

1⃣7⃣
Thariq ya tattaro hankalinshi yaba baban, yace son yaka mata ka ajiye iyalifa wai mesa bakason yin aurene?? Thariq ya sosa keya yace dad wlh inaso nazama kaman kai ne, nafison saina kai 40 years  zanyi aure.

Dad yaji kaji wauta ko, ni danakai 40 bakasan phd dana tsaya nayi bane. kai kariga kagama karatu kazama likita, is tym ka ajiye iyali nima naga jikoki na, ya shafa kanshi son will u do dat 4 u dad?? Yay murmushi yace dad tunda kanason hakan naji zanyi, amma kadan ban lokaci na gama program dinan danakeyi a ABU sheka na zaria, dad yace shikenan son Allah maka albarka.

Dad yace zancen karatun shukra fa?? Thariq yace dama inaso nasata a school kafin nakoma zaria, a ss3 ta tsaya bata cigaba ba saboda lack of money, yanzu inason nasata a makaranta da imran yake tunda sunada secondary sai sudinga zuwa tare, sanan nasata a islamiyya da kuma haddan asabar da lahadi, dad yace hakan nada kyau my son, am proud of you, Allah yabaka ikon cika alkawarin daka dauka na rainon shukra yace Ameen, daganan suka cigaba da fira.

Wuraren 1 suka shigo gidan, mum taimata shopping sosai ta siyo mata kayayyaki dadai sauransu, tunda suka shiga falo dad ke kallon shukra, itako tana hango thariq da sauri taje kusa dashi ta zauna akasa ta kama kafanshi ta rike gam, shidai thariq tunani yake anya shukra zata chanza kuwa?? ta shigo bata gaida kowaba, kuma tazo tawani rikemai kafa.

Mum ce tai magana tace sannu shukra wato ke thariq kadai kike yarda dashiba, mu dodanni ne, tunda muka fita takewani dar dar dani kaman na satota, amma daga ganin thariq har kinje kusa dashi kin zauna, alh ne yay magana haba hj kidena takurama yarinyar nan, yarinya ce ahankali zaki bita, bata saba damuba, lallabata zamuyi tayi harta sake, hj sake baki tayi tana kallon Alh.

Alh ya kalli shukra yace shukra baby, ahankali ta dago ta kalleshi, oya zokusa dani ki zauna kinji baby na...

Maman shakur 😘
[04/11 9:10 PM] Aishat muh'd: TAWA CE!!!  

TAWA CEWhere stories live. Discover now