45 - 46

1.2K 49 1
                                    

[09/11 9:57 AM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!!   💞
               💞          🌿🌿🌿
4⃣5⃣
Sai bayan sallan isha ya leko dakin tako mike tsaye tana dariya ciki ciki, ya daure fuska ke wakikema dariya ta turo baki to ai badakai nakeba dakaina nake, yace oya mutafi gidan isma'il din kiyi sallama da Amina gobe zata tafi, komawa falo tayi ta kwashe bras din tasa a leda da wasu kayan makeup suka tafi.

Databa Amina aiko ta dinga murna tana mata godiya sai wuraren goma suka bar gidan, thariq yakawo kudi mai yawa yabama Amina da kyar ta karba tai godiya.

Suna komawa gida shukra ta shiga dakinta sai bacci.
Washe gari da sassafe thariq ya shirya zai tafi asibiti shukra ta dinga kuka, yaya dan Allah kaje dani, tuntuni fa kai tafiya sai jiya kadawo plz go with me,  yace jekiyi wanka to, daki taje tai wanka tazauna tayi kwalliya sosai dan zama da amina yasa ta iya make up yanzu.

Daya daga cikin dogayen rigunan da hajara takawotama tasa, pink ne sai akimai kwalliya da black stones tadau gyalen tayafa gashinta takama amma still saida yazubo har tsakiyan bayanta tadau black flat shoe tasa sai kamshi take.

Fitowa tayi ya tsaya yakura mata ido, yaushe shukra ta iya gayu haka?? Murmushi yayi yace zama da amina mana. Kallonta yayi yace bakiga ana ganin gashinkiba ta tsaya agabanshi ta juyamai baya yaya dan tusamin gashin nakasa.

Hanunshi na rawa yakamo jelar gashin wani taushi yaji da santsi yay rolling sanan yatusa aiko ya shige sanan suka fito ya kulle gidan suka tafi.
Suna shiga sai kallonsu ake sunyi bala'in matching, wata doc mace shukra taga tanata hararanta, tace yaya wacece wanchan ya kalleta  yace ohhh wata doc ce sunanta JAMILA amma muna cemata JAMCY..

My dear jamcy mai kwankwaso sau🙊 lot of luv jamcy ina sonki.
Maman shakur 😘
[09/11 5:29 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!!    💞
               💞            🌿🌿🌿
4⃣6⃣
yakamo hanun shukra suka shiga office dinshi.
Telephone din office din ya dauka yakira secretary yace akawo mana min abinci plates biyu.
Suna zaune shukra sai tabe tabe take shikuma sai Kallonta yake, aka kawo abincin saida sukaci tai nak sanan yace ki zauna a nan karfa kije ko ina bari na shiga na duba patients tace saika dawo.

Yana fitowa jamcy tabiyo bayanshi ranta abace tace Thariq wacece yarinyar chan?? Wani kallo ya jefeta dashi batare daya bata amsaba, kagafa abunda na tsana dakai kenan wanan miskilancin naka. Ya kalleta ok jamcy ne
duk macen dakaika gani dani sai kinsan ko wacece? Tace haba thariq ka tausayamin ina sonka wlh, kishinka nake. Yace jamcy banasonki plz stay away 4rm me.
  **Jamcy doc ce tana bala'in son thariq shikuma bayasonta dan jamcy tama girmeshi she is 36 yanzu.**
Wucewa yayi yabarta a wurin, jamcy azuciye takoma, office dinshi ta wuce direct tana zuwa taga shukra gaban laptop dinshi tasa farin coat din thariq yanda kukasan doc, jamcy ta daka mata tsawa ke tashi dan ubanki, mezakisa coat din Doc Thariq??. Shukra ta mike wlh karki kara zaginmin babana yamutu.

Jamcy tace ance dan ubanki din, shukra ta kalleta sama da kasa sanan tace mai KWANKWASON SAURO kawai. wani super jamcy tayi tazo ta shake wuyan shukra....nikuwa nasa gudu nafito dan nakira thariq 🏃🏻🏃🏻

Maman shakur 😘

TAWA CEWhere stories live. Discover now