[03/11 2:13 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
1⃣1⃣
Shukra kuka tafara sosai, shikuma thariq ya girgiza kai ya cije lebe, sanan ya kunna motan dayake motoci sun fara moving.Kuka tayi sosai daganan kuma bacci yay gaba da ita, dama ance anacin bashin komi amma banda na bacci, hamdala yayi yanda tai baccin dan kukanta bala'in sosamai rai yake, parking yayi gefen hanya yafito yazagayo ta inda take ya bubbuga kujeran yana kiranta da "yar baba, yar baba" shi kwata kwata yama manta sunan kawai yazo bakinshi ne alokacin.
Bude ido tayi ahankali ta kalleshi kadan sai kuma tamaida idon tarufe yasake cewa shukra tashi mana ki koma baya zakifijin dadin baccin ki, kin cika nauyin bacci, da kyar ta iya bude baki tace ni babana ka kyaleni, wlh nagaji anjima zan tashi, zanma kuka fa karka kara tashina. saikuma tacigaba da gwalan gwalan din bacci ahankali har takoma bacci duka.
Girgiza kai yayi yarufe kofan yakoma yashiga motan yafara driving har ya shiga cikin kano acikin gaida gidansu yake, horn yayi gaban wani tamfatsetsen gida wanda idan kaga kyawun shi saika zata government house ne.
Mai gadi yazo yabude mai gate, yashiga ciki. NAZIR na ganin gidan da motansu yar kakkyawan yarinyan shi tashiga yay murmushi yace wlh koke wacece sai kin zama TAWA!! Nazir bai taba neman abu ya rasaba KE TAWA CE baby, yaja motanshi yay gaba, NAZIR matashi ne kakkyawa shikadai iyayenshi suka haifa saisa suka sangartashi dayawa, komai yakeso sai sun bashi, yagama karatunshi inda ya karanci ELECTRICAL ENGINEERING wanan kenan.
Maman shakur 😘
[03/11 2:35 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
1⃣2⃣
Yana gama parking yafito daga motar, mai gadi yazo yana kwasan gaisuwa suka gaisa yaciro kudi mai yawa yabashi yadinga godiya, wanan shine halin thariq dayasa kowa na sonshi akwai yawan kyauta ga tausayi.Bude kofan yayi yana dukan kujeran ahankali, shukra takara zumburo baki babana wlh asuba batayiba, da dai yaga bata da niyan tashi ya daka mata wani irin tsawa a firgice ta tashi jikinta narawa, ya kalleta yace biyoni mun iso gidanmu.
Yay gaba tsayawa tayi tana kallon gidan ita bata taba ganin gida mai kyau hakaba, haryakai bakin kofan shiga ya juyo yaga ita ko tahoha batayiba, ya tsaya ya kuramata ido fuskanshi a daure da sauri tataho da sallama suka shiga dakin dad da mum dinshi suna zaune suna kallon news.
Amsawa sukayi da murmushi a fuskansu, itadai shukra tana ganin mutane a dakin ta labe a bayanshi tana matsar hawaye, yagaida mum dinshi da dad shukra tai shiru yajuyo ya kalleta yanda talabe a bayanshi bazaki gaisuwaba, ahankali murya na rawa tace ina wuni, mum ce tana murmushi ta tashi tace haba bakuwarmu tsoranmu kikeji ne tazo zata kama hanunta,
Ihu shukra tayi ta kankame bayan thariq tare da chusa fuskanta abayanshi, mum ta tsaya turus, tace thariq bakuwar tamu tsoran mutane take ne?? Thariq ya cirota daga jikinshi ya dago kanta yanda take kuka yasa ya kwantar da murya shukra kidena kuka, iyayena ne babu abunda zasu miki kinji,
Share hawayen idonta tayi, tace babana yace kai kadai zan dinga yarda dakai, kumama ai ranan muna kwance a gadon nan na asibiti,kuma yace kanada kirki bazaka cutar daniba, yace kai kadai zan dinga yarda dakai ko bayan ranshi, ai baice dasuba, kumani babana yahanani magana da maza tana nuna dad dinshi, kuma.... Dayaga maganan nata bamai karewa bane yace to naji, ba baba yace kidingajin magana naba?? Tace eh, yace to ni yanzu kidinga yarda da iyayena babu abunda zasu miki kinji ko?
Maman shakur 😘
[03/11 3:01 PM] Aishat muh'd: 🌿🌿🌿 TAWA CE!!! 💞
💞 🌿🌿🌿
1⃣3⃣
Ta girgiza kai alamun to, yace oya je wajan mum dina, mum ta miko mata hannu ahankali taje tana tafiya tana waigen thariq ya gyada mata kai mum ta rungumeta, sannu kinji bakuwarmu babu abunda zamu miki dagayau ke yatace, ya sunanki?? murya na rawa tace shukra, mum tace wow sunanki mai dadi. Jeki gaida alh sai kije kiyi wanka kici abinci ko ai gobe zaki samu abokin fira harsaikin gaji.