*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
_Wani mutum kana masa alkhairi yana binka da sharri, kana k'ok'arin kyautata masa yana son munana maka, kana son dariyar sa yana son kukan ka, kada kaji damuwa a ranka ko ka gaza kowa irin aikinsa yakeyi kuma alkhairi danko_ .
*Duniya Makaranta* 👌🏻
*Page* 0⃣8⃣
________ "Alhaji nace ya ake ciki game da auren Mu'azzam?" Momy ta tambayi Abba lokacin da yake break fast, sanda ya kammala sannan ya maida hankalin sa gunta.
"Mu'azzam d'in ne yace miki ya tashi aure ko yaya?"
"Yanzu fisabilillah Alhaji yaro kamar Mu'azzam shekaru 30 da d'oriya ake tambayan ya tashi aure, ga sa'anninsa nan duk sunyi aure wasu har da 'ya'ya, haba dan Allah"
Murmushi yayi mai kyau "Zainabu Abu! Zan bincike sa naji daga bakin sa, zakiji yadda mukayi"
Tuni farinciki ya lullub'eta har da 'yar dariyar ta dan bata da burin da ya wuce ta ga Mu'azzam ya auri Samiha, dan ganin take shine kad'ai sakayyar da zatayi wa Umman ta akan k'aunar da take nuna mata(a naki ganin ba) "yawwa Alhaji kokai fa yanzu naji batu".......
" Ammi na kammala" Aymanah ce ta fito daga kitchen, tana gayama Ammin ta ta kammala aikin da ta saka ta, sanye take da Atampha Riga da siket sun zauna das a jikinta dan Aymanah badai diri da kirar jiki ba, komai cif-cif kamar wata babbar budurwa "to ki zubuwa Yayanku a plate ki kawo masa" ware ido tayi ta wani zazzaro su, dan ita sam bata ma san ya shigo ba, ido suka had'a harara ya watsa mata, tare da d'auke kansa daga kallon da yake mata, koma wa tayi jiki sanyaye ita dai a rayuwar ta Allah ya jarabce ta da bala'in tsoron Ya Mu'azzam, mugun kwarjini yake mata.
Dambun nama ne wanda yasha kayan had'i sai kamshi ke tashi, aje masa tayi akan table d'in da ke gefensa tare da d'akko masa ruwa da lemu a fridge tana gama aje masa ta shige d'aki ta bar shi suna firar su da Ammi ita har mamakin yadda yake fira take, su kuma yana musu fuskar shanu( Jan girma keko yan mata)..
"Bismillah Mu'azzam kaci dambu mana" kunyar Kada Ammi tace yak'i ci yasa shi cin spoon d'aya, dan shi a tunanin sa jagwalgwale ne kawai tayi, saidai me tuni labari yasha bambam....jin wani tasty and yummu da ya ratsa kunnuwan sa, ai basan yaushe ya kara lodo spoon ya auna ba, sai mamaki yake wai yaushe aka haifi yarinyar nan ne da har ta iya girki haka, amma ba mamaki Renon Ammi ce, dama can yafi kowa sanin dad'in girki shiyasa muddin yana gari to kwanonsa na d'akinta.
Mutumin fa sai lodi yake suna fira bai ankara ba sai plate, ganin haka yasa Ammi tace "Mu'azzam ko a karo maka ne?" Dan shafo kansa yayi "eh to Ammi inda shi a saka a dan flask ko Muneera sai ta kawo min" dan gaskiya yaji dad'in sa sosai, yana so ya samu ya k'ara loda wa da anjima, sallama yayi ma Ammi, ita kuma ta saka a flask taba Muneerar takai masa, dake da d'an yawa tayi, dama ita bata rabo da ire-iren ababen tab'awa.....
***************
"Mu'azzam ya maganar Aure har yanzu shiru banji kace komai ba, gashi Momyn ka ta fara k'orafi, ya ake ciki?"
Sosa keya yayi "eh Abba.....dama dai har yanzu ina dubawa ne, sannan kuma da naso sai na koma na dawo gaba d'aya sai...."
"Aa dama baka gama dasu bane, k'ara koma wa zakayi, ga kasar ka ta haihuwa na buk'atar da Mu'azzam"
"Eh Abba nima shiyasa nake so na koma nayi musu handing over na dawo kawai dan, zuwan da nayi kwanaki gurin wani abokina Barrister Haris naga cases barkatai most of them duk akan child abuse da kidnapping kuma abin takaici duk yafi ta'allak'a ga cutar talaka, shiyasa ma hankali na ya dawo gida, gaba d'aya, duk da nasan sai nayi da gaske kafin su amince da dawowa ta, amma dai I will do all my best naga na dawo gida gaba d'aya"
"Subhanallah! Ai talaka a Nigeria yana cikin matsala, Allah dai ya sawwaka mana wannan rayuwar, Ku kuma Allah yayi muku Albarka, ya taimaka muku akan niyyoyin Ku na alkhairi, ya shige mana gaba mu da ku baki d'aya"
"Ameen Abba"
"Kai Gwarzo wallahi kai shegen gari ne, jibi dan Allah yadda kake k'ara wani fresh dakai ko maganar Aure bakayi anya baka bin guntuwar hanya kuwa?" Wani aminin sa daya kawo masa ziyara ke masa tsiya, tsaye suke daga waje a bakin motar abokin nasa.
"Kai fa, Abdallah shedani ne Allah, me kake nufi da ina bin guntuwar hanya, banson iya shege fa" ya fad'a yana wani basarwa cikin salon sa na miskilanci.
"Sannunku, ina wuni" lafiya qlau 'yan kannen mu an dawo daga makaranta to sannunku" Abdallah ya Amsa wa su Aymanah gaisuwar da sukayi musu cikin sakin fuska, tare da bin su da kallo har suka shige ciki.
Mu'azzam kam k'ara had'e rai yayi tare da d'auke kansa, yana jin haushin yadda Abdallah ya wani sake musu fuska harda wani dariya salon su Rena su......."tabdi jam, harka! Gwarzo haka kuke da tsala-tsakan 'yan mata a gidan nan, gaskiya nikam na hango ta biyu"
"Mtsst! Kai fa gayen nan a jawu ne, wad'annan yaran ne 'yan mata? Salon ka jamin a rena ni? Kaga in ta biyu kake so kabi gari ko kaje site Inda mata suke ba wad'annan kwailayen ba, dan la karka sake min wannan wasan banaso"
Ganin yadda yake maganar da iya gaskiyar sa, yasa Abdallah binsa da kallon mamaki lallai sai abar Gwarzo, amma zai so yaga kalar matar da zai aure!!...............
_nima dai zanso naga zabin Mu'azzam🤔 kufa friends??_
Manage
*Siddiqa ce*
YOU ARE READING
Zuria Daya(rikicin cikin gida)
RomanceLabarin ZURI'A DAYA(RIKICIN CIKIN GIDA) labari mai dauke da makirci irin na cikin gida, sadaukarwa, soyayya, hassada, kiyayya, dama dai sauransu mai karatu kaidai biyoni kasha labari.