*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

640 37 0
                                    

*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

      By
_Maryam Abdul_


*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*




*An karb'o daga baban Mas'ud (A'D) yace Manzon Allah (S.A.W)  yace "kada Ku zagi sahabbai na domin koda d'ayanku zai bayar da zinare kwatankwacin girman dutsen uhudu bazai kai mudun d'ayan su ba" ya sake cewa "kai koda rabin mudun su"👌🏻*

_Sahabbai nada girman daraja, dasu aka yi gwargwar maya har muluncin ya tsayu har ya zo garemu muna yinsa cikin sauki, indan bamu yaba musu ba bai kamata mu zagesu ba_ maganar gaskiya👌🏻

Husnul Muslim.









          *Page* 2⃣3⃣




_______" Hmm ki bari kawai sisto ai na matuk'ar jin dad'in shawararki....." Katse maganar tayi jin an turo k'ofar tasan shi kad'ai ne zai shigo mata a wannan lokacin, mik'ewa tayi tare wayar hannunta tana wani iri kamar mara gaskiya, da kallon tuhuma ya bita tare da k'ara d'aure fuska, fisge wayar hannunta yayi "keda waye a waya?" Ya fad'a cikin tsawa.....

Ganin Nusee ce yasa ji jefa wayar kan kujera kawai tare da jan tsaki, shigo ta ya fara yi yana ja da baya ganin fuskan nan ba  rahama ita a nata tunani ya tsaya ya jiyo duka hirar da sukayi.

Sanda ta manne da bangon, ganin da gaske nufota yake yasa ta lumshe idonta tare da matsewa gefe d'aya,  hannayensa yasa a jikin bangon ya sunkuya dai-dai fuskarta har numfashin su yana had'uwa "Ke! Ni sa'ar wasan ki ne? Nace ni sa'anki ne?" Ya fad'a cikin tsawa ware ido tayi cike da tsoro da har yau tana tsoron tsawar sa, daga d'ayan yayi yana shirin sauke mata shi...

'Yar k'ara ta saki tare da fad'awa kan k'irjinsa ta cukuicukeye shi sosai tare da k'ank'amesa "pls yaya kayi hak'uri bazan k'ara ba plsssss!" Ta fad'a cike da shagwab'a mai tare da tsoro, wanda ya k'ara narkar da shi cikin yanayin da ta saka shi..

Rufe ido yayi na d'an lokaci tare da waresu a kanta har sun sauya launi "sake ni bazan dake ki ba" ya fad'a cikin wata irin murya wacce tafi kama data maye, k'ara shige masa tayi "Aa wlh wayau kake son yimin" ta k'ara fad'a cikin sangarta..

Dafe kansa yayi da duka hannayensa, tare da furta "ya ilahi" a hankali "wai kin sake ni ko sai na tura ki ne, na kuma jibgeki anan gun?" Ya k'ara fad'a cikin tsawa dan ya fahimci shine kawai last solution a gun shi....

Cika shi tayi tare da sulale wa a hankali saida taga ta gama yi masa nisa sannan ta tattare rigarta "Kaine sa'ata  d'in" ta fad'a cikin daga murya tare da shigewa bedroom da gudu, banko k'ofar tare da saka mata key..

A daddafe ya isa ga kujera tare da zubewa a gun kamar wasu kayan wanki, ga tufafin sa duk sun gama yin squeezing duk ta bata masa guga, lumshe ido yayi tare da yin baya da kansa ya jingina da saman kujeran, ya dad'e a gun haka na tsawon mintuna....

Samiha dake mak'ale jikin labulen  k'ofar dake ta glass ke duk tana hango abinda ya faru, tuni hawaye sun gama wanke mata fuska dan a tunaninta kissing d'inta ne yayi dan bata jiyo me suke cewa, da gudu ta ruga tana kuka ganin ya mik'e jiki a sanyaye ya nufo k'ofar...

D'aki ta fad'a kan bed tare da fara rero kuka "lallai Yaya Mu'azzam yakai mayaudari mara adalci, ta gama sadaukar masa da kanta jiya, bai wani yi appreciating ba yanzu ya koma can yana kissing yarinyar da ta tsana cike da caring, bayan ya gama soka mata magana" duk cikin ranta take saka maganar "Wlh I can't, I can't tolerate at any cost, ni zai nuna wa bata gabansa amma ya koma gefe yana munafurta ta?" Ta fad'a a fili tare da janyo phone d'inta ta danna no. Ummanta...

Samansa ya koma tare da sake kaya, sannan ya d'auki car key nasa tare da barin gidan gaba d'aya ya nufi Family house nasu...


**************

Dariya ta shiga yi kamar zararriya a d'aki "wlh ya Mu'azzam baka ga komai ba ma, saina tabbatar maka kwaila ma mace ke, saina nuna maka mace komai k'ank'antar ta, komai muninta indai tayi amfani da kasancewar ta mace zata juya namiji a hannu, muje zuwa" ta fad'a tare da sakin wani shu'umin murmushi..

"Umma wlh yana sonta, kedai kawai kiyi wani abu dan gaskiya akwai matsala" ta sake fad'a cikin kuka...

"Is OK baby, nasan me zanyi, kedai kiyi abinda na gaya miki"

"OK My Umma"

"Dat my baby, ki tashi ki k'ara gyara fuskarki, mutane zasu fara zuwa muku so ki iya takunku kinji baby" amsa mata tayi sannan suka yi sallama..

A Parlon Abba ya same shi tare da Dady da Hajja, suna magana, gaisawa sukayi tare da tambayansa iyalan da sabon yanayi amsa wa yayi da Alhmdllh lillah sannan ya shiga ciki..

Nan fa ya fara had'uwa da 'yan uwa da abokan wasa sai tsokanarsa suke da Ango ango yasha k'amshi, fuskarsa ba yabo ba fallasa yake wuce su ba tare da ya tanka su ba, dama sun san hali.....

A can bedroom ya samu Momy tare da wasu 'yan uwanta, suna magana, fita sukayi bayan sun gaisa suka bar shi da ita, zama yayi kan sofa ita kuma tana kan gado...

"Lfy, ya 'yata Samiha fatar tana lafia ba wata damuwa"

Baiji dad'in yadda Momy ta ware Aymanar ba saidai ba yadda ya iya "lfy" ya amsa a tak'aice.

"Yawwa dama kai nake jira, kana jina ba ruwanka da yarinyar nan, ka zuba mata ido karka yarda ka shiga harkarta, inta gaji da zama da kanta zata dawo gidannan, karka kuskura kaje kusa da ita bare ma wata alak'a ta had'a Ku banaso, ka jini ko?"

Sosai yake bin Momyn da kallon mamaki, har yau ya kasa gane meke damunta data tsani Ammi da iyalanta har haka shi ya rasa  dalili dan shi bai taba d'aukar aurenta da Abba yayi a matsayin dalili ba, dan baiga aibun hakan ba....

"Kuma wannan Umurni nike baka ba shawara ba, ka fahimce ni?"






_pls manage munyi rashin wuta ne, yanzun ma na matse ne kawai na muku wannan saboda k'aunar Ku gareni😊 ana tare👌🏻🤝🏼_


*Siddiqa ce*

Zuria Daya(rikicin cikin gida)Where stories live. Discover now