*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*2*
Gabanta ne ya fad'i tare da d'an tsorata ganin duk mutane tsaye cirko-cirko a farfajiyar gidan gashi duk attention d'in su ya dawo kanta, musamman su Momy dake jifar ta da mugun kallo kamar su zo su rufeta da duka, k'asa tayi da kanta tare da k'ara rungume littafanta ta kasa shigowa ta kasa komawa....
"Ummina! Ina kika tsaya ki ka k'i biyo 'yan uwanki gashi duk kin tashi hankalin mu" Abba ya katse mata shirun tare da bata kwarin gwiwar shigowa.
" Tadai tashi hankalinka, yo dama ai barewa ba tayi gudu ba, d'anta ya tsaya rarrafe, yarinya taje gantalin ta, data iya anzo an tayar mana da hankali sai kace ita kad'ai ce 'ya, mtsss aikin banza, ke Ku shige muje"
"Zainab a kullum ki ringa furta alkhairi akan kowa ki dena barin bakin kishi da son zuciya suna tasiri a kanki" Abba yace ma momy tare da juyawa gurin Aymanah "zo nan Ummina"
Tsaki kawai Momy taja tare da cewa "kwaji dashi" tare da juyawa zuwa ciki, itama Umma da bakin cikin rashin maganar da batayi ba ya isheta kasancewar Abba surukinta ne ba damar tayi bak'ar magana a gabansa tattara nata yaran tayi.
Cikin sanyi Aymanah, ta isa gaban Abba tare da russuna wa, kanta k'asa ta fara gaida shi, amsawa yayi tare da d'agota yana murmushi "Eh Abba dama wani text book d'ina ne da Ameerah ta ara jiya kuma shine zamu fara exam d'in sa, shine ta manta min dashi a gida, to shine da aka tashi na bita na karb'o"
"Ayya! Ummina Aida kin biyo 'yan uwan naki daba sai driver ya biya tanan ki karb'o ba tunda gidan su a bakin hanya yake, amma dai yanzu tunda kin riga kin karb'o shikenan adai kiyaye gaba"
"Inshaa Allah Abba, kayi hakuri bazan k'ara ba" sai yanzu take data sanin k'in biyosun koda yanka ta zasuyi ba zagi da gori kad'ai ba, da ace ta tayar wa Abbanta mai sonta hankali...
"Ba komai Ummina ki shiga ciki kawai nima masallaci zan wuce"
Su Momy ko a corridor shiga main house d'in suka had'u da Nusaiba dake bin bango dan jikin nata ba wani kwari "oh ni! Zainabu kaji yarinya da jaraba meya fito dake keda na bari a kwance" Momy ta fad'a tana kama baki.
"Momy Adil yace wai ba'aga Aymanah ba, shine na taso naji ko anji inda take" kara bud'e baki Momy tare da dunk'ule hannu ta watsa mata zagi "kaji shanyayya! Aymanah kanwar uwarki ko? Nace kanwar uwarki ko?"
Dariya umma tayi "Aifa sai kin tashi tsaye kan 'yarki dan inaga ba haka kawai aka barta ba" su kam su Samha tsabar takaici tuni sun shige ciki.
"Kai tsakani na da Fatima saidai Allah ya isa, duk da mijin da aka kwace bai isa ba sai kuma an biyo min har 'ya'yana" momy ta fad'a cikin k'unar rai, girgiza kai kawai Nusaiba tayi, dan ita ta rasa meke damun mahaifiyar tata da sauran 'yan gidan su, da suka d'ora karan tsana akan su Aymanah ita sam bata illar Ammi da 'ya'yanta ba, meye laifinsu dan sun kasance a cikin zuri'ar su, sun riga sun zama *Zuri'a d'aya* kuma dole su rayu tare har abada, addu'arta kullum shine Allah ya ganar dasu gaskiya.
"Ke! Wuce muje ba Inda zaki, ai gatacan ta dawo daga yawon gantalin nata"
"Momy dan Allah ki bari naje na ganta, itama fa ta damu dani"ba inda zaki wuce muje"
"Aa barta kada kuma Yaya yaji ya kara tayar mana da jijiyar wuya kinsan komai zai iya akan wannan 'yar gold d'in tashi" cewar Umma tana jan hannun Momy, kallon ta kawai Nusaiba tayi dan ita tasan ba Wanda yake kara rura wutar fitina a cikin gidannan sama da Umma shiyasa kullum tana nanike da Momy tana bata mugayen shawarwari wai ita nan sonta take, ita kuma momy da idanuwan ta suka rufe akan kishi sai hawa take duk inda ta d'ora ta.....
Kicibis sukayi a k'ofar corridon da Aymanah, da sauri Aymanah ta kamata tana mata sannu "Nusee meyasa kika fito kiga jikinki har yanzu duk zafi" ta fad'a tana tab'a wuyarta.
"Ni ki kyaleni ba ruwana dake tunda ace ina ciwo tunda kika shigo jiya baki kara zuwa kin dubani ba, amma da kece ai a d'akin nake tarewa nayi jiyyar ki" tace tare da d'an tsuke fuska...
"Yi hakuri Nusee kinsan bazan ki zuwa haka kawai, kawai dai.."
"Kawai dai me? Tsoron momy da aunty Samha ko? Amma ai gidan Ku ne, kina da damar ki shiga duk inda kike so naga, ni wallahi banason wannan tsoron naki" smiling tayi.
"Nusee ba tsoro nakeji ba tashin hankali banaso, banason kullum ace a gidan nan a kai na ake rigima ko fad'a" dafata Nusaiba tayi
"Na fahimceki 'yar uwata, nasa ni ba'a kyauta miki a gidan nan akan wani banzan dalili mara ma dogara, kiyi hakuri, ki kara hakuri wata rana sai labari, inshaa Allah da sannu zasu gane gaskiya"
Wannan karon murmushin nata har saida ya bayyana wushiryar ta da dimple d'in ta "wlh ba komai kada ki damu 'yar uwata ni bana rike kowa a raina kuma ni ko yaushe ina k'aunar su dan mun riga mun zama *Zuri'a d'aya* ,kinga is ok muje ki huta Idan na cire uniform nayi sallah zanzo ni nayi jinya"
"Chabb! Bazan saka rai ba dan nasan ba zuwan zakiyi ba" zanzo da gaske daga nan sai na Nuna maki revision d'in da akayi yau"
"Tau Allah yasa" daga haka sukayi ciki Aymanah na rungume da Nusaiban har sanda ta kaita K'ofar part d'in su sannan ta juya zuwa nasu....
*******
A parlour ta cimma Ammi rungume da Arif tana bashi abinci yayin da Muneer da Muneera ke cire uniform d'in su, sannu da gida tayi wa Ammi tare gaida ita, sannan ta ije books d'in kan centre table tare da cire hijab d'in, ta d'auki Arif da tun shigowar ta ya zame daga jikin Ammi ya dawo gunta yana mata gwarancin sa, ci gaba da feeding d'in nasa tayi.
Saida ya daina karba alaman ya k'oshi sannan ta sauke shi tare wanko hannunta a sink d'in da ke gurin dinning area sannan da tattare uniform d'in da su Muneera suka cire tana cewa su tashi suje su watsa ruwa suyi sallah, har ta mike ta nufi hanyar bedroom d'in su Ammi ta kirata.
"Aymanah"
"Na'am Ammi" tace tare da dawowa..."Ina kika tsaya dazu baki biyo bus d'in taku ba?"
"Am Ammi...Am dama..." Sam bata iya yiwa mahaifiyarta k'arya komai k'ank'antar ta, tama rasa me zata gaya mata..
"Koma dai meye kada ki kara irin hakan tunda kinsan dole hankalin Abban ku zai tashi, ki kiyaye banason abinda za'ace kece silar faruwar fitina, kedai ciki gaba da hakurin nan da kike yi, komai mai wucewa ne kinji" jinjina kai tayi tare da cewa "inshaa Allah Ammi zan kiyaye bazan k'ara ba"
"Kuma ma Ammi baki ji ba, haka Aunty samha tace..." Yimin shiru a gurin Muneera bana hanaki k'ananun maganganun nan ba?" Ammi ta kwab'e ta, tare da cewa su wuce zuwa sallah su suzo suyi lunch.....
Dan San batason yaranta su tashi da tsegumi da gulma, tasan dai komai mutum yayi kansa yai ma wa....
Bayan sun yi wankan tare da sallah, sun ci abinci ne, suna kallon peace TV, Aymanah tace "Ammi zanje na duba jikin Nusaiba"
Shiru ne ya ratsa kafin tace "tau Amma ki kiyaye sosai banason rigima...
Littafin ta d'auka tare da ficewa, saidai tana isa K'ofar part d'in nasu Nusee taji zuciyar ta ta tsinke, ta kasa shiga dan batasan kalar wulakancin da zata sha ba.......
*Siddiqa* ce👌🏻
[9/29,
YOU ARE READING
Zuria Daya(rikicin cikin gida)
RomansaLabarin ZURI'A DAYA(RIKICIN CIKIN GIDA) labari mai dauke da makirci irin na cikin gida, sadaukarwa, soyayya, hassada, kiyayya, dama dai sauransu mai karatu kaidai biyoni kasha labari.