*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢
🤦🏼♀🤦🏼♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼♀🤦🏼♀
By
_Maryam Abdul_*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*
*An karb'o daga Abdullahi Dan Abbas (R'A) yace Manzon Allah (S'A'W) yace "Mai kyauta ya karb'e ko mai kyauta ya amshe kamar kare ne yayi amai sannan ya koma ma Aman nasa ya lashe.*
Wa'iyazu billah Allah ya kiya shemu
_Husnul Muslim_
👌🏻😍 _My friends masu bibiyar wannan littafin ina jin dad'in yadda kuke nuna k'auna gareshi I really appreciate👌🏻pls masu bibiyata PC da sunan na turo daga farko ko kuma neman pages, pls Ku tausayamin nayi nisa ina matukar jin wahalar turawa ta PC, Ku tambaya a group inada tabbacin zaku samu, pls Ku kuma idan sun tambaya a group banda shariya ni kuma taimaka hope k'orafina ya karbu🤝🏼_
*Page* 2⃣5⃣
________kan seat ya jefata tare da nuna ta da yatsa, cikin kakkausar murya idanuwansa sun kad'e sunyi ja fuskar ba rahama kamar wani jaririn zaki " kisan irin kalaman da ke fitowa daga bakin ki, ni nafi k'arfin ki kirani hotiho kuma zan tabbatar miki nid'in ba shasha sakaran namiji bane, sai kinyi regrating kina hotiho da kika yi" yana kaiwa nan ya fice fuu daga parlon gaba d'aya, Samiha kanta sanda ta tsorata da yanayin sa, ita kanta ta tsorata dan bata tab'a ganin irin wannan yanayin a tare dashi ba....
Tab'e baki tayi tare da d'aga kafad'a bayan ta mik'e "oho dai, nidai na fad'i abin da ke raina, ba kuma wanda ya isa ya hanani fad'ar son raina a gidan nan ehe" tana kai aya ta wuce zuwa part d'in nata hankali kwance........
Driving yake ya furzar da iskar bakinsa dake yi masa da yake jin zafinta "lallai it higher time daya kamata na nuna wa yarinyar nan bata da wayo it time daya kamata na koya mata hankali" duk cikin ransa maganan, sai amon zancen nata ke masa yawo a kunnuwa " _indai akan wannan hotihon mijin naki ne, nina fi k'arfin ajinsa ni sai tsalalen saurayi dan Under 30_ " shine kawai ke masa yawo a kwakwalwa yana kallon hoton yadda take maganar cike da renin wayo "Never!" Ya fad'a da k'arfi tare da dukan sitarin......
"Momyn Samha wai haka zamu zuba ido ba zamuyi komai akai ba?" Umma ta ce da Momy, wani kallo ta bita dashi mai cike da ma'anoni "lallai Suwaiba nan bayan asarar kud'in da kika ja min nayi k'arshe abin ya juye a kaina, tunda kinga nayi miki shiru ban tanka miki ba shine har kike da kwarin guiwar k'ara tunkara da maganar na koma na k'ara bata wasu kud'in saboda bansan zafin su ba ko?"
"Aa ba haka bane, wancen ma akasi aka samu dan bamu abin zai juye a kan mu ba, Amma ina mai tabbatar miki wannan karon komai zai tafi dai-dai"
"Allah ko? To bari kiji ni nayi wa d'ana magana kuma nasan bazai tsallake magana ta ba, dan haka ba inda zanje kije ke kad'ai sannan kar a yadda a sako min d'ana ciki kiyi iya 'yarki da 'yar matsiyaciyar kin gane ko?"
Murmushin yaudara ta sakar mata "Allah ya huci zuciyar ki Momy, na fahimta zanyi yadda kika ce" daga haka ta fice daga d'akin, tana fad'a cikin ranta "inkin San wata ai baki san wata ba"...
**************
"Ranka ya jima mai gobe da nisa, aikinka yankan wukane saidai an samu akasi a aikin da akayi mana a baya..." Daga mata hannu yayi tare da fara magana cikin mummunan sautin nasa Mara dad'in sauraro "kaikayi ya juye kan mashekiya ko, ai nasan komai, auren ya koma kan d'an wacce kuka zo tare sannan ke kuma mijin 'yarki" ya fad'a mata kai tsaye....
YOU ARE READING
Zuria Daya(rikicin cikin gida)
RomanceLabarin ZURI'A DAYA(RIKICIN CIKIN GIDA) labari mai dauke da makirci irin na cikin gida, sadaukarwa, soyayya, hassada, kiyayya, dama dai sauransu mai karatu kaidai biyoni kasha labari.