*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

569 37 0
                                    

*_ZURI'A D'AYA_*🎆🏢🏢

🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀ _Rikicin cikin gida_ 🤦🏼‍♀🤦🏼‍♀

      By
_Maryam Abdul_


*In dedicated 2 Bilkisu Hashim(Mom Zee)*







*An karb'o daga Jabirin (R.A) yace manzon Allah (S.A.W) yace misalin sallolin Farilla guda biyar da mukeyi a yini, kamar misalin koraman ruwan tafki ce take gudana a bakin kofar kowannen mu, yake wanke jikinsa a kullum sau biyar a rana(yana nufin yadda mukejin dad'in jikin mu Idan mukayi yawaita wanka muna wanke daud'a to kamar Haka sallar ke wanke mana zunuban mu! Allah ya bamu ikon kiyaye ta👏🏻)*

Husnul muslim👌🏻










        *Page* 3⃣3⃣









_____kasa daurewa ya isa Malam Aminu kano yayi ganin yadda take bleeding sosai gashi har yanzu ba numfashi a tare da ita, ga hankalinsa da baya jikinsa driving yake kawai amma ba wata nutsuwa a tare dashi, wata private clinic na kan babban titin unguwar tasu ya shiga da ita, aiko a gaggauce aka kawo gadon d'aukar marasa lafiya aka d'auketa, Emergency aka shiga da ita ganin ta in critical condition, bin gadon yayi hannunsa cikin nata yana shafawa, shidai fatan bai wuce ta dawo hayyacinta ba duk a rid'e yake ya kasa yin tunanin komai...

Yanayin da yayi musu magana dashi da yadda ya figi motar ba girma, ba karamin kad'uwa ya sakasu ba, sun San yana da zafi sannan akwai tsare gira saidai wannan yanayin nasa na yau ya sha banban koma suce basu tab'a riskar sa a irin yanayin ba...

Sosai jikin Samha ya sanyaya lallai sun tabka ta'asar da basu san iya abinda zai biyo baya ba, tun anan ta fara data sanin biyo Samihar da tayi ba tare da ko mijin ta yasan ta fito ba "bleeding? Mean for?" Ba Momy ta gaya mata ta hana Yayanta shiga shirgin ba, kuma tasan yadda yake tsananin yi mata biyayya amma tabbas wannan jinin ba shakka na zubar ciki ne alamar yana kulata tunda ga sakama ko b'aro-b'aro....

Ciki ta koma a guje tare da d'auko kayanta ko mayafin a tafe take yafashi, rik'eta gam Samiha tayi tare da yi mata wani irin kallo wanda yafi kama Dana maraici, itama jikinta yayi sanyi lakwas dan batasan makomarta ba "kina nufin tafiya zakiyi ki barni anan?" Figze hannunta tayi tare da watsa mata harara "to da na zauna ya sameni kike nufi, au ke zama zakiyi kenan?"bata wani jira cewarta ba ta wuceta cikin sauri, itama ciki ta koma da gudu tare da tallabo veil d'inta cikin sauri ba zata yadda ta zauna ya dawo ya sameta ya nemi kasheta, gara yaje gida komai ta fanjama fanjam..

Saidai me suna zuwa bakin gate mai gadin yace bai san zancen ba dan yallab'ai yace kar ya bari kowa ta fita a cikinsu kuma kar a shigo, bala'i da hauka suka fara gwada masa dake dama ya kulle kuma mak'ullin na hannunsa yasa ya sharesu dan k'arshe ma ya shige d'akinsa ya rufo k'ofarsa ya barsu nan suna ruwan ashar d'in su, shidai umurnin oga kawai ya ke bi kodon ya wanke laifin da yayi masa, dan tabbas yaji hayaniya a ciki saidai sanin dokar sa tayi masa iyaka daga gate sai gate, yasa baije ba laifinsa kuma da bai kirasa kuma wannan Sam baizo kansa ba..

Daga karshe ganin tabbas da gaske ba barinsu fita zaiyi ba ya saka su dole komawa ciki hankali a tashe dan sun San tabbas yau kashin su ya gama bushewa saidai har cikin ran Samihar taji dad'in zubewar tsinannen cikin da sam basu San da zamansa ba, tabbas  wannan al'amarin yayi mata dad'i duk da ranta fal fargabar makomarta...

Samha kam safa da marwa ta shiga yi a parlon dan abubuwan sun had'e mata da yawa itafa ba ma da niyyan zama tazo ba dan 'yan kwanakin sun fara samun matsala da mijinta k'orafin ta cika yawo ga rashin girki ya gaji da yin take away, rashin iya tsabtace gida duk da kuwa tana da maid kuma tana yi amma dake Neman rigima yake yace sai ita zatayi da kanta yaushe zata iya, ga dokar fita daya kafa mata ba tare da izninsa ba, har ya tabbatar mata ta sake zai d'au tsattsauran mataki akanta, gashi tana so ta koma gida kada a dawo ya samu bata nan an hanata, dabarar kiran Momy ce ta fad'o mata...

Nan take ta shiga labarta mata duk abinda ya faru, a zabure Momy ta mik'e "What! Kika ce  ciki fa? Waima ubanwa yayi mata cikin dan badai my Son ba" Momy ta fad'a kausashe cikin tashin hankalin da ya dirar mata a yanzu a ba zata "ciki fa kuma yadda ya nuna damuwar sa da yadda ya fita hayyacin sa ya nuna ya damu da ita yana sonta, nidai ba wannan ba Momy yanzu ya za'ayi na fita da matsala fa"

"Karki damu yanzun nan zan turo mudi ya d'aukeki aini kin biyani dota, ki kwantar da hankalinki ba abinda zaiyi muku, shi kuma dan ubansa zai zo ya sameni, kice ma Samiha itama ta biyoki kuzo tare"

"Hum ni ai ba wani biyowa da zanyi ta nan gida zan wuce dan na gaya miki da Matsala" amsa mata tayi sannan ta katse wayar...

Safa da marwa kawai Momy keyi tama rasa bakin magana wato ita Mu'azzam zai ninke a baibai ita zai renawa hankali, da ba dan su Samha ba kenan da saidai ta wayi gari taga abinda tafi tsanar faruwar ya faru wato had'uwar jini tsakaninta da Fatima "bazai tab'a yuyuwa ba!" Tace a fili da k'arfi "wannan karon dole nayi abinda banyi ba a baya koda haka na nufin Barkewar rashin jituwa tsakanina da Alhaji, dole na raba wannan tsinannen aure dake shirin hargitsa ni, dole nayi magantu fiye da baya, tabbas Mu'azzam zai fuskanci matsancin fushina ni..ni yakeson had'awa jini da Fatima tabbas ya d'auko magana" haka tayi ta tambatun ta cikin tsananin b'acin rai...



************




"Sir!"

Da sauri ya juyo tare da kallon nurse d'in da rinannun idanuwansa da kallo d'aya zai tabbatar maka yana cikin matsananciyar damuwa, tunda aka shiga da ita ya kasa zama sai ka da komo yake yana kallon k'ofar ransa fal tausayin ta cike da damuwa Mara adadi...

"Yes! Yawwa ya ake ciki ta farfad'o?"

Ya tambaya a same  time, cikin tausayawa da sanyi irin na wasu ma'aikatan jinya Idan zasu gaya maka bad story about ur patient(bak'in labari game da majinya cinka) "sorry 2 say kun rasa babyn ta samu miscarriage, and tana buk'atar jini yanzu saboda jinin da ta rasa sosai" kasancewar end of week ne hospital d'in ba Dr sai nurses....

"Miscarriage" ya maimaita a fili dama Ashe ciki ne da ita da gaske kamar yadda yake hasashe, amma kuwa ya zama wawa daya kasa gane hakan tun farko, yayi sake wanda yaja masa rasa gudan jininsa, baisan lokacin da hawaye suka wanke masa fuska ba cike da juriya irin tashi yayi saurin goge hawayen tare da cewa nurse d'in suje a gwada nashi in zaiyi dan shi kowa ma bai samu gayawa ba asalima yabar wayoyin a mota, yafi so sai yaga ta farfad'o tukun kafin ya samu nutsuwar sanar da gida...

Cikin sa'a kuwa jininsu yazo d'aya aka d'iba nan take...

Duk yadda Mudi yaso gate man d'in ya bari ya shiga gidan fur ya murje ido ya ce baisan zancen ba tunda oga bai kirashi ba dama gashi k'abila sarkin kafiya da rik'o  gashi wani gabjeje kakk'arfan gaske, haka dole Mudi ya koma ya gayawa Momy an hanashi Shiga..

Wayar Mu'azzam taci gaba da kira cikin b'acin rai sosai gashi tana ring amma baya d'agawa aiko takai k'arshe a k'uluwa sai kwafa take...

Zuwa yanzu kuka Samha takeyi dan tasan ta gama kad'ewa har ganyenta musamman da taga kiran mijinta ya shigo mata, kasa d'agawa tayi sai fad'i take "na banu na gama ai" itama Samihar hankalinta Sam baya jikinta gashi ta kasa samun umman ta a waya...

Ganin wani kiran ya k'ara shigowa a wayar ne yasa ta had'iye yawu tare d'agawa hankali tashe "kina ina" taji saukar muryarsa a kunnenta a kausashe "um...um..inaa..." Katse ta yayi..

"Good duk ma inda kike daga nan ki wuce gidanku har na nemeki" bin wayar tayi da kallo kafin ta rushe da kuka tare da d'ora hannu akai "Wayyo Allah na, amma dai Samiha kin zaja min"......







Manage pls am busy










*Siddiqa ce*

Zuria Daya(rikicin cikin gida)Where stories live. Discover now