ZAMAN GIDANMU..

766 19 1
                                    

*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_

*Jamila Umar(Janafty)*

 

                

.....""Sai da Suka Shekara Daya Cur da Aure kana Wasila tace yakamata Suzo Bauchi Tunda kuma tace Shikenan mgana ta zauna,Zuwan da sukayi sai da kowa yayi Nadama mussaman Hajiya Don Zuciyarta ta kusa bugawa na ganin yadda Rayuwar Baffa Ta koma Bita zaizai,sai Abunda Wasila tace Shi yakeyi Wani karin Abunda takaichin ma ko gaida iyayen nasa ma Sai da Wasila tace ya gaida su kana Baffa ya Gaida Mallam da Hajiya.

Tunda ga Zuwan nan bai kara taka kafarshi Bauchi ba,Su kuma basu Daina addu"a ba,Al"amarin akwai ban Tsoro aciki koda Abun yaso ya lalace Da Zarar Wasila Taji lbrin Baffa yana kiran Bauchi abakinshi Zata kira Hajiya Kudirat su koma Wajen Boka su Zube kudi asake sabon aiki,shikenan kuma sai Abu yakara komawa baya,Wasila ta zama itace Uwarshi da ubanshi sai Abunda tace Shi Baffa keyi,Ta mallakeshi dashi da Dukiyarsa gabadaya daga ita sai Yan"uwanta ke fantamawa da arzikinshi iyayenshi ko ya ma manta dasu kwata kwata mganar ibada ko Wasila duk ta kara Susutar dashi dama itama ba gwana ba,Wani lokacin baya sallah akan Lokaci Addu"a ma Baya samun yi balle har yayi ma kanshi ko wani mtsalan Nashi ya ragu.

   Saboda Samun waje Har Kannenta Tace su dawo gidan da Zama su Jamila suna tsoma biyar suna Fito da goma,babu Abunda Sukeyi sai dai Su ci su kwanta Suyi chart ko suyi wanka Direba ya Fita dasu yawo,mganar gyaran gida da girki kuma Tun kafin Aurensa da Wasila yana da kuku Josepen,shine ke kula mai da gidan,ko yanzu kuma Da ya Auri Wasilan Babu Abunda ya Chanza Zani.

Tun Bayan Aurensu likitoci Suka tabbatarma da Wasila baza tataba haihuwa ba Har abada sakamakon Tun lokacin Datake kan ganiyar Watsewarta Tayi ta amfani da kwayoyin hana Daukan Ciki su sukayi Sanadiyar lalata mata mahaifa Yasa bazata iya Daukan ciki ba,Wasila bata wani damu ba,ta bar Abun Aranta tana ganin sai dai ita da Abdallah su Mutu basu ga Dan kansu ba,ammh Bazata taba bari Abdallah yaji wannan lbrin ba balle har ya kara aure Wata tazo ta Haihu dashi.

  Rayuwar Wasila ta chanza Fiye da Tunanin mai karatu,takara Fari da kiba da kyau Abdallah ya Siya mata Motar Kirar Vibe2019 sabuwal dal Ga Kudin daya ke Bata tana yarda taga Dama Babu Abunda ya Shafeta,Illah Soyayyar Abdallah Wanda takejin ko Uwar data Haifeshi bata Fita Son Shi ba shiyasa take bala"in kishinsa ko kallon Banza wata mace bata isa tayima Abdallah ba yanzu Wasila zata Fara hauka,shiyasa yake kiyayewa kirarin Da wasila take ma kanta itace kwara daya jallin tal matar  Abdallah da ita zai Rayu kuma da ita zai Mutu.

Abunda bata sani ba Bayan Auresu Da Wata goma Tafiya ta kama Abdallah Zuwa Lagos wajen Saminar daga wajen aikinsu ada yaso Ya taho da Wasila ammh sai taki,tace mai ya Tafi kawai ashe lokacin tana son taje Bida zasu koma wajen Boka,akan mganar iyayen Abdallah Tana so ayi musu Farraqu har abada atsakaninshi da wannan Shegen mijin Kanwar nashi Yusuf...

Wannan Zuwan Shine Sanadiyar Haduwarshi da *POLINA* Wacce ta kasance Ba musulma ba kuma Karuwa ce Sosai wacce tasan Duniya sosai,A Hotel din da Abdallah ya Sauka anan ya kyallah ido yaga polina kawai yaji ta burgeshi Don shi akwai Son mace Doguwa Fara mai jikin Mata,ammh Duk da haka bai mgana ba,Saboda ajinsa,sai itane data hangeshi sanda yake kallonta ta kariso gareshi tana mai kwakwarsa,Da farko tashi yayi ya bata waje,Ya nufi dakin daya sauka ganin haka yasa tatashi ta bishi,yadda taga ya bar mata dakin Abude yasa ta tabbatar da yana Ra"ayinta.

     Da farko tasha Wahalanshi don yayi mata jinkanshi ammh sai ta nunamai ita yar Duniya ce tayi amfani da barikinta ta hilace Suka kwana aikata masha"a,Abdallah yasha mamakin yadda yaji ya Fita daga hankalinshi akan polina Duk da Tun dayake bayan Wasila bai taba kusanta Wata mace ma,ammh yaji polina tasha bambam da Wasila nesa ba kusa,ta tafiyar dashi yadda ya kamata,ga Ta da Ni"ima Sosai sai gashi Wasa wasa Shakuwa ta Shiga tsakaninsu Suna tare har yayi kwana hudun da zaiyi yayi Shirin komawa nan Fa hankalin Polina yatashi Domin ita ta kamu da Son Abdallah gaye ga kyau ga kudi ga iya Sarrafa mace,dakyar ya lallasheta akan zai dawo ya bata kudi masu yawa bayan sun karbi Nombar wayar Juna...

ZAMAN GIDANMU..Where stories live. Discover now