*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_*Jamila Umar(Janafty)*
Sai around 8am ta baro asibitin dayake sai da Suka tsaya Sukayi Round din safe,Cike da Farinciki ma"u sukayi sallama da Sister Bahijjah,Banki ta fara biyawa ta cire kudi daganan kasuwa ta Wuce Ta siyanma Su Fati tsaraba,ko Bauchin bata kira ba so take ta basu Suprise,Tana Adaidaita zata koma gida ta kira Aisha awaya tana Fadamata Yanzu zata tafi Bauchi.
Bata Fuska Aisha tayi tana fadin Asma"u bata kyauta mata ba,Da bata fadamata Tunda Wuri ba,data Shirya Sun Tafi tare,Cike da Dariya Asma"u ke Fadin kibarma wa mijin naki da kuma my Son..? cike da Shagwaba Aisha tace Su zauna Su kadai mana Rabin Raina,Jin haka yasa Asma"u yin dariya sanin wacece Aisha,kafin suyi sallama sai da Aisha tayi ta jaddama Asma"u ta isar da gaisuwanta wajen Mama,da su Hajiya.
Koda ta Shiga gidansu bata iske kowa atsakar gidan ba,Dakin su Baba lami ta leka suka gaisa,Nan take sanar da ita yanzu zata tafi Bauchi baki Baba lami ta washe tana Fadin"Ehe yau ma"u sai kwananan dakin Mama ko.."Asma"u na dariya tace"Sosai ma Baba lami,bari naje na Shirya kada nayi dare ahanya ba,da dadewa zanyi ba Ranar Sunday zan dawo.."
Gyada kai Baba lami tayi tana Fadin"Gaskiya kam,hanzarta kada Rana tayi.."Kofar dakinta ta isa bayan tasa makulli ta bude,ta Shiga da sallama tana kwabe hijabin gidan dake jikinta,Tiolet dinta ta Fada bata ma tsaya neman Ruwan zafi ba ta tara Ruwa afomfon dake Bayin ta Cikashi da Ruwa kafin ta Tube tayi wanka agurguje ta Fito Fuskarta kadai in ka kallah zaka san Asma"u na cikin Farinciki.
Good 1hr Yabata ta kamallah Duka Shirye Shiryenta,Ta Zuba kayanta akaramar akwatinta Kala Uku,sai kayan barcinta da Dan Abunda zata bukata ita kuma ta Shirya Cikin wata Doguwar Rigar Atamfa wanda Ammi ta dinka musu sanda Aisha ta Haihuwa mai kalan orange da Brown,Mayafinta ta sanya brown babba,Fuskarta ba wani makeup dama ita ba ma"abociyar kwalliya bace.
Jakar hannu ta Dauka baka ta kuma sanya Wani Flat Shoe dinta baki,Sai da ta Kauda komai ta kashe Wutar dakin kana ta Jawo karamar Trolley dinta da hannun hagu,hannun damarta kuwa tana dauke da karamar Jakarta da kuma wayarta Ta Fito Fuskarta na bayyanar da Annuri.
Umma ce da Mama ke Tsarkan gidan,Umma ce ke kofar dakin Hajiya iya atsaye da alama suna mgana ita kuma Mama ta coge akofar dakinta Tana kallon Umma kamar dai wata mgana ce ta hadasu,cike da mamaki Suke bin Ma"u da kallo ganin ta Ijiye akwatin tana kulle Kofar dakinta da makulli,Galala suke kallonta musamman ma Umma,don ita mama Sau daya ta kalleta ta kauda kai,ita ko Umma kallon Kurillah tabi Asma"un dashi ganinta yau Cikin walwalwarta.
Basu samu zarafin mgana ba Asma"u tagama kulle dakinta ta waigo tana Riko akwatinta gefe daya tana gyara zaman mayafin kanta,Hakoranta duka Suna waje take Fadin"Umma,Mama zan tafi Bauchi...'
Mama ce tace!"Ayyah Allah ya kiyaye hanya.."Fuskarta bata Nuna Me Zuciyarta ke Ciki ba,Umma ko ido ta kwalalo tana fadn"Bauchi kuma..? Asma"u bata bi ta kanta ba tace"Eh,Anty amarya batanan ne.."?Bata samu amsa ba Hajiya iya Ta Fito daga dakinta tana Fadin"Waye nake jin ana zai Tafi Bauchi kuma...?Umma tace"Wai Asma"u gatanan ta Fito ma..."
Kallonta Hajiya iya tayi Shekeke kafin tace"Bauchi kuma.. ? Toh da izinin wa zaki Tafi...?"Abba da Shigowarshi kenan yace"Da izinina Iya,Jiya take Sanar dani tana So taje akwai wanda ba lafiya ne,ba dadewa zatayi ba Ranar Lahadi zata dawo.."Yafada yana kallon Hajiya iya wacce ta wani mele baki tana Fadin"Sai ta dawo Tunda kai ka Daure mata gindin gantali Agari,Mutum bazai ma kanshi Fada,Sa'o'inshi da kannenshi Sun gama kammaluwa agidan Aure,Allah dai ya Sauwake Wlh..."Tafada tana komawa daki .
Mirmishin yake Asma"u ta saki aranta tana jin bazata bari Hajiya iya Ta bata mata Mood dinta na Farinciki ba,Kallo Abba tayi tana Fadin"Abba zan Wuce bana son nayi dare ahanya.."Gyada kai yana Fadin"Gaskiya ne Ma"u Duk inda zakaje katafi ido na ganin ido,karbi kiyi na mota,kinji dai yadda mukayi dake kidawo Ranar lahadi na barki ne Saboda kin Dade bakije ba.."

YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU..
FanfictionTAYI NASARAN RABASHI DA KOWA NASHI YAZAMA NATA ITA KADAI..SHIN ZATAYI NASARAN RABASHI DA MATAR DATAYI KUTSE CIKIN RAYUWARSHI..?KO KUMA ZAI CIGABA DA ZAMA NATA HAR ABADA..