ZAMAN GIDANMU..

789 24 2
                                    

*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_

*Jamila Umar(Janafty)*

          

......" *Alhaji Ladan Sharif Mai Auduga*  Shine asalin sunan mahaifin Asma'u wanda haifaffen garin babban birnin jihar Jigawa ne, wato Dutse, ya samo asalin laƙabin Mai Auduga ne sakamakon tun yana matashi yake manominta, ya gada ne shima a wajen mahaifinshi, dan da ita aka sanshi har kawo yanzu, domin itace rufin asirinshi, Alhaji Ladan baiyi karatun boko ba sai na addini, sai daga baya ne kana suka shiga makarantar yaƙi da jahici.

    Mahaifinshi ya rasu sai mahaifiyarshi mai suna Hauwa'u wacce ake kira da Hajiya Iya, ya'yansu goma cur na da suka haifa kuma babu wanda ya koma duka suna nan da rayuwarsu, kai tsaye bazaka kirashi da mai kuɗi ba, amma za'a iya sakashi cikin sahun masu kuɗin dake zaune a unguwar Gida Sittin dake Dutse, matarsa ta farko mai suna Mandiya wacce ake kira Ummah auren zumunci akai musu, Mandiya irin matan nan ne masifaffu, ga son abun duniya ga ƙyashi, ba laifi itama mahaifinta ya mutu ya bar musu tarin dukiya, shiyasa Hajiya ta matsa kan sai mahaifinta ya aurota domin Hajiya Iya itama akwai son harka da masu dashi.

  Shekaransu biyar da aure har tayi haihuwa biyu 'yarta ta farko itace Aunty Ruƙayyah, sai mai bi mata Aunty Bilki, tun a lokacin yaso ƙaro aure, saboda yana ƙaunar Allah ya bashi ɗa namiji domin shine duka burinsa, sai Hajiya Iya ta hanashi, badan yaso ba ya bar maganar, kuma tun daga kan Aunty Bilki sai haihuwa ta tsayama Ummah cak bawai don ta gama ba sai don haka Allah ya tsara mata.

  Zuwanshi Bauchi wajen harkan sana'rsu ta Auduga achan ya haɗu da mahaifiyar Asma'u wato Habiba, kuma tunda ya ganta ALLAH ya ɗora mai sonta baiyi ƙasa a gwiwa ba ya nemi gidansu kuma ya gana da mariƙinta wato wan mahaifinta, domin lokacin Allah yayi ma mahaifinta rasuwa ba tare da jin ta bakin Habiba ba aka bada aurenta ga Alhaji Ladan, duk da ko da taji ba taji daɗi ba, amma bata nuna ba sai ta sadda kai tayi biyayyah ga iyayenta aka sanya ranar aure akayi biki aka ɗauketa daga Bauchi zuwa Dutse.
 
   Lokacin da Alhaji Ladan yajema Hajiya Iya da maganar Habiba bataso ba, amma ganin shi ya dage ne yasa ta amince, amma bayan taja kunnansa kada ya sake ya wulaƙanta Mandiya wato Ummah, ya kuma mata alƙawarin hakan ba zata taɓa faruwa ba, tunda Ummah taji za'a auro Habiba shikenan hankalinta ya tashi ta fito da kishinta muraranta, har aka kawo Habiba gidan nan Ummah na cikin masifa da Alhaji Ladan, kawai baya biye mata ne, saboda yadda ta samu ɗaurin gindi a wajen Hajiya Iya.

   Da farko zamansu ya fara daɗi saboda Habiba mace ce mai tsananin hakuri da kawaici, koda Ummah tayi mata wani abu bata tankata, kuma tunda ta lura Hajiya Iya na nuna bambamci tsakaninta da Ummah tafi sonta akan ta, bata damu ba ta watsar da komai ta rumgumi mijinta hannu bibbiyu, watan Habiba biyu da zuwa gidan ciki ya ɓulla a jikinta, murna wajen Alhaji Ladan ba'a magana yana ta addu'ar Allah yasa wannan karon ya samu namiji, tunda Ummah taji haka shikenan hankalinta yaƙi kwanciya ta dinga shiga tana fita domin tayi alwashin bazata taɓa bari Habiba tazo daga baya ta haifi ɗa namji a gidan ba.

   Ko ita kanta Hajiya Iya bata ƙaunar taga Habiba ta haifama Ladan ɗa namiji a gidan, ita ko Habiba ba tasan wainar da suke toyawa ba, illah ta maida kanta ga kula da kanta da abunda ke cikinta, da kuma kai kukanta ga Allah, don ita mace ce mai yawan ibada, haka dai har cikinta ya kai wata tara, rana tsaka ta tashi da naƙuda Alhaji Ladan ya kwasheta shi da su Hajiya Iya zuwa wani private Hospital inda aka shigar da ita labour room.

  Ko awa ɗaya ba'ayi ba sai ga wata nurse ta fito da dariyarta tana faɗin Habiba ta sauka, cike da tsantsar farin ciki Alhaji Ladan ke faɗin Masha Allah, Hajiya Iya ko da Ummah haɗa baki sukayi wajen tambayar me Habiban ta haifa cikin fara'a nurse ɗin ke sanar dasu ta samu ɗiya mace, washe baki sukayi suna hamdala a tare, shiko Alhaji Ladan yaji mamakin abunda sukayi amma sai bai kawo komai a ransa ba, duk da bai samu abunda yakeso ba, bai nuna damuwarsa ba,.sai washegari aka sallami Habiba suka dawo gida aka shiga kiran dangi ana sanar dasu labarin haihuwar....

ZAMAN GIDANMU..Where stories live. Discover now