*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_*Jamila Umar(Janafty)*
Duk da Asma"u batayi Wani barcin kirki ba bai hanata tashi akan Lokaci ba,Ko data idar da Sallar A subama Bayan Tagama Azkar din Safe,Bata koma ba Fita tayi Zuwa babban Falon gidan inda ta tarar Da Maman Fati nata aikin Hada Abun kari a kichen.
Gaisheta Tayi Cike da kulawa kafin ta tambayeta Dame Zata Taimakamata,Firan Dankalin Datakeyi ta Sakarmata ita kuma Ta koma wajen Dama garin kunun da Zata dama ma Mallam suna cigaba da Hira jefi jefi,Inda take son Mamanta kenan bata da yarda wata yar aiki tayima mijinta abinci ba,Tunda hajiya bata da lafiya ita keyin girki kullum sai dai indan Yalwa tazo ta taimakamata da Wasu ayyukan kamar Su wanke wanke da Gyara gyaren Waje
Tagama Fere Dankalin kenan Ta dora Koskon Suya ta Kalli Maman Fati tana Fadin"Mama yau fa zan koma..."Dakatawa tayi ta Zuba Ruwan Zafi acikin Fulas Tana Fadin"Yau kuma Ma"u nasha sai gobe.."?Girgiza kai Asma"u tayi kafin tace"A"a dama yau Abba ya bani kuma ko ba Haka ba gobe ina da Zuwa asibiti.."Shuru Maman Fati tayi kafin tace"Toh Shikenan ki karya sai kiyi Haraman Tafiya kada kiyi Dare,ai mun gode.."Dakai ta amsa mata kafin ta Cigaba da Abunda takeyi Ita kuma Maman Fati Ta dauki Fulas din Ruwan Zafin Ta Fice Daga kichen.
Kafin Wani lokaci Asma"u ta kammallah komai,tana Kokarin gyara kichen din sai ga yalwa tazo,suka gaisa ita ta karbeta ita kuma ta Koma daki tayi Wanka ta Iske har Maman Fati ta Shirya su Fati Cikin kayan Haddarsu Ita da Mahamud,sai Tura baki Suke suna fadin bazasu ba,Maman Fati tace Dolensu kuwa,Dariya Abun yabama Asma"u aranta tana Fadim"Kuruci Dangin Hauka.."
Koda ta Fito wankan Maman Fati bata a shashen,kayan jikinta Ta maida Tunda Jakar kayanta gabadaya yana Shashen Hajiya,hijabinta ta Maida kafin Ta Fito daga Shashen Maman Fati Zuwa Shashen Hajiya,Tana Shiga da sallama dashi tafara Hada ido yana Zaune akasa kusa da kafafun Hajiya,yana sanye da Jallabiya mai Ruwan Toka,Fuskarsa ta Fayau ammh kuma ta bayyana Rama Kadan,gabanta ne ya fadi Duk sai ta Daburce sanda Hajiya Dasu Anty Safina ke amsan Sallamanta.
Cogewa tayi abakin kofar takasa Shigowa kanta na kasa,hajiya ce tace"A"a Asma"u kariso mana,jiya kuma sai aka min Yaji ko..? Tafada Tana yar Dariya,Jikin Asma"u Asanyaye ta kariso chan nesa da Hajiya ta Durkusa tana gaisheta ta amsa Cikin Sakin Fuska tana kara Fadin",Haba Ma"u kuma Shikenan jiya sai kika gudu wajen Habiba ko..? Kanta na kasa tace"Ba haka bane Hajiya,barci ne ya kwasheni bansani ba.."Hajiya ta Kada kai tace",oho koda Naji,kin tashi lafiya.."?Ta amsa da lafiya lau kafin ta juya barayin Su Anty Nafi ta gaishesu,Amal yar wajen Nafi ce ta rarrafo wajenta sai ta yunkura ta dauketa tana Satar kallonshi.Kanshi na kasa yana Latsa wayarsa dakyar tace"Ina kwana..."Yana jinta ammh ya basar kamar bada Shi take ba,ya Lura yarinyar Tana da jin kanta sai da Hajiya tace Baffa bakaji Ma"u na gaisheka bane,kana ya Dago yana amsawa da lafiya kawai Daga haka ya Maida kanshi ga latsa wayarsa,Asma"u ko kanta na kasa tana Wasa da Amal ammh duk Sai taji ta takura,gashi tana Son tashi ta Shiga dakin Hajiya ta Dauki kayanta,kuma ta kasa Don sai ta Wuce ta gabanshi,shiyasa tayi Zamanta Kanta na saka tana wasa da Amal dake hannunta.
Maman Fati ne ta Shigo dakin Dauke da wani babban Farantin kayan karyawansu bayanta yalwa ce itama da Wani Farantin Anty Nafi ce tatashi da Sauri ta karbeta tana gaisheta,amsawa tayi Cikin Fuska kafin su gaisa da Anty Safina ta juya suna gaisawa da Hajiya,Tana jinsa yana gaida Mamanta ta amsa tana mai Tsiyar Wanda ya bar gida,Ganin Asma"u Zaune yasa tace"A"a Asma"u baki Shirya ba,Kada fa kiyi Dare Bisa hanya Baida amfani.."
Da Mamaki Hajiya ta kalleta tana Fadin"Ta Shirya Zuwa ina...? Maman Fati tace"Dutse Zata koma Hajiya,dazu take Fadamin Babanta yau yace Ta dawo kuma gobe tana da aiki.."Hajiya tace"Kai da Wuri haka Ma"u,Gaskiya banji Dadi ba,Da kin bari Zuwa gobe.."Kanta na kasa tace"Hajiya Nima na So haka,ammh ina da Aiki ne gobe Da Safe Shiyasa.."..

YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU..
Hayran KurguTAYI NASARAN RABASHI DA KOWA NASHI YAZAMA NATA ITA KADAI..SHIN ZATAYI NASARAN RABASHI DA MATAR DATAYI KUTSE CIKIN RAYUWARSHI..?KO KUMA ZAI CIGABA DA ZAMA NATA HAR ABADA..