ZAMAN GIDANMU..

3.5K 106 2
                                    

*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_

*Jamila Umar(Janafty)*

*Bismillahir rahamanir Rahim*

_*GARGADI:BAN YARDA WANI KO WATA YA JUYAMIN LBRINA BA,WANNAN LBRIN MALLAKINA NE,BAN YARDA A SARRAFASHI TA KOWACCE SIGA BA,YIN HAKA ZAI SA A HADU DA FUSHIN HUKUMA*_🖐☝

_I Dedicate Dis 1st page To u my Friends 4evrer...👫👬 *AHMED MUSA* 😘And u *JABIR ABUBAKAR* 💔 Tanque Dudes..Tanque For ur Advice_👐

    *Free page*    0⃣1⃣

_DUTSE-Jigawa_

......."Misalin Karfe 2:30pm Na daren Ranar Monday,Litini kenan acikin anguwar Gida Sittin,Sautin karan Alamar din data Saitashi acikin wayarta Wanda ke Tashinta Duk Dare,shine yafara Bugawa Ajikin wayarta Dake Kan wata karamar Dirowa dake Gefen Katifarta

Cikin Natsuwa ta Farka Tare da mika,kafin Ta Zuro da duka kafafunta Waje,Wayar ta Fara Dauka ta kashe alamar din kafin tayi amfani da wayar wajen Haska dakin Sakamakon ko"ina ya dau Duhu Dumdim ,Nepa sun Dauke Wuta Tun kafin ta kwanta, gen kuma tana Tunanin Mai ya kare ya kashe kanshi,da Hasken Fitilan wayarta tayi amfani ta haska har ta Dangana da Tiolet din dake Dakin Tarki ta Farayi kafin ta Dauro alwala ta Fito tana Tsane Ruwan Fuskarta da hannunta,Kai tsaye Dirowan dake Manne da Katifarta ta Nufa inda ta Dauki Dardumanta ta Shmfidata agabas,hijabinta Shima dake Ninke awajen ta Dauka ta Saka Wanda yakai mata har kasa,daga gani ta ijiyeshi ne Domin ibadarta,wayar Hannunta ta ijiye a gefenta,Gabas ta kallah kafin Ta daidaita Natsuwarta Ta Tada Sallah.

Sai tayi Raka"a Goma,sai kuma tayi Shafa"i da Wuturi Raka"a Uku kafin ta Sallame,Cikin Natsuwa ta kalmashe kafarta Ta sanya yatsun Hannunta tana kirga dashi,Ba"a ganin Fuskarta Saboda Dakin yana Da Duhu sai dai ana iya ganin Inuwarta,Cikin hakane Ta Daga Hannayenta Sama tana Kwararoma Allah kirari _Ya Allah Don Girmanka da Isarka Don Mulkinka..Ya Allah Don Gudurinka Ya Mahaliccin Samai da kasa,Kaine kake Umartan Abu yafaru kuma ya Faru Nan take,Ya Allah kaine Gatan kowani Bawa kai ka Umarci kifi daya Hadiye Annabi Yunusa,kai kuma ka Umarci Wuta Data zama Salama ga Annabi Ibarahimu,Kai ne Shugaban Halittun Duniya,kai Ubangijin Annabinmu Muhammed Salallahu alaihi Wasallam,Yakai mai Sunaye Guda 99 Da Tara Nayi Tawasalli dasu ya Allah na sani kana sane dani baka kuma Manta dani,Kai ne kake bawa Wanda kaso arziki ko wani kawan Duniya ka kuma hana Wanda kaso ba don baka son Shi Ba sai don Jaraba imaninsa,Kai kuma kai Aurar da wanda kaso,ka hana wanda kaso,ka azurta wanda kaso ka Hana wanda kaso..Ya Allah na karbi Kadarrata hannu bibbiyu Allah ina Rokon ka Sanya Jinkirina ya Zama alheri Allah ka Bani Miji na gari wanda Zai Soni Tsakani ga Allah,wanda zaiji kaina ya Mutumtani dani da iyayena Gabadaya..Ya..Allah...Ya.Allah.."_

Take Fada kuka na cinta kafin Ta kife Fuskarta da Duka Hannayenta tana Sakin Shesshekan kuka mai Cin rai,sai da tayi ya Isheta kafin ta Dago Fuskarta Bayan ta Share Hawayenta,Wayarta ta Dauka ta Duba taga 5 Saura na asuba da Hanzari ta Mike Ta Cire Hijabin jikinta ta Ninkeshi tare da Sallayan ta Maidashi inda ta Daukoshi Tana Kokarin Fitowa Daga Dakin, Sai ga Nepa sun Dawo da Wuta kau kamar Rana,ajiyar Zuciya ta Sauke sai alokacin na dago ina kallonta Yar Matashiyar Budurwa Ce Wacce akallah zata kai Shekara 26 aduniya Fara ce Doguwa,mai Dauke da Dogon Hanci tana da Fadin Fuska ammh ba Sosai sai bakinta daya kasance yana da Fadi kadan,daga gefe da gefe kuma ya Tsuke kanshi,Akallon Farko in kayi mata zaka Fahimci Tana da Dirin Mata,domin kirjinta ne ya bayyana cikin kayan Barcin dake Jikinta Riga da Wando,Kanta na Sanye cikin Wata Hula mai Raga raga kamar ta Sakan Zare,wanda Har ana Iya Hango Kitson kalaban data Hadesu Waje Daya ta Dauresu da Band,Yanayin yadda kan natayi ne zai sa ka Fahimci tana da Yalwar Sumar gashin kai.

*ASMA"U LADAN SHARIFF* Kenan Tana cikin Jerin ya"yana Na Uku acikin Jerin ya"yansa goma da Allah yabasa,ma"akaciyar asibitice waccce ke aiki ababban asibitin Jahar Dutse

ZAMAN GIDANMU..Where stories live. Discover now