*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai Cike da kunci)_*Jamila Umar(Janafty)*😘
1️⃣4️⃣
Sai da Baffa ya kwashe Sati biyu Cur a Garin Bauchi kana ya Koma portharcourt,Wanda Kafin yatafi sai da Mallam yakara Zuwa Wajen Mallam D'abarani ya karbo Mai Wasu Ruwan Addu"an,wanna Karan a kananan Goran Swan ne,Daya na Wanka Daya na Sha ne,sai wasu Addu'o'in da ya sake Rubutamai Kuma Alhamdulillah Sunga Chanji Sosai Shi kanshi Abdallah yafara Dawowa Cikin Hankalinshi.
Ta jirgi ya Koma Portharcourt Wanda Mallam da kanshi ya kaishi Har Filin jirgi na Abubakar Tafawa balewa Dake Bauchi Shida Mamman,Hajiya ko da Su Anty Nafi da Baffa Zai Tafi Rikesa Sukayi Suna Kuka,Domin gani suke in yatafi To sai Yafi da Da dadewa kafin yazo Gida,Hajiya ko Takasa Tsaida Hawayenta Saida Abdallah ya Duka Yana Share Mata Hawaye Yana Tabbatarmata da Cewa bazai Kara kwatatanta Abunda yafaru abaya ba,Insha Allahu Zai Dinga Zuwa Gida akai akai da Zarar Bukatar Hakan ya taso,da wanna Kalaman ya Taushi Zuciyar Hajiya Suka Rabu Cike da Kewa,haka ma Maman Fati da su Mahamud Suka Rike hannayensa kamar kar yatafi,sai da Mallam ya Ankarar Dasu Cewa Jirgin da Zai bi saura Lokaci Kadan ya Tashi kana Suka Sakeshi Yafada Mota Shida Mallam Mamman ya Fice Daga haraban Gidan Suna Daga Musu Hannu,shi kanshi Baffa Yana Jin Wani kwarin gwiwa acikin Ranshi Hawayen Hajiya Yafi Komai Dagamai Hankali,yanajin Shi kanshi baya kyautama kanshi Wanda baisan Dalili ba,ammh yayi alqawarin Gyara kurakuranshi na da Izinin lahi.
Su Mallam Basu Baro Airport ba sai da Jirgin su Abdallah ya Tashi ya Lula Sararin Samaniiya,shi kanshi Mallam kafin su Rabu sai da ya Dinga Jaddama Abdallah kada ya Sake yayi Wasa da Amfani da mgungunarshi,Kuma Kada ya Koma ya Shagala ya Manta da Addu"o'i tare da Azkar,Cike da ladabi Abdallah ke Fadama Mallam Cewa Insha Allahu Zai Kiyaye,Da haka suka Rabu Bayan Sun Rumgume juna,shi kanshi Mallam sai da ya Share kwallah,Yana Fatan Allah Yasa Karshen Wahalansu Kenan Akan Baffa.
Daganan Cikin Mkranta ya Wuce Zuciyarsa Duk ba Dadi,Gida kuwa duk Sai yazama Wani iri,Hajiya Dakinta taShige ta kwanta tana Tunanin Zucci,Aranta Tanajin Lokaci yayi da yakamata Itama ta Motsa Domin Tunda Har Baffa hankalinsa yafara Dawowa gida,to ya kamata Anemi wani Abu Wanda Zai Kara karkato Dashi na Har Abada,Wanda ko Matarsa Bata Isa tahanashi Zuwa garesu ba,tana wanna Tunanin Har barci ya kwasheta,su Anty Nafi Basu Dade ba kowacce taKoma Gidan Mijinta Hajiyama Bata Tashi ba lokacin,Maman Fati sukama Sallama da Zasu Tafi,haka Gidan ya Wuni Babu Wani Walwala,shi kanshi Mallam din har ya Dawo Bai da Wani karkarshi Hankalinsu Bai kwanta ba sai da Abdallah ya Kira wayoyinsu ya Sanar Dasu ya Sauka Gida lafiya,hatta Maman Fati Sai da ya Kira,shine Zuciyarsu ta Dan kwanta Suna Kuma ji Aransu Insha Allahu Sukeda Nasara.
*******. ********. ********PORTHARCOURT*
wasila Bata da masaniyar Dawowar Abdallah Domin Bai kirata ba,Wacce ke kwance bisa Daya daga Cikin kujerun Falon,kallo daya Zakamata ka zata Ta Shiga Haukane Saboda yarda Ta Dawo kamar Wata Mahaukaciya Sabon kamu Saboda Tashin Hankali,sanye take da Riga da wando,wandon mini ne Kuma ya kamata Sosai,sai Wata karamar Riga Mai Kama da Shimi,Iyakarta Cikinta Don ko Cibiyarta Bata rufe ba,kitson Attachement din ya Tsufa Duk ya Fara Tugewa Saboda Dadewa,Fuskarta Duk ta kode hartafara Wani Tambarin Baki baki,da wasu kananan kujera na kazanta,Idanuwanta sun Kada sunyi Jawur,da alamun Wuni Suke Suna Zubar kwallah.
Ita kadai ce Afalon,su Jamila Suna dakinsu Domin yanzu Indai Anty Wasila na Falo suka Fito Sun bani da Masifa Duk sai Ta nemi Hucewa akansu,yanzu ba Halin Su Shiryawa su Fita club in Suka Dawo takama Bala"I Sai Sun Raina kansu,Gabadaya ta takura Musu ta damesu Kuma so ko Tsausayamata basa yi,Sudai Kawai Suji Dadi su Hole Tunda ita ta sakarmusu ammh yanzu ta Fara chanza Musu ko Kudi bata Basu balle Su Fita su Ji Dadin Rayuwarsu,shiyasa Suma suke banza da ita Suyi Shigewarsu daki Ko zata Shekara Tana Kuka ko a haban Zaninsu,toh ko su emeka da Josepen Basu Tsira ba kuskure kadan Mutum Zaiyi Sai ya Raina kanshi Ranar Har Sai da ta Shararama Josepen mari,Wai takan ya Kawo mata lemon Fanta ita Kuma Maltina tace,shine Kawai ta kasheshi da Mari,Toh ya ya iya Banda Hakuri Domin ba karamin Aikinta bane ta Bashi Red Card.

YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU..
FanfictionTAYI NASARAN RABASHI DA KOWA NASHI YAZAMA NATA ITA KADAI..SHIN ZATAYI NASARAN RABASHI DA MATAR DATAYI KUTSE CIKIN RAYUWARSHI..?KO KUMA ZAI CIGABA DA ZAMA NATA HAR ABADA..