*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai Cike da kunci)_*Jamila Umar(Janafty)*😘
1️⃣3️⃣
*BAUCHI*
...... Zuwansu Yusuf yasa kewar Asma"u Bata taba su Hajiya ba Sosai ba Nan aka sake sabon Zaman Hira gida ya Gama Haduwa,Baffa ko da Yusuf suna gefe,suna Hira Jefi Jefi domin Baffa dama ba ma'aboci Mgana bane sai Ta Kama Ranar in kaga Ahalin sai kaji Sun burgeka Ganin yadda kowanne Fuskarsa ya cika da Annuri lalle Baffa Shine jigon Gidan Proff.Abdallah Azare.
Mallam Bai Fita ba Aranar Sai Zuwa da yammaah Suka Fita Shi da Yusuf Wanda Hajiya ce Take da Labrin inda zasu,Ko Baffan Bai sani ba,yana dakin Hajiya kwance acikin Bedroom dinta Gajiya yayi da Hayaniyarsu Nafi yashiga ciki ya kwanta,Chan ma Bai samu Runtsawar ba Saboda Kiran Wasila kamar mayya sai lokacin ya samu Kiranta,Kuka Reras take sakin Mai Tana Fadin yayi Tafiyarsa Bai Sanar Da ita ba,Lallashinta yafarayi Yana Fadamata Tafiyarce Tazo ba Shirin Shiyasa,Nan Wasila Tace Ko ya gayamata Ranar Da Zai Dawo ko Itama gobe ta Biyoshi Bauchi,Jin Haka yasa hankalinshi yatashi Domin yasan yadda iyayensa da Yan"uwansa Suka Tsani Wasila Zuwanta bazai Hafar da Mai ido ba.
Hakuri yadinga Bata Yana Tabbatarmata da Zuwa jibi Zai Dawo,Duk da Bata yarda ba ammh Taji dadin gane Haryanzu Abdallah Nata ne ita Kadai Sun Dade Suna Mgana a waya tana Narkemai kamar Wata yarinya Kafin su Rabu Shima Shigowar Hajiya yaji shiyasa ya Yankee Kiran,Hajiya Bata Kawo komai Ba don data Shigo Saurin Runtse ido yayi kamar Mai Barci so Bata gane Komai ba,lekasa tayi Kafin ta Dafa kanshi Cike da Tsausayawa kamar Wani karamin Yaro,blanket taja ta Rufemai Kafafu kafin ta Fice tana Rufemai kofar.
Kofar ya Kurama ido Yana Sakin ajiyar Zuciya,Polina ya Lalubo itama din Kukan Shagwaban ta sakamai ammh ita na tayi kewarsa ne,ammh Bata Nuna damuwarta ba kamar yadda Wasila Ta Nuna Na Zuwanshi Bauchi Hirarsu Sukasha Cikin Romantic love kafin Suyi Sallama,Yana nan kwance Yana Tunanin Yadda abubuwa Suka Faru Dashi kamar amafarki Barci Mai Nauyi ya kwashe,dama Kuma ga Hayaniya tasa kanshi yayi Nauyi.
Suko Mallam da Yusuf wajen Wani abokin Mallam sukaje Wato Mallam D'abarani Wanda ya kasance Malami ne na Boko Dana Addini ya Shahara Kuma yayi suna Wajen Bada mgungunar Musulunci Kama daga kowani Cuta har Zuwa na Sammu,To abokin Mallam din ne Sunyi karatun Addini tare Wajen Wani malaminsu Dake Azare,akwai kyawawan alaqa Sosai atsakaninsu ko lamarin Abadallah ma Yana Fadamai Yana sakasu Cikin addu"a toh adaren Jiya Sunyi Mgana da Mallam yamai bayanin Zuwan Abdallah da wasu Karin bayanai Shine yace gobe da Yammaah yazo ya Sameshi agidanshi Sukara Tattaunawa,shine ya nemi Rakiyar Yusuf Suka Tafi Tare.
A D'anjuma goje Mallam D'abarani ke Zaune da iyalansa Nan Su Mallam sukaje dayake yasan da Zuwansu aka saukesu Cikin Babban Falon da yakan Sauke bakinsa masu Muhimmanci,Bayan ya Fito sun gaisa sai Kuma bayanai Suka biyo baya Sai da Mallam Da'barani yagama jin Komai kafin yayi gyara Murya yace"Masha Allah Naji Duka bayananka Mamuda,mganar gaskiya ayadda Duka abubuwa Suka Faru yaron naka Sihiri ke Dawainiya Dashi..."
Gyada Kai Mallam yayi Yana Kallon Yusuf Wanda Shima ya Natsu Yana Sauraran Jawabin Mallam Da'baranin ,Ganin sun yi Shuru ne yasa Mallam din ya Cigaba da Fadin"Kuma kowa yasan Cewa Sihiri gaskiya ne Don ma Anuna mana gasgastan Hakan Sai da ya Kama Shugabanmu Annabi Muhammed (SAW)..."Suka Cike Salatin gabadayansu kafin ya Dora da Cewa"Toh mganar gaskiya itace Mu bamu Isa mu Yi abunda Allah Bai Tsara ba,Sai dai zamu Mika Al"muranmu ga Allah,akwai addu'o'in karya Sihiri Wanda Za'a Tofasu Aruwa,nasha ne Dana Wanka sai Kuma Garin magarya da Zan Hadamai da Wasu Karin magunguna da Zai Dinga Sha Yana Wanka Dashi da izinin Allah Duk Sihirin Dake jikinsa Zai Warware da yardan Allah.."
Gabadaya daga Mallam Har Yusuf suka had Baki Wajen Fadin.."Allah Shi yarda..."Daganan Mallam D'abarani ya kalli Proff.yana Fadin"Karka damu Komai Zai Daidaita sai dai Kuma Adage da addu"a domin Ita Addu'a makamin Mumuni ne,Wannan ne yaron wajen Naka..? Yafada Yana Kallon Yusuf.

YOU ARE READING
ZAMAN GIDANMU..
FanfictionTAYI NASARAN RABASHI DA KOWA NASHI YAZAMA NATA ITA KADAI..SHIN ZATAYI NASARAN RABASHI DA MATAR DATAYI KUTSE CIKIN RAYUWARSHI..?KO KUMA ZAI CIGABA DA ZAMA NATA HAR ABADA..