ZAMAN GIDANMU..!

1.8K 64 39
                                    

*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai Cike da kunci)_

*Jamila Umar(Janafty)*😘

_*Alhamdulillah Allah Ne Abun godiyata akoda yaushe,Tun kafin LABARIN ASMA"U Ko nace ZAMAN GIDANMU yayi Nisa Mutane Sun Fara Tsinta ko Nace gane inda Alkalamina ya Dosa,Naji Dadin hakan Sai Dai Tunda Nafara Rubuta Wannan Lbrin na Samu Text massages da Kiran waya Babu Adadi,Wato Yan Mata Da dama Suna Cikin Wata Rayuwa,Daga wacce Zatacemin kamar Lbrinta Nake Rubutawa sai Wacce Zatacemin Wlh Abunda Ke Faruwa Da Asma"u Yana Kan Faruwa Da ita!Ya illahi Wlh Tallafi na Zubarma da Sakonnin Wasu Hawaye Dadama,Shiyasa Nayi Amfani Da Wannan Damar Wajen Jawo Hankalin iyayen Mata Da Maza,Matar uba kike..?Antyn gida ne..? Uwa ce ke..? Toh ki Natsu Wlh Allah kadai ne Maiyi ,kuma ya Umarta yakuma faru a lokacin,Karmu Manta AURE na Allah ne,In kina Tunanin Ni ya"yana Sunyi Aure ko Kannena sun Samu Miji ko ya'yan Yayyena duka Sun Samu Miji shikenan sai Kifara zunden Wance,ita Bawani Lbrin ne..? Kuji Fa Wasu ma Cewa Suke Toh Wance Waye Kuma alayi.? Tun suna ganin Zabi ta tsayayi harda daga karshe Kiji ana Fadin Ta Tsaya jiran Mai Kudi,kuma iyayenta Na ganinta..! Plz my Sisters iyayenta Suna Da Ikon Aurar da Itane indan Allah bai yarda Ba,Wlh Aure da mutuwa lokaci ne,Ubangiji ke Dibanmusu,in Lokacinka Yayi Ko ka kashirya Ko baka Shirya ba,Wlh Zaka Mutu hakama In Lokacin Aurenka Yayi Ba Mutum ba Aljannah babu Wanda ya Isa ya Hana,Saboda karfin Lokaci Da Rabo Har Rasa Rai anayi,Kuma Haka Zalika In Lokacin mutum baiyi ba Wlh duk son Mutum da Aure Haka Zai Hakura Sai Ranar Da Allah yace,Shiyasa nake Kira Da Mu kama Allah Shine Majibincin Kowani Al"umura tare da Rokon Duk Wanda ya Karanta Wannan page din ya Daga Hannun ya Rokon Ma Duk yan'matan dasuke gaban iyayensu Babu Mijin Aure Allah ya basu Mafi alheri albarkacin Wannan Watan mai zuwa Mai albarka Wato RAMADHAN...AMEEN*_🤲👏😪

  *LAST FREE PAGE*👐

       1️⃣5️⃣

*BAUCHI*

      Misalin karfe 4:30pm na yammah,Proof.Muhamud Abdallah Azare Yana Zaune Acikin Daya Daga Cikin Manyan Kujerun Falonshi Wani Littafin Azkar ne Ahannunshi Yana karantawa Yana Sanye da Wata Jallabiya Doguwa Mai Ruwan Toka Harda Wata Hula Mai Kama Da Tabani Kaji Hadisi,😂,Idanuwansa Sanye Da Wani Siririn Glass Wanda Ke Taikamai Wajen Karatu,Gefe Daya Kuma Kira"a ne ke Tashi Acikin Katon Talabijin Din Dayayima Falon kwanya tashar Manara TV ne Suka Sanya Karatun Alqur"ani Cikin Suratul Ankabut,Cikin Kira"ar munshawi.

   Hajiya Tayi Sallama Ta Shigo Falon Cikin Kulawa ya Amsa Mata Sallaman Yana Kokarin gyara Zamanshi Lokaci Daya Yana Kallonta Kusa Dashi Ta Zauna Tana Fadin"Barka Da Hutuwa Mallam.."Bai Dago ba sai da Ida Karatun Dayake kafin ya Janye idanuwansa Lokaci Daya Yana Rufe Azkar din Dake Hannunsa.
 
   Dubansa yakai Kan Hajiya kafin ya Saki Mirmishi Yana Fadin"Yauwa Hajiya Hajiya Uwar Abdallah bawan Allah.."Ya Fada Da Sigan Zolaya,Mirmishi Ta Saki Tana Fadin"Kai Mallam Baka rabo Da Zolaya yau Kuma kirari Akejin yi ne.."Mirmishi ya Saki Kafin yace"Eh Mana Wato Hajara Kowa yagama Lura dake In Ana Son ganin Hakoranki awaje toh Ayi Miki Zencen Abdallah,Ciwo ya Kare ko Tunda yanzu Baffan Na Kula da Uwarsa Dakyau Dakyau.."Yafada Yana Yar Dariya.

  Kunya Takama Hajiya ta D'an Dara Tana Rike Baki,Dariya Mallam Ke Mata Cike Da Farinciki yace"Kina Rike Baki,ko nayi Karya Tsakaninki ga Allah Zaki Fada.."Bakinta Awashe Tace"Ni bance kayi Karya ba Mallam ammh.."Dakatar Da ita yayi Yana Fadin"A"a bar Mganar Maman Nafisa Tunda Dai Kin San Gaskiya.."Yafada Yana Kallonta Lokaci Daya Yana Mata Dariya.

  Gyara Zama Hajiya Tayi kafin Tace"Mallam wajenka Nazo Fa.."karkato Da Hankalinsa yayi Kanta Bayan ya saka Hannu ya rage Karan Karatun Da Remote din Dake kusa Dashi ya Maido da Hankalinsa Kanta Yana Fadin"Inna jinki Hajiya Allah sa Lafiya.."

  Muskutawa Hajiya Tayi kafin Tace"Wani Tunani nayi Game Da Baffa Mallam.."Da Mamaki ya Kalleta kafin ya Maimata Sunan da Sigar Tambayan"Baffa Kuma..? Cike Da kwarin Gwiwa tace"Eh Mallam,Duk da yanzu Hankalinshi ya Dawo Jikinsa ya Fahimci Mune iyayensa Na har Abada Wanda Bai da kamarmu,Addu"armu Bata Fadi kasa Banza  ba Mallam Tunda yanzu Zaka Ga Duk Safiya sai Baffa ya Kira mu Yana Tambayanmu lafiyanmu Wanda Abaya bamu Samu wannan Damar ba.."Ta Dakata tana Sauke Numfashi.

You've reached the end of published parts.

⏰ Last updated: May 10, 2020 ⏰

Add this story to your Library to get notified about new parts!

ZAMAN GIDANMU..Where stories live. Discover now