ZAMAN GIDANMU..

765 21 1
                                    

*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_

*Jamila Umar(Janafty)*

          

Koda Suka idar da Sallar Asuban Ma'u kara Matsama Hajiya tayi saida ta koma barci,ita kuma sai da ta gama Azkar Dinta kafin ta Tashi bayan ta Sanya karamin Hijabinta Datazo dashi acikin kayanta,Ta Fita Zuwa babban Falo,babu kowa sai dai taji motsi a kichen haka yasa ta gane Mamanta ne Ke aiki,da hanzari ta karisa kichen din tana Ma Maman Fati Sallama,wacce ke ta Faman Soya kwai,hade da Dankalin Turawa.

   Waigowa tayi tana amsawa lokaci Daya Ta washe baki tace"A"a Ma"u,Harkun tashi,ya hajiya ta kwana da jikin..? Asma"u na karisawa gareta take Fadin"Ina kwana Mama,Hajiya taji Sauki Don na matsa mata tayi barcI Sosai yanzu hakama na Sata ta koma.."Cike da Farinciki Maman Fati tace!Masha Allah naji Dadi Sosai Ma"u,.."

   Asma"u Ta kada kai tana Fadin"Toh ai dama Mama koda Hajiya na Shan mganin Hawan Jini,matukar bata samu Hutu da barci da kuma Kaucema hayaniya,Toh bazata rabu da Wannan Azababban Ciwon kan ba.."Jinjina kai Maman Fati ta Cigaba Dayayi alamun gamsuwa kafin tace"Hakane Kam,Allah yayi Miki albarka kema Allah ya jikanki ya baki mai miki Asma"u.."Ta amsa da Ameen Cikin Farinciki kafin tace"Me zan Tayaki Dashi Mama..?

  Maman Fati tace"Na kammallah komai Saura kadan na Karisa,Ammh Sai dai ki Shigarmin wajensu Mahamud yanzu haka Suna chan Wajen Tsiyansu na Fama,Shida Fati basu Shirya ba.."Kada kai Asma"u tayi tana Fadin"Toh mama,...Tafada tana Kokarin Ficewa Daga kichen din,Ta sa baki ta kirata.

  Asma"u...!Ta fada da kakkausan Murya alamun ba wasa kafin ta juyo tana maida hankalinta kan Asma"u Data waigo tana Fadin"Na"am Mama,.."Ajiyar Zuciya Maman Fati ta Sauke tana dafa hannunta ajikin Cabenet din dake kichen din kafin tace"Ya zaman gidan mahaifinki ?ta chanza zani koko har yanzu yana nan ayadda na Sanshi..."? Tafada tana Tsurama Asma"u ido,Saurin Sadda kanta Ma"u tayi kafin tace"Bai wani Chanza ba Mama,Kawai kinsan yau da gobe sai Allah,Nida ba Wuni ma nake agidan ba ina zasu ganni,.."Tafada tana kokarin boye Damuwarta.

  Girgiza kai Maman Fati tayi kafin tace"Haka dai kika ce Asma"u ammh ni na Haifeki nafi kowa sanin Zurfin Cikinki,Abunda nake So dake ki kara hakuri akan Nada,Insha Allahu Jinkirinki ya kusa Zama alheri.."Kan Asma"u na kasa ta amsa da Allah yasa acikin Ranta,Maman Fati na kallonta sai ma ta kada kai Ta juya tana kokarin Juya Dankalin Dake Cikin Mai take Fadin"Shikenan Dama,Jeki Dubamun Su Fatin in Sun Shirya.."Bata yi musu ba ta juya jikinta asanyaye ta Fita Daga kichen din,Maman Fati ta bi bayanta da kallo Cike da Tsausayi kafin Ta Kada kai Tana Fadin"Allah gamu gareka..."

  Koda Asma"u ta Shiga Falon Maman Fati babu kowa,cikin bedroom taji hayaniyar Su Fati,koda ta Shiga ta Iskesu Sun sarke da Rigima kan Wandon mkrantansu Na hadda,dayake iri daya Ne,Karisawa tayi garesu Tana Musu Yar dariya,suna ganinta gabadayansu Suka tafi gareta Suka Fada mata Suka Rumgumeta suna gaisheta da kwana,amsawa tayi tana Shafa kawunansu,Cike da Farinciki da Annuri.

  Ita ta Raba Rigimar bayan ta Fidda ma kowa wandonshi kuma ta Taimaka musu Suka Shirya,Kafin 7:30am Sun Fito Falo,lokacin kuma Maman Fati Tagama Hada musu Breafsat,ta kuma Zuba musu Cikin Luch box dinsu,Karyawan ma Sama sama Sukayi Ruwan Tea kadai Suka Sha,Fati ne ma taci buredi ammh Shi Mahamud irin Mallam ne bayacin Buredi dayake ma takwaranshi ne,kuma Mallam din da kanshi ya hana Kowa ya sakaya Sunan Yace kowa ya Kirashi da Mahamud dinsa.

  Sai da Suka Biya Shashen Proff.Suka gaisheshi da kwana zasu Shiga wajen Hajiya Asma"u ta hana tace ta kwanta,Dole Suka Hakura, haraba gidan Suka Fita da gudu kowanne da jakarsa,hanuun kowanne Rige da basket dinsu,Tunda Haddar mai Hade da Islamiya ce sai yammah Zasu Dawo,Koda Suka Fita har Mamman yazo,Shiga mota kadai Sukayi yajasu Suka Fice Daga gidan Zuwa mkrantar Nasu.

  
   Suna Fita Asma"u ta koma Shashen Hajiya,Tunda Maman Fati ta Shigarma da Mallam Abun karinshi Shashenshi ta barmusu Nata ita da Hajiya a kichen tace ta Dauka tatafi Dashi Chan Shashen Hajiyar,Tana komawa Ta Shiga gyaran Falon Hajiya dayake ma ba wani datti yayi ba Cikin lokaci ta gyara ko"ina,hatta Dayan bedroom din sai da ta Shiga ta gyarashi ta wanke Tiolet,Dakin Hajiya ta koma ta isketa Haryanzu Tana barci,Toilet din ta Shiga wanka ta wankeshi tas kafin ta Fito tana kauda wasu kayan Hajiya dake Bisa gado,Duk ta Ninke mata ta Bude Wardrope dinta ta Saka mata,ganin har Lokacin Hajiya bata tashi bane yasa ta Shiga wanka,bayan ta Fito ta Tsane jikinta ta Jawo jakarta ta Fito da Manta na Olive ta hau mulkama jikinta,sai da ta gama tsab,Kana ta Fito da wani Less dinta Doguwar Riga mai Kalan Maruon,da Zanen ja,Dinkin A shape ya Dace da Surar jikinta,Dankwalinta ta Daura irin Daurin Zamani na Zahra Buhari,Bata yi ma Fuskarta kwalliya ba,illah Liptick data Shafama bakinta.

ZAMAN GIDANMU..Where stories live. Discover now