ZAMAN GIDANMU..

818 25 0
                                    

*ZAMAN GIDANMU..!*
_(Mai cike da Kunci)_

*Jamila Umar(Janafty)*

            

Da karkarshinsa ya Tura Kofar Dakin Hajiya ya Shiga da sallama,ammh a ciki,dakin Shuru sai dai Wani Ni"imantattacen kamshi Turaren Wuta Daya Daki Hancinsa,Lumshe ido yayi kafin ya Bude su Fes yana bin Dakin da kallo har idonshi ya Sauka kan Hajiya Dake kwance kan gado Tana barci.
  
   Cikin Sanyi Jiki ya karisa gabanta yana Kare Mata kallo,gabansa ne ya Fadi,ganin irin Ramar da Hajiya Tayi Duk ta Zabge Ba wannan kibar Nata,da Cikar Fuska mai Cike da karamci,Tsaye yayi yana kallonta idanuwansa Sun chanza kala Sun kara ja,yana ji kamar ya Durkushe Bisa kafafunsa. ya saka kuka,Hajiya ko dake barci dayake Duk Nisan barcinta Hayaniya kadan ko Mutum ya matso kusa da ita Zataji yanzu Zata Farka.

   A hankali ta Bude idanuwanta Da Suka Shige Saboda Barci,Abunda tagani yasata Saurin Maida idanuwanta ta Rintse kafin Wasu Siraran Hawaye Su Zubomata ta Gefen Fuska,gyara kwanciya tayi Kafin ta Murmusa tana Fadin',Har Sai Yaushe ne Baffa Zaka zo gareni,?Akullum bani da wani mafarki sai na ganka Tsaye agabana.."Take Fada idanuwanta na Runtse tana kuma Share Hawayen da Suka zubo ta gefen Kunnenta.

  Jin Abunda Hajiya ke Fadi ne yasa baisan Sadda ya Durkushe gaban Hajiya ya kamo Hannunta ba,Cikin karaya Da Nadama ya Furta.."Gani Agabanki Hajiyata ki Bude idanuwanki Da gaske wannan Karon Baffanki ne agabanki ba Mafarki kike ba.."Jin Muryan Baffa da kuma Hannunta daya Riko yasa Hajiya Bude idanuwanta Fes akanshi,Kuramai ido tayi kafin ta wani Zabura Kamar Zata Fadi,sai gata ta Diro kasa da Mugun karfi har kafarta na Turgudewa Yayi Saurin Rikota yana kallonta.

   Kafadunshi Ta damka tana Girgiza Shi Take Fadin"Da gaske Baffa na ne,Agabana..? Abdallah kai ne kuwa Kodai haryanzu Ban Farka daga mafarkin dana sabayi bane na Kazo gareni.."Tafada Hawaye Suna kwaranyomata Kana Duka hannuwanta Biyu tana Shafa Fuskarshi,Shima kukan yake son Saki ammh kuma Idanuwansa Sun bushe Zuciyarsa ne kadai ke iya Fassara Hadin Bakin Cikin Dayake Ciki

  Ganin haka kawai yasa ya Fada Jikin Hajiya yana Sauke ajiyar Zuciya yana Fadin"Ni ne Hajiyata Abdallah ki ne,Don Allah ki yafemin bansan meya Sameni ba.."Yafada yana Runtse Ido Saboda yarda Kansa yake Saramai,Ai da hanzari Hajiya ta Kamkame Shi tana Dariya Hade da Kuka tana Fadin"Alhamdulliah Allah Mun gode Maka daka amsa addu"armu ka dawo Mama Na Abdallah garemu.."Take Fada tana kamkame Dashi tana Dariya da Kuka lokaci daya,yau Hajiya Duk ta Cire wannan alkunya ta Dan Fari ta na murna Zuwan Abdallah.

   Daidai Lokacin Maman Fati ta Shigo dakin Hankalinta tashe,Asma"u na Biye da ita abayanta,Ganin hajiya Rumgume da Wani Saurayi tana kuka yasa Suka yi Turus,Maman Fati bata samu Zarafin mgana Hajiya ta ankare Dasu,Da hanzari ta Saki Abdallah tana Riko Hannunshi take Fadin"Maman Fati mu gode ma Allah,yau dai ga Abdallah yazo garemu.."Sai alokacin Maman Fati taga Fuskarshi,Ware ido tayi kafin itama ta karisa garesa tana Damko hannunshi take Fadin"Hajiya Da gaske,Abdallah nake gaani ko kuwa Idona Keman Gizo.."?Tafada tana Shafa Fuskarshi Kai ya girgiza kafin kawai ya Durkushe gabanta yana Rike da Hannunta yace"Maman Fati,Ku min aikin gafara,ku yafemin Wlh bansan meya Sameni ba,har nayi wannan Tsawon Lokacin banzo gareku ba.."Yafada yana Sakin Nishi Sama sama.

  Kamosa Maman Fati tayi Tana Fadin"Ai mu ba Laifi tsakaninmu Baffa,sai godiya Ga Allah daya Sa kadawo kana Cikin Hayyacinka."Tafada Tana Dagosa,Hajiya Dake gefe banda Sharan Kwallah Babu Abunda Takeyi,kallon Maman Fati tayi tana Fadin"Kamar amafarki na ganshi Habiba,Waya gaya miki Zuwanshi...?

   Maman Fati tace"Asma"u ce Tazo Da gudu tana Haki take Cemin ga wani Chan ya Shigo gidan,wai ya Shiga Har Dakin Hajiya,Ganinta atsorace yasa Na boyota nazo na gani.."Tafada tana waigawa baya Inda Asma"u ke Tsaye sai dai Suka ga wayam,Bata adakin ita ko Asma"u Tunda Daga Hajiya Rumgume da Baffa tana Kuka Abun yayi Mata wani iri baya taja kawai Ta Fito daga dakin Tadawo Falo a zuciyarta Tana taya wannan Ahali Murna Dawowar Wanda Suka Dade Suna Nema.

ZAMAN GIDANMU..Where stories live. Discover now