BABI NA GOMA

347 12 0
                                    

Kamal da ke waje,har ya gaji da jira,sai gasu nan,sun fito,Samira da ta san halin sa na rashin son jira,ya sa ta yin dariya ita kadai.

Ranta ko kara mamakin sa take yi,na yadda ya zauna,ya jira su har suka fito,duk da lokacin da suka bata,wanda ta san inda ita ce,da ta sha masifa,ko ma ya ja motar sa yayi gaba,sai dai ta hau mashin ko keke napep.

Amma sai gashi wannan karan har da jira,lallai Hausawa sun yi gaskiya da suka ce So hana ganin laifi.....

Ganinsa ne ya sa Maryam ta shiga fadin

"Ya Kamal kayi hakuri don Allah,wallahi wani abu ne ya dan tsayar da mu,shi ya sa muka dade"

Don har ga Allah ita ta ma manta yana waje yana jiran su,dan murmushi ya yi mata,kafin ya ce

"No! kar ki damu,ba sai kin bani hakuri ba,ai na fada miki ba kya laifi a guri na"

Da haka ne Basira ta gaishe shi,ya amsa,da sakin fuska,kafin suka shiga motar,a wannan karon ma su Samiran ne suka shige baya,ita kuma ta zauna a gaba,sannan suka wuce....

A hanya yake tambayar su,ina ne Cafe din da zasu je,Samira ce ta bada shawarar su je Bajinta Cafe na kusa da gidan su,haka ya je ya sauke su a wurin,sannan ya wuce,bayan ya ce wa Maryam ta jira shi a gidan su,bazai dade ba zai dawo sai ya kaita gida....

Sun shige Cafe din inda aka fiddo musu da results dinsu,Maryam ta fito da A guda uku,sai B guda shidda

Samira da Basira kuma kamar hadin baki results din su ya fito iri daya,inda suka ci B guda hudu,A daya sai C guda hudu,ba karamin dadi suka ji ba

Sai ihun murna suke ta yi a cikin Cafe din,wanda hakan ya sa mutane suka shiga kallan su,sai dai ko a jikin su,sai da suka yi printing kafin suka fito don tafiya gida....

Bayan sun gama ne suka garzaya gidan su Samira,saboda a nan za a zo daukan Maryam,Basira kuma tayi waya gida,direban su zai zo ya ya dauke ta anjima.

Nan suka yi sallar la'asar,sannan Samiran ta sako musu abinci,White rice da miya,ta hado musu da ruwa tare da drink mai sanyi,suna ci suna hira cikin raha,Basira ma ta sake sosai kamar ba ita ba....

Wajajen karfe hudu na yamma,Ya Nabil ya iso gidan don daukar Maryam,sai dai kuma bai da nambar wayar ta balle ya kira,haushin kan sa ya dan ji da dazun bai amsa number din ta,karasawa yayi cikin bakin gate din gidan

Sallama da mai gadi akan don Allah yana so ne a kira mishi ita su wuce,mai gadin ne ya shige don ya kirawo ta,shi kuma ya koma cikin mota yana jiran ta.

Ko da mai gadin ya shiga ya ce an zo daukar ta,ta san shi ne,sai dai duk da ya ce mata zai dawo,bata yi tsammanin da gaske yake yi ba

Dama ta na da shirin kiran Dady ne akan ya zo ya dauke ta ko ya aiko Idi direba,sai gashi nan kuma ya zo,da haka ta shirya,ta kara wa Ummar su Samiran sallama,kafin suka fito da su Samiran don su rakata..

Danne-danne yake yi a wayar sa kirar iphone X ya ji an k'wank'wasa gilashin motar,whining glass din motar yayi,ganin su a tsaye,ya sa shi fitowa daga cikin motar,yayin da ya kai duba sa wajen da Maryam ke tsaye,wacce tayi saurin yin kasa da kanta

Su Samira ne suka shiga gaisawa shi,da fara'arsa sosai ya amsa musu,tare da sakewa da su tamkar ya dade da sanin su,kafin sukayi sallama da kawayen na ta

K'ADDARA TA Where stories live. Discover now