Sanda Maryam ta shige dakin ta,fadawa kan gado ta yi jiki a mace,ta rasa dalili,haka kawai,ta rinka ganin hoton Ya Nabil yana mata yawo a gilishin idanuwan ta.
Duk da tasan ba wannan bane karo na farko ta taba jin makamanciyar abin da take ji dangane da shi a yanzu,sai dai na wannan karon ya sha bambam,toh me ya sa?,ta san dai tun tana karama ta ke jin son sa a ranta,sai dai ta bar abin a matsayin yarinta,tare da danganta shi da sabon da suka yi tare da shakuwa
Anya ma ya san tana yi kuwa?take tambayar kanta,sai kuma wani wata zuciyar ta ce mata,tasani kila ma can makarantar da ya je ya hadu wata yarinyar seka soyayyar su,don ta lura kamar ba ta yar kayan sa.
Wanda haka ya kara sagar mata da gwiwa,ta nema farin ciki ta,ta rasa,tinawa da tayi bata yi sallah bane ya sa ta azamar tashi,tare da mamakin kan ta na dadewar da tayi tana tunani har lokaci ya tafi,bayan ta idar da sallar ne bacci barawo ya sace ta a nan kan dardumar da tayi sallar a kai..
☆☆☆☆
WAYE ALHAJI BASHIR
Mal Garba Mai -Atamfa shi ne sunan mahaifin sa,asalin su yan kano ne a cikin kamar hukumar Madobi.Gaba daya yan uwansa a nan suke,wadan da suke yan uba,kasancewar sa d'a daya wurin mahaifiyar sa,sakamakon yaran da take haifa suna mutuwa sai shi kadai ya tsaya,in da gaba Allah yayi wa iyayen na sa rasuwa.
Sana'ar sa ita ce sai da atamfofi da sauran kayayyaki,wan da tun ya nayi da kadan,har Allah ya buda masa ,ya samu karamin shago a nan cikin garin su ya sa kayan sa,wanda ta sanadiyar sana'ar sa ce,ya samu inkiyar karshen sunan sa wato mai atamfa.
Anan cikin kauyen nasu ya samu wacce yake so,yarinyar makocin su mai suna Mairo,ba a yi wani tunani ba akai yan uwa suka shige masa gaba aka musu aure,tun da gari ne da kowa ya san kowa,sannan sun yaba da hankalin sa.
Sannu a hankali sana'ar tasa take bunkasa wanda hakan ya su baro kauyen su zuwa cikin gari don kara kafa sana'ar sa, in da ya samu dan madaidaicin shago a nan kasuwar kurmi ya siya,sannan ya sama musu gidan haya matsakaici ciki da falo wanda bai da nisa da shagonsa suka zauna.Hankalin su kwance da matar sa,suke rayuwar su,so,aminci da kaunar juna.
Ana cikin haka ne ciki ya bullo jikin mairo,aiko dadi kamar zai kashe su,a haka suka suka cigaba da rainon cikin,har ya kai munzulin haihuwar,ta samu namiji aka sanya masa suna Bashir,sai dai bayan shi Allah bai kara basu wani dan ba,wanda haka ya dan so ya daga musu hankali daga farko,amma ganin Allah ya albarkace su da dayan ne ya sa su kara gode masa tare da rungumarsa hannu bibbiyu,tare da bashi tarbiyya dai dai iyawar su
Kwanci tashi,Bashir ya girma zuwa matashin saurayi mai cike da kwazo,Mal Garba bai yi ilimin zamani ba,sai na muhammadiya amma sun tsaya wajen ganin sun wadata Bashir da ilimin zamani da na addini,a wani bangaren kuma arzikin sa sai habaka yake yi.
Ana haka ne ranan suna hira da wani abokin sa,sai yake bashi shawarar me zai hana ya kara bubkasa kasuwancin sai zuwa wasu garuruwa ba sai a kano kadai ba har yake ce masa in har zai yiwu ya fara budewa a kaduna don garin yana da dadin kasuwanci shima,bayan ya gama nazarin shawarar da abokin nasa ya bashi ne,ya ga hakan ba karamin cigaba bane a gare shi,ya sa shi dauki shawarar,domin ya san bazai taba bashi shawarar da zata cutar da shi, godiya yayi ya shiga yi masa sosai na taimakon shawarar da ya ba shi.
Bayan ya gama tunani da shawara da mai dakin sa ya shi tsaida hukuncin barin kano zuwa kaduna,don kara kafa sana'ar tasa kamar yadda ya kudura,bayan ya bar shagon sa a hannun wani yaron da ke mai aiki ganin yana da kwazo da amana,da zummar zai rika zuwa yana duba yadda komai yake gudana..
Dawowar su Kaduna ne,ya siyan musu gida mai kyau da tsari a Kawo,sannan ya samu tafkeken shago cikin kasuwar gari ya zuba kaya kamar Atamfofi,laces,materials,shaddodi da sauran su wadanda yawancin su ba a nan ake kawo mishi ba ganin yanzu arziki ya ci uban na da😝kafin ya biya musu zuwa sauke farali a dakin Allah,in.da bayan dawowar su ne ya koma Alhaji Garba Mai Atamfa.
YOU ARE READING
K'ADDARA TA
RomansaBanko kofar dakin ta yi a fusace,dole yau ayi wacce za a yi a kare tsaknin ta da shi,hakimce a zaune ta same shi ya bama kofa baya daga shi sai boxers,ba riga sai karfaffn jikin sa d ke a murde,macbook pro na a gaba shi abnda ta hango a ciki screen...