BABI NA SHA UKU

378 28 0
                                    

Rayuwar gidan ya ci gaba da gudana ne cikin walwala da kwanciyar hankali..

Ko da Momy ta nunawa Dady kayayyakin da Nabil ya siyawa Maryam,fad'a ya shiga yi sosai shima,dan bai ga dalilin da zai ta barna tar da kudi a banza ba,har ya ce zai kira shi ya zo ya tafi da kayayyakin,da kyar Momy ta shawo kan sa ya hakura,akan ita ma sai da tayi mishi fada akan hakan,kafin nan ya hakura da zancen...

A bangaren Nabil kuwa,tun rannan da suka fita da ita,ba ta sake saka shi a idanun ta ba,yau kusan sati day'a kenan,wanda hakan ya fara damun ta,a tunanin ta,ganin ranar da suka fita,al'amomin da yake ta nuna mata kamar shi ma ya damu da ita,ashe abun ba haka bane..

Lallai ta yarda son maso wani take yi masa,sai yanzu ta san zafin rad'ad'in da mutum kan ji idan yana san wanda baya san sa...

Ashe samarin da ke bin ta tana k'in kula su,haka suka ji kenan?take tambayar kan ta,da ta san haka ake ji,da ta sassauta musu,ta kula su,tunda ita ma ga ta nan,tsundum cikin son wanda bai ma san tana yi ba...

A y'an k'wanakin kwata-kwata ta daina walwala,kullum tana dak'i dalili ne mai karfi ne ke sa ta fitowa,hakan ba karamin damun iyayen ta yake yi ba,musamman Dady,Momy kam zuba mata ido ta yi,dan ta dad'e ta gano halin da y'ar ta ta shiga...

Sai dai a yau dinne abun ya ishe Momy,dan kullum suka tambaye ta abunda ke damun ta,sai da ce musu ba komai,amma duk wanda ya san ta,ya kalle ta,a take zai gano akwai abinda ke damun ta,wanda har wata y'ar rama tayi...

Tana kwance a daki ta fad'a tunani wanda ya zamar mata farilla,ta ji an murdo kofar dak'in ta,tare da had'owa da sallama,d'ago kan ta tayi,don ganin mai shigowa,tare da amsa sallamar,idanuwan ta suka sauka kan na mahaifiyar ta,wacce ta ke karasowa in da take kwance,ta shi ta yi,ta zauna tare da jingina bayan ta da kan gado,sannan ta ce

"Sannu Momy",tana sadda kan ta kasa,saboda ganin irin kallan da take mata....

Bata ba ta amsa ba,ta zauna a gefen gadon kusa da ita,sannan ta ce

"Ai ke ya kamata a yi ma sannu,tunda kika dauki damuwa kika daura wa kan ki"

Kara sadda kai kasa tayi tana jin hawaye suna kokarin zubo mata,ita ba ta san ta yadda zata fara fadawa wa mahaifiyar ta halin da take ciki ba

"Ke da a tunanin ki,kina ganin akwai abinda zaki iya boye min ne,wanda bazan iya karantar sa a tattare da ke ba,Toh ki sani cewa ni mahaifiyar ki ce wacce na haifi ki da ciki na,na san ki na kuma san halin ki,wanda ko a fuskar ki zan iya gano abinda ke damun ki,na zuba miki idanu ne na k'yale ki,in ga ko zaki tunkare ni damuwar ki,sai na ga abun naki ba na kare bane"

Shiru tayi tana sake kallan Maryam,wacce ita ma ta kasa furta komai,ga jikinta da yayi sanyi sosai da jin kalaman Momyn,kafin ta cigaba da fadin

"Tun ranan da yayan ki Nabil ya zo gidan nan,na lura kika fara shiga halin da kike ciki,sakamakon son sa da kika fad'a"

Da hanzari Maryam ta d'ago kan ta ta sauke idanuwan ta kan na Momy,da t'sananin mamakin jin abinda ya fito daga bakin ta,ta yaya Momyn ta gane soyayyar Ya Nabil ne ke d'awainiya da ita?take tambayar kan ta...

Dan murmushin takaici Momy ta yi,sannan ta cigaba da fadar

"Kina mamakin yadda akayi na sani ne?"

Momy bata ba ta fuskar magana ba,hakan ne ya sa ta kara sunkuyar da kai,cike da kunya da kuma tsoro...

"Yaro man kaza;Sai dai wani abu da baki sani ba,shi ne ke mace ce,mai mutunci da daraja,ba ke ya kamata ki bashi damar da har zai iya gane halin da kike ciki a kan sa ba,mata an san su ne da jan aji tare da alkunya,idan kika yi hakuri,in har shi ma yana son ki,kina zaune zai kawo k'ok'on barar sa wajen ki,ba sai kin sa ya gano ke kika fara son sa ba,don su maza ba a nuna musu haka,da zarar ya san ke ce kike san sa har kika shiga damuwa,ba lallai bane ya dauke ki da daraja...

K'ADDARA TA Where stories live. Discover now