BABI NA SHA D'AYA

453 29 0
                                    

Tafiya suke don komawa gida,sai kuma ta lura ya doshe wata hanyar daban,bata iya ce masa k'ala ba,illa na mujiya da ta zuba,tare da maida hankalin ta kan kallan hanyoyin da suke ta wucewa,don ganin in da zai kai ta,duk da ta san bazai taba iya cutar da ita ba,da haka ta sake zuciyar ta suka cigaba da sharara titi...

A wannan dan t'saikun ne ta ji muryar shi ta zo mata a bazata

"Ya results din da kuka je dubowa,i hope yayi kyau?

Juyo kan ta tayi daga wajen da take kallo,ta ji dadi har cikin ranta ,daya tambaya,dan bata yi ma tsammanin zai iya tunowa ba ,balle ya har tambaye ta,wanda hakan ke nufin,ya damu da al'amuran ta,dan murmushi ta saki,ta bashi amsa

"E!Alhamdulillah yayi kyau sosai"

Tafin hannun sa daya ya mik'o mata,wanda da baya amfani da shi wajen tuk'in,ba tare da ya kallo in da take ba,kan ta ne ya dan d'aure ganin abinda yayi,sam bata gane abinda yake nufi da hakan ba,dan juyowa yayi ganin tayi shiru,sai dai yanayin yadda da tayi da fuskar ta ne ya sa shi dan sakin dariya ciki-ciki dan daga gani a rude take,sai yaga ta kara mishi kyau,kafin ya ce

"Results din na ke so ki bani na gani"

Oh sai da yayi maganar da gane inda ya dosa,dariya ta dan yi wa kanta na rashin gano abinda yake nufi tun farko,cikin jakar ta ta sa hannu ta ciro fefar(paper) da ke nad'e,tare da mika masa

T'saut'sayi ya sa hannayen su tab'a na juna,tsigar jikin ta ne ta ji ya tashi,ga wani abu kamar electric shock da ya zo tun daga tsakiyar kanta zuwa tafin k'afar ta,kallan juna suka yi a lokaci guda,domin yanayin da taji,shima haka yaji a tasa bangaren,kafin tayi saurin janye hannun ta,bayan ta sakar masa fefar a hannun sa,cikin sanyin jiki,ta kawar da kanta zuwa kallan waje kirjin ta sai dokawa yake sakamakon yanayin da taji a jikin ta...

Dan rage gudun motar yayi,sa'annan ya warware fefar,don ganin abinda ya k'unsa,wani murmushi ya saki,tare da fadin

"Wow!I am really impressed,this is a very good result,kin yi k'ok'ari sosai,ashe dai k'anwar ta wa brainee ce"

Ya karashe da sigar tsokana tare dan kallo in da take,bayan ya ajiye mata fefar a kan jakar ta,wani dadi ne ta ji ya lullub'e ta ta koina,na yabon da ta samu daga gare shi,a hankali ta furta kalmar

"Thank you"

Wata tambayar da ya sake sakowa da ya sa y'an hanjin cikin ta k'ad'awa,tare da saurin sake kallo in da yake

"Uhmm ni ko k'anwata,ko kin san me ya sa Hajja tunanin soyayya mu ke yi?

Tirk'ashi!!Wata sabuwa in ji y'an c'ac'a,ta ya zai yi mata irin wannan tambayar,kara sadda kanta kasa tayi ga bugun zuciyar ta da ke dad'a karuwa fiye da na d'azu,a sanyaye ta tayi karfin halin cewa

"Ni ma fa ban sani ba"

Ta re da gyabe fuska kamar za ta yi kuka,yanayin yadda tayi maganar,da yadda ta yi da fuska ne ya k'afa fiddo da tsantsar yarintar ta,wacce ta bashi dariya sosai,da ma da gangan yayi mata tambayar duk dan ya tsokane ta,ba karamin kyau take karawa ba in ta yi alamun rud'ewa,bai sake ce mata komai ba,wanda hakan yayi ya mata dadi..

Da haka suka cigaba da tafiya in da ta ga sun shiga wani wuri,sannan yayi parking,d'ago kanta tayi tana kallan kayataccen ginin da ta ga an rubuta "Dalema Supermarket" a sama,kashe motar yayi tare da fadin

"Muje koh"

K'ad'a masa kai tayi ba tare da tace komai ba,ta fito,sai da ya sa wa motar makulli(lock),kafin suka jera zuwa ciki.

Cikin yayi matukar birge ta,ce mata yayi ta d'ibi duk abinda take so a wurin,amma ta kasa,ganin bata da niyyar daukar komai ne,ya sa shi fara jidar mata kayayyaki,dangin su cosmetics,turarruka,chocolates,biscuits,chocolate forge,assorted drinks da sauran kayan tarkace,daya gama dan gwalalo idanuwa ta shiga yi ganin tulin kayayyakin da ya kwaso,taso tayi magana akan sun yi yawa,sai dai bakin ta ya kasa tabuka hakan,haka tana ji tana gani ya gungura keken da ya cika taf da kaya,zuwa counter don ya biya kudin inda take biye da shi kamar wacce ruwa ya cinye,mika musu Atm card din sa yayi dan su cira ta P.O.S kasancewar bai da isassanun kudi a jikin sa,jikin ta sai ya kara mutuwa da ganin dubunnan kudaden da aka cira,sannan suka fito...

K'ADDARA TA Where stories live. Discover now