Bin bayan ta yayi da kallo ganin yadda take ta sauri,komai na jikin ta na motsawa,wani irin abu ne ya ji ya tsarge ilahirin jikin sa,gashin jikin sa gaba daya sun mike,yanayi ne da bai taba tsintar kansa a ciki ba,ajiyar zuciya ya dan sauke,tare da furta
"Hasbunallah"
Yayin da yayi saurin kawar da kan sa gefe,cike da sanyi jiki da kasala,don in ya cigaba da kallon ta zai iya shiga wani hali.
Wani irin sonta da kaunarta ne ke fizgar zuciyar sa,dan ya lura ita ma akwai son sa a zuciyar ta,a gefe guda kuma ga tayin soyayyar sa da ta karba,wanda bai yi tunanin samu a sauki ba,sai gashi Allah ya tausaya mishi ya sa ta aminta da shi,bashi da sauran wani farin cikin a rayuwa.
Cikin sauri ta karasa cikin gidan,kirjin ta na bugu,tare sauke nunfarfashi,saboda gudun da tayi,burin ta bai wuce taga tayi nesa da shi ba.
Fadawa falon tayi ko gaban ta ba gani sosai,dan ko sallama bata yi ba,kai tsaye tayi hanyar hawa stairs zuwa dakin ta,sai dai muryar data dakatar da ita ce ta sa ta tsayawa cak!ta wawayo don bata lura akwai wani a falon ba.
Momy ce ta yi mata maganan,dan ta dan tsorata da yanayin yadda ta shigon
"Lafiyar ki kalau kuwa kika shigo a firgice babu ko sallama kaman wacce aka biyo?
Shiru babu amsa dan bata san me zata ce mata ba,in ban da ajiyar zuciyar da take saukewa
Ganin haka ne ya sa ran Momyn ya fara baci,ya sa ta sake fadin
"Ba da ke nake yi ba ne kika yi min shiru?
Jin yadda tayi maganan ta san ran mahaifiyar tan ya fara baci,hakan ne ya sata karasa wa in da take zaune,kaman yadda ta barta kafin ta fita,ta samu waje ta zauna sannan ta ce
"Ki yi hakuri Momy,Allah babu komai"
"Babu komai shine kika shigo a firgice da har kika kasa yin sallama wanda hakan ba dabi'ar ki bace,balle ma ki lura da ni a nan,ki fada min gaskiya tun kafin rai na ya gama baci"Momy ta fada a hasale
Dukar da kan ta tayi kasa,don ta tsure😂da yadda Momyn ke magana,kafin ta ce
"Daman Ya Nabil ne"...Sai kuma ta kasa karasa maganan tayi shi ru
Gaban Momyn ne ya dan bada ras!kar dai wani abu yayi mata ta bayan ta fita kiran da yake mata ta,fada a ranta,sai dai kuma ta aminta Nabil bazai taba iya cutar da Maryam ba,amma fa ba a shaidar dan yau,hakan ne ya sa ta sake fadin
"Uhmm ina jinki me Nabil din yayi miki"Momyn ta fada ta na kara tsare ta
A hankali ta ce
"Dama fa cewa yayi yana so na"ta fada tana mai sadda kanta kasa,tare da jin ina za ta saka kanta saboda kunya,sai dai ba ta da wani zabi dole ta fada mata gaskiya..
Jin abunda Maryam ta fada ne,ya sanya ta sakin ajiyar zuciya,shi ya sa babu kyau zargi ba tare da bincike ba,sai gashi shaidan ya sa zuciyar ta ya tafi in da ma ba hakan bane,a lokaci guda kuma ta saki murmushi jin dadi sannan ta ce
"Alhamdulillah!kin ga amfanin hakuri da tawakkali koh?da ki ka yi hakuri ba gashi nan ya tako har in da kike ya fada miki sirrin da ke zuciyarsa ba?kin ga kenan me? kin tsira da mutuncin ki da darajar ki ta y'a mace,duk da bawai ina fadin laifi ne mace ta nunawa namiji tana son sa ba,tunda hakan ya faru tsakanin Nana Khadija da Manzon Allah (SAW)ita ta fara nuna tana son sa,wanda hakan bai sa ya wulakantata ba,ila ma so,kauna da tattali da ya nuna mata bayan auren su,har mai rabawa ya raba,sai dai a irin zamanin da muke ciki na yanzu,ba kowanne namiji bane ya ke daukar macen da daraja ba in har ita ce ta fara nuna tana son nasa,wani hakan da ta fada sai ya sa k'ima da mutuncin ta su zube a idanun sa,hakan ne ya sa mafi akasarin mata ke rike soyayyar da namiji a ran su don gujewa cin mutumci da wulakanci,in har rabon su ne sai kika sun same shi(jan hankali gare mu mata),ko nan gaba ina kara mai nusar da ke akan hakuri,duk abinda kika samu ki saka a ranki naki ne kuma rabon ki ne,wanda baki samu ba,to dama can ba naki bane,sai ki hakura har Allah ya baki naki da fatan kin gane bayanin da na yi miki"
YOU ARE READING
K'ADDARA TA
RomansaBanko kofar dakin ta yi a fusace,dole yau ayi wacce za a yi a kare tsaknin ta da shi,hakimce a zaune ta same shi ya bama kofa baya daga shi sai boxers,ba riga sai karfaffn jikin sa d ke a murde,macbook pro na a gaba shi abnda ta hango a ciki screen...