SHIMFIDA.

12.3K 752 27
                                    

Bismillahir Rahamanir Rahim.

~~~

An ce wai k'addara tana da tarin ma'anoni a duniyar nan.

Ance kamar yadda rayuwarmu take mabanbanciya, haka k'addarar ma take.

Sai dai kamanceceniya a sunanta kawai.

Wani zai fassara maka kaddara da sanadin rasa dukiya ko mulkinsa.

Uwa zata baiyana maka ita da mummunan abinda ya faru ga d'anta.

Uba zai iya d'ora ta kan duk abinda zaiyi hijabi da farin cikin iyalansa.

Wasu kan iya siffanta maka ita da dalilin rasa wani buri na rayuwarsu.

Sannan bayan duk wad'annan, k'addara kan iya d'aukar siffar alkhairi ma.

Misali, wani zai kasance mai nasara a komai na rayuwarsa, sai ace maka 'k'addararsa kenan.'

Ko kuma idan wani abin alkhairin ya same ka, mutane sai suce 'Dama hakan na daga cikin kaddarar da Allah ya tsara maka.

Ta riga ta san duk wad'annan, kamar kowa abinda bata sani ba shine...

Me cece tata k'addarar?

Yaushe zata fuskance ta?

A wane yanayi zata zo?

Mai kyau? Ko akasin haka?

Wad'annan tambayoyin suke yawo kullum cikin kanta, da su take kwana take tashi, cikin tsumayin lokacin da alk'alami ya bushe akansa, don wata k'addarar tamkar ZANEN DUTSE ce... Babu wani abu da ya isa ya canja ta!

Zanen Dutse Complete✓Where stories live. Discover now