Assalamu alaikum, fatan na same ku lafiya, kuyi hakuri a duk lokacin da kuka ji shiru ya tsawaita daga gare ni, abubuwa sun sha kaina ne ta kowanne ɓangare, kuma ina koƙarin daidaita komai ɗin ne don abubuwa su tafi min daidai. Me akace ne? Wai kowacce kwakwalwa da iya abinda zata iya.
Nagode da fahimtarku da kuma addu'oinku. Idona nata samun sauki tunda ga MAJID nan a yanzu na kawo muku.
~~~~
Jidda ta buɗe idanunta a hankali cikin madaidaicin hasken ɗakin daya baje a iska, ta fahimci cewa lokacin safiya ne amma kuma a cikin sakannin da suka biyo baya sai ƙwaƙwalwarta ta kasa tantance wajen da take, idanunta kaɗan suke a buɗe alamun bata gama wartsakewa sosai ba amma duk da haka tana iya ganin dishi-dishin abubuwan dake zagaye da ita.
Gadon ƙato ne, filon mai laushi sannan ga hoton wasu labulaye masu kyau da take hangowa daga ɗan nesa kaɗan, kuma ba kalar labulayen ɗakin Baddo bane balle inda ta saba kwana a lagos, saboda haka ta sake ƙifta idanunta a hankali tana jin yadda jikinta yake a dunƙule, ƙafafunta haɗe da cinyoyinta sannan cinyoyinta haɗe da cikinta, kamar da wani abu ya tare ta ne a yanzu kuma da babu shi sai take jinta sakayau.
A hankali ta ƙara maida idonta ta rufe sannan ta gyara kwanciyarta tana ƙara duƙunƙunewa cikin bargon da take lulube dashi, baccin ya tafi a idanunta amma duk da haka bata son tashi, yanayin hasken ɗakin da kuma iskar ciki data dauki wani sanyi ba mai yawa ba ya mata dadi sosai, don haka ta sake gyara kwanciyarta hancincinta na ƙara shiga cikin filon yayin da wani sassanyan ƙamshi ya shiga kurɗawa cikinsa.
Sakan daya, biyu, uku... Kafin ta fahimci ƙamshin na menene da kuma inda ta sanshi, don haka lokaci guda ta miƙe da wani irin sauri a tana yaye bargon, kuma babu wata kwana-kwana ƙwaƙwalwarta ta fahimci inda take da kuma yadda akayi tazo ɗin, idanunta suka shiga wulgawa koina na bangaren ɗakin sai dai babu wanda take nema din, fita yayi kenan? Ya barta ita kadai? Ina ya tafi? Karfe nawa ma? Tambayoyin suka ɗarsu a ranta sanda idonta ya kai kan bedside drawer inda labtop dinsa ke kunne a jone jikin charger, daga gefe kuma wayoyinsa ne guda biyu.
Yana nan kenan, tunda dai ai ba zai fita ya bar wayoyinsa a ɗaki ba, don haka da sauri ta matsa ta danna wadda hannunta ya fara kaiwa don ganin lokaci. Ƙarfe tara har da ƴan mintina na safiya... Innalillahi wa'inna ilahir raji'un! Ita mai cewa ƙarfe bakwai daidai zata tafi? A wajensu Baddo ai yanzu rana ta take har ta kai tsakiya ma, ba shiri ta sauko da ƙafafunta ƙasa kuma saura kadan tayi ball da flask ɗin abincin nan na jiya tsabar sauri, har ta nufi hanyar ƙofa sai kuma ta tuna babu ko ɗankwali akanta, don tun bayan sanda Madaki ya zame ta da kanta bayan dun idar da sallar asuba bata ƙara ganinta ba.
Wani abu ya ratsa cikin kanta da ta tuno yadda ya sake rike ta a jikinsa yana saka hannunsa cikin gashinta, wani abu daya hargitsa tunaninta kenan ta manta komai balle har tayi tunanin tafiya a wannan lokacin, don a yadda ta tsara tana yin sallar asubar zata kama hanya tun kafin ma haske ya bayyana mutane su fito, amma yadda ya sake rungumeta suka koma gadon nan sai ta nemi wani sauran tunaninta ma ta rasa. Kuma saukinta ɗaya shine har a lokacin bai nemi amsar tambayoyin abinda ya gama gaya mata jiya ba, don Allah ya sani har a yanzu bata gama jin nauyinsu a kanta ba ma balle har ta fitar da amsar da zata iya bashi.
Kuma un tana tunanin zai ce da ita wani abu har ta daina, ta tsaida zuciyarta kan yadda hannayensa ke ratsa gashinta da kuma sautin fitar numfashinsa kawai, a haka har bacci ɓarawo ya ɗauke ta wanda bata farka ba sai yanzu... Yanzun da take ƙarfe tara har da mintuna na safiya.
Babu shiri ta juyo ta koma can wajen mudubi inda dardumar da suka yi sallah take, daga hijabin sallar kuwa har hular suna nan, sai dai kafin ta sunkuya hankalinta ya kai kan mudubin dake gabanta kuma take idanunta suka zare a lokaci guda, ba wai don ganin fuskarta ba sai don ganin gashin kanta wanda ɗan laushin da yake dashi ya taimaka wajen sawa bai hargitse sosai ba, amma ba abinda ta lura dashi din ba kenan, jelolin kitsonta na gefe gabadaya babu kitso ba alamarsa a jiki sai gashi kawai buzu-buzu wanda yawansa da yafi tsawonsa yasa ya tashi sosai...

YOU ARE READING
Zanen Dutse Complete✓
General Fiction#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...