~~~~~Mubarak yasa hannunsa ya tura ƙofar banɗakin a hankali, katakon ƙofar ya bada wata ƙara ta katako irin ƙiiiii ɗin nan, ƙarar da ta shiga kunnen Salwa tasa ta juyo da wani irin sauri mai haɗe da fargabar data haska tar a cikin idonta.
A lokaci guda kuwa wayar hannunta ta sulale ta daki dandaryar tiles ɗin banɗakin, ta rikice kuma diririce tana kallon Mubarak ɗin da nasa idon da ke haskawa da wani irin ɓacin ran daya haddasa kalarsu canjawa.
Tasa hannu ta dafe gefen sink ɗin tana jin kamar zata fadi sai kuma ta sake shi ta shiga takawa baya a hankali tana cigaba da kallonsa haɗe da girgiza kai cikin amsar da ba'a tambayeta ba. Mubarak ya haɗe hannayensa biyu yayin da yake kallonta da idanunsa da a yanzu suka rikiɗe suka kaɗa jazur!
"Wane Madakin kike cewa zaki mallaka?"
"Yaya... Ba wai ni bace, kawai... Kawai tunani nayi..."
"Cewa nayi dan ub*nki wane Madaki kike cewa zaki mallaka?"
Sai da ta zabura saboda yadda ƙarar tsawar daya daka ta karaɗe bangwayen toilet ɗin. Ta cigaba da girgiza kanta hannayenta na rawa, saboda Allah ya sani tunda take a rayuwarta baza ta taba cewa ta taba sanin wannan kalar ta Mubarak ba, a kullum shi wanta ne mai fahimta da kuma yi mata uzuri a lokacin da kowa kr ƙalubalantarta, amma a yanzu fuskarsa tamkar na wani zaki ne dake shirin yunƙurowa ya keta ta...
"Ke kika sa aka harbe shi?"
Wannan karon muryarsa na karkarwa alamun tsananin ɓacin ran da yake son daurewa. Salwa ta cigaba da girgiza kanta tana ƙara yin baya har sai da ta dangana da bangon karshe.
"Wallahi tallahi Yaya ƙawata ce tace..." Sai kuma ƙaryar ma ta ruguje ta rasa me zata kamo ta fada.
A lokacin ne Khadija ta ƙaraso cikin wani irin sauri hannunta damƙe da da tsakiyar top ɗin data ɗora akan siririyar rigar baccinta, ƙarar tsawar da Mubarak ya daka ce ta fito da ita ba shiri a firgice.
"Me ya faru Daddy? Me nene?..."
Ta tambaya a ruɗe tana kallon yanayin Mubarak ɗin da ita kanta bata taba gani ba tsawon zamansu. Sai kuma ta juya cikin banɗakin ta kalli Salwa da jikinta ke faman faman karkarwa cike da tsananin tsoron dake haskawa a idanunta.
"Wallahi Yaya, wallahi tallahi... Na rantse ka saurare ni, ka tsaya, ka tsaya, ka tsaya kaji..."
Cewar Salwan cikin ihu a lokacin da Mubarak yayo cikin toilet din, wayarta data fadi a kasa ya tsugunna ya ɗauka sannan hannayensa biyu ya ɓalla ta gida biyu da wani irin ƙarfi ta tsakiya.
Har a lokacin Salwan ihu take tana roƙonsa cewa ya tsaya zata masa bayanin komai.
"Mubarak me nene wai? Me tayi? Dan Allah ka saurara tunda tace ka tsaya..."
Mubarak bai saurari Salwan ba balle Khadija, ya ƙarasa ya damƙo hannayenta duka biyu a lokacin da ta ƙara rikicewa ta shiga ƙoƙarin tirjewa tana ƙara roƙonsa amma karfinta da nasa ba daya bane, ya jawo ta yana mai ture Khadija dake tsaye a kofa tana ƙoƙarin riƙe shi gefe sannan ya cigaba da jan ta suka fita daga toilet ɗin.
"Yaya dan girman Allah kayi hakuri, ka tsaya kaji, wallahi ban san shi zasu harba ba..."
Roƙonsa take yi tana magiya yayin da take juyawa tana kallon Khadija dake bin bayansu kamar mai neman taimako, suka isa har falo kuma anan din ma bai tsaya ba, gadan-gadan ya nufi hanyar ƙofa da ita bayan ya suri wasu tarin muƙullai da suka haɗa har da na motarsa akan dan center table ɗin dake falon.
"Mubarak ina zaka kaita? Fita zaka yi? Ƙarfe goma fa ta wuce... Ina zaka je a daren nan...?"
Khadija.
YOU ARE READING
Zanen Dutse Complete✓
General Fiction#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...