SHA HUDU.

4.1K 623 91
                                    


Assalamu Alaikum.

Ina miƙa tarin gaisuwa da godiya ga duk wani masoyin labarin nan ko'ina yake a faɗin a duniya sannan ina fatan baku manta da taurarin namu ba da kuma gaɓar da muka tsaya.

Kar ku manta kuma wannan labarin mallakar ƙungiyar FIKRA WRITERS ASSOCIATION ne.

Na gaishe ku kyauta.

~~~~

08:00PM
Expressway, Lagos.

"Kilo shele? (Me ya faru?)"

Cewar wani gabjejan soja a lokacin da yake ƙarasowa gaban wasu shuttle bus guda uku, inda inda sojoji biyu ke tsaye suna bincike kayayyakin da aka zube a k'asa.

"Akanwo awon bagi na. (Kawai muna duba jakunkunan ne)."

Cewar ɗaya daga cikin ƙananan sojojin dake tsaye akan kayan.

Idanun Jakadiya Babba dake tsaye a cikin mutanen motocin da aka firfito dasu yabi hannun sojan daya amsa tambayar, duk da duhun wajen tana iya ganin tudun kuɗaɗen da yake cusawa a aljihunsa wand'anda ya ciro daga aljihun jakarta, sai dai ba ta su take ba, da kowanne bugu na zuciyarta fata take kar ya gama bincika jakar ya koma kan jakar asirin nan dake gefe, taso ta riƙe ta, ta b'oye ta cikin ƙaton mayafinta amma daya daga cikin sojojin nan ya daka mata tsawa cewar ta haɗa ta ciin jakunkunan da aka jere akan titi kusan na motoci bakwai, don haka ba yadda ta iya haka ta kutsa ta ajiye ta kusa da jakar kayanta.

Tana iya jin ƙarar bugun zuciyarta kamar zai faso daga ƙirjinta wanda ke nasaba da abu guda biyu, tsoron kar sojan ya buɗe jakar da kuma tsoron kar ɗaya daga cikin matan dake tsaitsaye a gefenta su gane ta, don ko kadan ba'a tsara cewar ƴanuwan yarinyar zasu san da zuwanta ba, shi yasa ta zauna a ɗaya daga cikin motocin dake ɗauke da kayan garar.

'Bayan mun isa zan aika a kira min yarinyar ba tare da sanin ƴanuwanta ba, zan bata asirin tare da sharaɗin da bata isa ta bijire mana ba balle har ta sanar da ƴanuwanta zuwana.'

Maganar da ta gayawa Fulani kenan a daren da zasu taho, shi yasa bugun zuciyar tata ke bugawa tamkar zai faso daga cikin ƙirjin nata. Ilai kuwa, sai fatanta ya karbu da ƙarasowar wannan ƙaton sojan mai tambaya.

"Wetin be this? Who ask you to check their bags?" (Meye haka? Wa yace ku caje jakunkunansu?)

Cewar Sojan cikin wata gabjejiyar motar da tayi kama da saukar aradu da tsakiyar dare. A lokaci guda d'aya Sojan ya durƙusa da sauri ya zuge zif ɗin jakar tata sannan cikin alamun rashin gaskiya ya shiga ɗaga murya yana cewa sauran 'yanuwansa an gama da kayan zasu iya wucewa su tafi.

Jakadiya Babba ta sauke wata nauyayyar ajiyar zuciya a lokacin da aka bawa direbobin motocin umarni cewa su kwashe kayayyakinsu suyi gaba, idanunta na kan jakar ba tare da ko ƙiftawa ba aka fara d'iba ana maidawa cikin motar, duk jakar da aka d'ago sai mai ita ya d'aga hannu a saka a cikin motarsu, a haka har aka zo kan tata, wani soja ya gifta ta gabanta amma tayi nasarar ɗaga hannunta dake rawa sama aka sanya jakar cikin motarsu sannan aka cigaba da sauran.

Kuma bayan nan sai da aka shafe wasu mintuna talatin d'in kafin su iya barin wajen saboda wani azababben go-slow da ya had'e ko ta ina, don haka kamar yadda aka tsara, suna isa cikin garin Lagos kai tsaye gidan Haj. Karima suka nufa, wata hamshakiyar 'yar siyasa da take k'awa a gun Fulani.

Gidan k'ato ne mai d'auke da b'angare-bangare na gine-gine, tunda dama an san da zuwansu kasancewar Fulanin ta sanar da Haj. Karima. Motar dake dauke da kayan gara na farko ta dire Jakadiya Babba a wani ɓangare na gidan yayin da a wani ɓangaren kuma aka yiwa su Aunty Zainab, Jamila da sauran ƴanuwan Baddo iso zuwa cikin wani gini mai d'auke da d'akuna huɗu da k'aton Falo, anan duk suka baje gajiyarsa suka dinga mik'e kafa suna mik'a kafin a kawo musu had'adden abinci abinci daga kwararrun masu aikin gidan, sai hankalinsu ya koma nan tunda dama banda 'yan kame-kame a mota babu wani ƙwaƙwaran abinci da suka samu tsawon kwana biyu.

Zanen Dutse Complete✓Donde viven las historias. Descúbrelo ahora