~~~Sakan ɗaya, biyu, uku...
Kafin komai ya ƙare.
Washegari.
11:30 AM.Jidda ta tsoma slice ɗin dafaffiyar doyar data dauko cikin ƙwan data fasa a wani ɗan bowl sannan ta saka cikin man da yayi zafi a frying pan, ƙamshin albasar dake cikin kwan ya tafaso ya shiga hancinta amma duk da haka wanda take ji a jikinta yafi ƙarfi, sai ta sake shanshana fatar hannunta sannan ta kai ɗaya hannun ma kan hancinta, ta rasa wane irin azababben turare ne wannan, ace har tayi wanka amma har yanzu bata daina jinsa ba, shi ba wani ƙarfi ba amma ya kama fatarta kamar tare aka halicce su.
Ba sonsa ne bata yi ba, abubuwan da yake tuna mata dasu ne bata so, farko shine can 'Gida' don a jikin layar nan data fara tone asirin Fulani ta sanshi da kuma sanda suka tone asiri na biyu ita da Sadiya. Biyu kuma shine 'Jiya' daren jiya da ya zama wani alaƙaƙai a ranta ta kasa manta tarin abubuwan data fuskanta a cikinsa, mafi girma a ciki shine lokacin da Madaki ya riƙe ta.
Sai ta juya doyar zuwa daya ɓangarenta zuciyarta na hasashen da ta bari ta daɗe a jikinsa ma shikenan ko wankan inji za'a mata ba zata taɓa fita ba, don sakan ɗaya biyu, uku kawai akayi ta miƙe da sauri ta zare jikinta daga nasan tunda dama ba da ƙarfi ya rike ta ba, don me ma zai rungume tan ne wai? Har yanzu ta kasa lissafawa, yana fama da azabar ciwonsa sannan bai ko yi sallar magriba ba balle isha amma ya san ya rungume ta? Ita da ta san ba mutuwa zaiyi ba ma me zai kaita har kan gadonsa...
Tayi tsaki a hankali tana tunanin Allah yasa yanzu ba zai dinga kallonta da wani abun ba, tunda dama tun farko ba yarda yayi da ita ba, amma sai ɗaya ɓarin zuciyarta ma yayi nasa tsakin, 'Kar Allah yasa ma ya fasa kallon naki da wani abun, duk tsiya dai ai ya san taimako ne ya kai ki wajensa ba wani abin ba.' A hankalin ta sunkuya ta kashe gas ɗin sannan ta tsame doyar.
Tunda ta tashi bata ganshi bama, taji ƙarar motarsa wajen karfe bakwai na safe ya fita amma kafin goma ma ya dawo shaidar ba aiki yaje ba, kuma haka kurum taji yau bata son haɗa ido dashi, ya sha zamansa ai ya warke tunda har ya san ya rungume ƴar mutane, ta zubo doyar haɗe da ƴar sauce ɗin da tayi sannan ta zauna kan island din kitchen ɗin ta fara ci tana kurɓar tean data haɗa. Sai dai bata ko yi nisa ba ta fara rage taunar tata a hankali tana kallon fuskarta ta cikin reflection na glass ɗin teburin, me yasa ne take jin jikinta wani iri har yanzu? Me yasa ta kasa daina tuna abinda taji a lokacin daya riƙe ta? Wannan abun daya tsarga tun daga kafafunta har zuwa yatsun hannunta, me yasa yaƙi wucewa a ranta har yanzu?
Allah zai saka mata! Ta ayyana hakan a ranta don jikin nata ba daɗi sam, kamar bata da ƙarfi ko kuma kuzari haka take ji tunda ta tashi kuma ita ba haka take so ba, lafiyarta ƙalau ta yini jiya kuma haka take son taji ta ma yau don taci burin yin wani alala mai kifi da Aunty Zainab ta taɓa koya musu.
Da ƙyar ta iya cinye doyar nan ta tashi, ta ɗauraye kayan data ɓata sannan ta fita zuwa falo, sai taji babu sharar da zata iya yi yau saboda haka ta nufi hanyar ɗakin da take kwana tana fatan idan yaga dama ya kafa hujja da rashin sharar ya sallameta kowannensu ya huta. Ta nufi jikin dressing mirrow dake ɗakin ta zauna akan stool dinsa tana kallon fuskarta.
Da wuya, Da wuya sosai wannan sabuwar rayuwar da take ciki, ko kwalli ta manta rabonta da tasa a idonta balle aje ga sauran abubuwan da ba zata iya lissafo su ba, musamman karatun Alqur'ani tunda yanzu babu islamiyya balle makarantar dare. Idonta kai kan jelolin kalbarta da suka fito ta gefen ɗankwalin rigar dake jikinta, sai kwakwalwarta ta sake tuno mata da sanda ya riƙe ta, sanda taji alamun hancinsa a tsakanin kitson, wani sanyi ya sake ratsa ta, taji kamar zazzaɓi ne ma ke shirin kamata. Allah sarki Baddo! Da tana kusa da ita da tuni ta jiƙa mata ƴar tazargadi ko sabara tace ta fara sha a matsayin rigakafi.
YOU ARE READING
Zanen Dutse Complete✓
General Fiction#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...