Bani da labarin nan a ajiye, a tsakanin kowanne tsallaken kwana da muke yi nake samu na ƙirƙiri komai har inyi typing in turo muku, ga aiki, sannan ga hidimar yau da gobe ta kowanne bawa. Don haka dan Allah ku daina ganin shauni na, ƴar ƙwaƙwalwar na iya ƙoƙarin da zata iya.
Nagode da fahimtar ku.
~~~~
Tara saura minti biyu!
Fulani ta jefar da wayar hannunta kan gadon da take zaune cikin takaici, ƴan mintuna tsakaninta da gama waya da Hajiya Bilki amma ta kira wayar Jakadiya kusan sau goma kenan har yanzu labarin dai bai sauya ba, kiran baya shiga, kamar yadda kai baya shiga ramin tulu.
Da haƙoranta na sama ta tamke lebbenta na kasa tana cigaba da gyaɗa kai cikin ƙwafa, biyawa kawai take a ranta cewa ko bayan wannan hargitsin ya ƙare Jakadiya Babba sai ta biya bashin wannan zulumi da ɓacin ran da ta saka ta, ita ce fa! Hafsatu. Wannan Hafsatun dake take jama'a da ikonta tamkar yadda takalmi ke murƙushe kwayar gyaɗa a dandaryar ƙasa.
kamar ta kwanta ta ɗan runtsa tunda yau ba itace da turakar Mai martaba ba, sai kuma ta yanke shawarar fara yin wanka tukunna, wataƙila hucin da take ji a ranta ma ya tafi da saukar ruwan sanyin da take marari, saboda haka ta miƙe ta isa ga ƙofar makeken bandakinta na alfarma dake manne da da ɗakin.
A cikin banɗakin taji bata son sakin shower akanta balle shiga kwarmin wankan na bathtub, saboda haka ta jawo wani ƙaton bokiti dake gefe ta shiga tara ruwan zafi dana sanyi daga famfo yayin da ta koma ta buɗe wata drawer a gefe ta ɗauko wani ƙaton towel tana shirin naɗe jikinta dashi.
A daidai wannan lokacin ne daga can cikin ɗakinta, agogo ya karaɗe da sautin kiɗan algaita, kiɗan dake shaida cikar ƙarfe tara daidai na dare! Kuma a daidai lokacin ne ba tare Fulani ta sani ba wasu abubuwa suka juya a cikin ƙwaƙwalwarta, suka canja mazauninsu daga daidai zuwa akasinsa. Ta dai ji kanta ya sara kaɗan sai dai kafin ta fahimci komai ta tsinkayi ƙarar bugun kofar ɗakin daga can waje, wani bugu da yazama sila kuma masomin faruwar wata ƙaddara da ƙoƙari da taimakawarta ya samar da ita, don tabbas ne wasu ƙaɗororin, bawa nr ke zana su da hannunsa cikin allon rayuwarsa!
Bugun ƙofar da ɗan ƙarfi yake don har sai da bugun zuciyarta ya daya a lokaci guda tare da mamakin wanda zai ƙaraso mata har ciki haka kuma ya tsaya buga ƙofar tunda ta san da Safina ce ba lallai ne ta buga ɗin ba, sai kawai ta fasa cire kayan sannan ta juya ta kashe ruwan da tara ta fita.
Kanta babu ko ɗankwali sai manya-manyan kalbar da ta kitse gashinta dashi saboda rashin lokaci ta ƙarasa ta bude ƙofar, kuma a take zuciyarta ta sake ɗaukewa da wani guntun taraddadi.
Wata fuska mai cike da haiba da kamala ta baƙunci idanunta, ta ninka taraddadin ta ya tashi daga wani abu guntu sannan haka kurum kuma jikinta yayi sanyi. Mai martaba a turakarta? Da wannan daren? Me ya kawo shi?? Yaushe rabon da ya tako ƙafarsa zuwa cikin sashenta?... Tun a ranar da yazo ya sanar da ita zancen maneman auren Aisha, zuciyata ta bata amsa kai tsaye shima kuma yazo ne ba da daddare ba, ta juya ta kalli agogon dake bayanta... karfe tara daidai, ai bai daɗe da shigowa cikin gida ba ma, to me zai sa ya nemeta a wannan dare kuma a lokacin da ba gurbinta ba? tabbas dai ta san ba ƙaramin abu ne zai kawo shin ba, sai dai ta kasa aunowa? Zancen bikin naɗin ne ko wani abu daban?
"Ranka ya daɗe..." A lokaci guda bakin ta ya ambata cikin ƴar ƙaramar gigicewa.
"Tare da naki sarautar mata..." Muryarsa ta fito a hankali yana ƙoƙarin yin murmushi.
"... Yau ikon naki ne ai tunda kece riƙe da kofa." Ya sake faɗa da wata ƴar guntuwar raha a cikin sautin nasa."
Sai a sannan ta lura tana tsaye ne riƙe da hannun ƙofar har yanzu, bata bashi damar shigowa ba, saboda haka tayi saurin yin baya kafin tace.
![](https://img.wattpad.com/cover/222171643-288-k121381.jpg)
YOU ARE READING
Zanen Dutse Complete✓
General Fiction#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...