~~~Ƙofar net ɗin ɗakin Baddo ta bude, Aunty Zainab ta sako kafarta ciki da ragowar saurin da take tafe dashi, daidai lokacin da Jamila ta fito daga can cikin ɗakin dake manne a falon..
"Baddo da Hajiyan suna ciki." Muryar Jamilan ta fito a wani irin sauti da ƙarara zaka tsinto fargaba a ciki.
Aunty Zainab ta juya ta rufe ƙofar da ƴar sakatar ciki kafin tabi bayanta cike da taraddadin da tayo dakonsa, don jiya da suka dawo daga wahalalliyar tafiyar da suka yi zuwa Lagos ba tare da sanin dalilin dawowar tasu ba, a cikin gari ta sauka gidan ƙanwar Hajiya (mahaifiyarta) inda take tunanin zata huce gajiyarta kafin ta ziyarci asibiti don a duba lafiyar cikinta da tayi ta fama dashi a hanya, amma sai wayar da Jamila ta rangaɗo mata da asubahin yau ta katse duk wani shirinta.
'Aunty Zainab, Baddo ce tace in kira ki kizo, wani abu ya faru... Wani abu muka tsinta a cikin jakar kayana kamar asiri.'
Ta kutsa kai cikin ɗakin a lokacin da zuciyarta ke ƙara bitar maganganun. Dukkaninsu suka amsa mata sallamar kamar yadda idonta yaga dukkanin nasu a lokaci guda.
"Da gaske ne abinda Jamila ta kira ni a waya ta gaya min?"
Kai tsaye tayi tambayar tana kallon tsofaffi biyun dake zaune a cikin ɗakin, musamman Baddo wadda ke zaune fuskarta fayau! Ba zaka iya tsinto ainihin abinda ke wakana a tunaninta ba. Hajiya Laraba dake gefe ta gyara zamanta sannan tayi magana.
"Gaskiya ne Zainabu, ai ki san wannan zancen baiyi kama da ƙarya ba, tana buɗe jakar kayanta ne da asuba zata ɗauko hijabi sai ganin sassaƙe tayi a cikin leda jiƙe sharkaf da jini, kuma sai da Baddo tasa ta kira ni nazo ma sannan muka ga ashe jakar ba tata bace canje akayi da ta wata. Sai dai abinda muka kasa ganewa shine wa zai aikata irin wannan abun alhali duk mutanen gida aka tafi dasu a motar babu wani bare, sauran motocin biyu kuma direbobi ne kawai da kayan abinci...'
"Innalillahi wa'inna ilahir raji'un... Yanzu tana ina jakar?"
Aunty Zainab ɗin ta katse dogon bayanin da mahaifiyar tata ke shirin yi don ba shine mafi a'ala ba, Jamila ta miƙe da sauri ta buɗe cikin wata ƙaramar wardrobe dake gefe ta ɗauko jakar.
"Tsoro muke kar wani ya shigo ya gani." Muryarta ta sake fitowa da irin sautin ɗazu.
Aunty Zainab tasa hannunta dake tsaye kyam saɓanin na Jamila dake rawa ta zuge zip ɗin jakar a hankali, kamar mai fatan jinkirinta ya canja abinda ke ciki, amma ina! A ciki sak ledar da Hajiya Laraban ke ƙoƙarin siffanta mata ce. Taji gabanta ya faɗi a lokaci guda amma duk da haka ta kai tafin hannunta ta taɓa ledar, sanyin daskararren jinin dake ciki ya ratsa fatarta lokacin da tunaninta ya hasko mata zancensu da Baddo a daren da zasu tafi.
'Me yasa muna ji muna gani zamu biye musu Baddo?
Me yasa zamu karɓi garar nan?
Me yasa zamu bari suyi amfani damu su cimma wata manufarsu?
Kamata yayi muma mu tashi tsaye mu kare Jidda da dukkan iyawarmu..
Tambayoyin da suka yi Baddon kenan a daren da Fulani ta kira su ta shaida musu cewavta dauke musu ɗawainiyar Gara za'a debi su ne kawai suje su kai kayan, wanda hakan ya zama tamkar an ƙara ingiza wutar hasashen da suke yi ne akan ita Fulanin, don ba su kadai ba kowa a masarautar ya san k'iyayyar dake tsakanin ta da Madaki ba abu ne da zata watsar dashi rana tsaka kamar komai bai taɓa faruwa ba.
Kuma duk da cewar al'amarin ya shafi Fulanin da kowa ke shakka, haka bai hana ƴan ƙananan surutai akansu tashi ba, to ta yaya kuwa zasu yarda su karɓi Garar duniya ta ƙara zaginsu? Tunaninsu kenan a wancan lokacin, amma amsar da Baddo ta basu ita ta kore duk hakan, ita ta kaisu ga karɓar garar har ma da tafiya Ikkon.

KAMU SEDANG MEMBACA
Zanen Dutse Complete✓
Fiksi Umum#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...