~~~
LAGOS.
ASABAR, 09:00AM.
K'arar rurin wayar dake yashe akan durowar gefen gado ya shiga kad'awa cikin sautin k'ira'ar addu'a daga Sheikh Abdurrahman Sudais, sannan vibration d'in jikin kid'an kuma ya dinga gurzawa akan katakon durowar, hakan ya tashi d'aya daga cikin mutanen dake kwance akan gadon d'akin.
Mubarak ya mik'o hannunsa cikin magagin barci ya d'auki wayar sannan ya kara a kunnensa.
"Wai an gaya maka cewa kowa ne tuzuru irinka?" Muryarsa ta fito da alamun bacci.
Daga can gidansa, Madaki ya d'auke kofin shayinsa daga kan island d'in kitchen sannan ya biyo hanyar da zata dawo dashi falo.
"Idan na tashi Madam tayi hakuri, amma kai in ba lalaci ba baccin me kake yi har yanzu k'arfe tara na safe?"
Mubarak ya murza idanunsa.
"Tsakani da Allah yau asabar fa? Ni itace ne da ba zan huta ba?"
Madaki ya nemi kan d'aya daga cikin lausasan kujerun falonsa ya zauna sannan ya kai kofin shayin bakinsa.
"Ya akayi?" Mubarak d'in ya sake tambaya.
"Jirgin da zan hau k'arfe goma zai tashi, kuma Habibu ya kira ni d'azu yace min FreTRUST zasu shigo yau akan zancen profit d'in nan, so dole ne zaka shiga anjima ka gansu."
Jin haka yasa ya mik'e ya zauna akan gadon sosai sannan suka shiga tattaunawa game da aikin, zuwa can kuma yace.
"Insha Allah zamu yi making, bari dai su kawo reports d'in tukunna."
"Allah yasa hakan.." Cewar Madaki. "Sai naji ka kenan."
Ya k'arasa yana kokarin katse kiran, sai dai cikin hanzari Mubarak d'in ya katse shi.
"Me ya faru a appointment d'inka da doctor jiya?"
Madaki ya runtse idanunsa sannan ya shafo sumar kansa, tun jiya bayan dawowarsa daga asibiti yak'i bawa zuciyarsa damar da shi da ita zasu tattauna zancen, don kamar yadda bai san me zai gayawa kansa ba haka bai san ta yadda a yanzu zai gayawa Mubarak cewa kwanakin da likitocin ke saka masa rai dasu a duniya suna k'ara raguwa ne sakamakon dad'uwar ciwonsa ba.
"Zancen aortic stenosis ne dai, yace aortic valve d'in ne yake k'ara tsukewa..."
"Mdee ka min yaren da zan gane mana."
Sai ya d'auki kofin shayinsa ya sake kurb'a sannan yace.
"Wannan jijiyar dake d'aukan jini daga zuciya zuwa sauran b'angaren jiki ce take k'ara tsukewa, yace shi yasa nake fama da yawan ciwon k'irjin da kuma jiri."
"Allah ya sawwak'e." Cewar Mubarak bayan yayi ajiyar zuciya.
"Kar ka manta dai ka tafi da defibrillator d'inka, Allah ya kiyaye hanya."
"Insha Allah, Nagode." Da haka suka yi sallama.
Ya ajiye wayar sannan ya kalli d'an madaidaicin akwatin dake d'auke da kayansa a saman kujera, tunani da yawa ke yawo a cikin kansa amma mafi rinjaye shine, ya kasa gane dalilin da yasa a yau zuciyarsa tafi hargitsewa fiye da ko wad'anne lokutan na tafiyarsa a baya, ya kasa gano dalilin da yasa taraddadinsa yafi na koyaushe, zuciyarsa ta kasa nutsuwa tun daga ranar daya yanke shawarar tafiyar har a yanzu da awa guda kawai ya rage kafin tashinsa.
Ya sake kallon akwatin sai kuma ya d'auke kai ya shiga ambaton istigfari cikin ransa, ya kunna wayar hannunsa sannan ya shiga laluben number mutumin da zai kawo masa mota bayan Jirgi ya sauke shi a garin Kano.
YOU ARE READING
Zanen Dutse Complete✓
General Fiction#1 in Aure 19/09/2020 #1 in Sarauta 19/09/2020 #2 in Halal Romance 19/09/2020 Ta riga ta san duk wata tarin ma'ana ta k'addara, walau mai kyau ko akasinta. Kamar kowa abinda bata sani ba shine... Me cece tata k'addarar? Yaushe zata fuskance ta? A wa...